• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ministan Yaɗa Labarai na so kafafen yaɗa labarai su jajirce wajen kare dimokiraɗiyya

by WAKILIN MU
October 31, 2024
in Nijeriya
0
Ministan Yaɗa Labarai na so kafafen yaɗa labarai su jajirce wajen kare dimokiraɗiyya

Idris (na 4 daga hagu) tare da shugabannin Ƙungiyar Editocin Nijeriya (NGE) a lokacin ziyarar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga kafafen yaɗa labaran Nijeriya da kada su yi ƙasa a gwiwa wajen kare dimokuraɗiyyar ƙasar da aka kwashe shekaru 24 ana yi.

Ministan ya jaddada hakan ne a wata ziyarar ban girma da Ƙungiyar Editocin Nijeriya (NGE) ta kai masa a ofishin sa domin tattaunawa kan shirye-shiryen Babban Taron Editocin Nijeriya (ANEC) karo na 20, wanda aka shirya gudanarwa a ranakun 6-9 ga Nuwamba, 2024, a Yenagoa, Jihar Bayelsa.

Idris ya jaddada muhimmancin rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen tallafawa tafiyar dimokuraɗiyyar Nijeriya, inda ya tuna da muhimmiyar rawar da suka taka a gwagwarmaya da mulkin kama-karya na sojoji.

“Kowa ya yi gwagwarmaya sosai a tafiyar dimokuraɗiyyar Nijeriya, inda kafafen yaɗa labarai ke kan gaba wajen yaƙi da mulkin kama-karya na soji.

“Saboda haka, shekaru 24 bayan haka, bai kamata a ga kafafen yaɗa labarai sun yi ƙasa a gwiwa ba a wannan muhimmin lokaci. Abin da ya kamata su yi shi ne ci gaba da ƙarfafa goyon bayansu ga dimokiraɗiyya.”

Ministan ya tabbatar wa shugabannin NGE, ƙarƙashin jagorancin Shugaban NGE, Eze Anaba, kan ƙudirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kare martabar dimokiraɗiyya, gami da ‘yancin yaɗa labarai.

Ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su zama jagororin kare dimokuraɗiyyar Nijeriya, da inganta zaman lafiya, haɗin kai, da tsaron ƙasa wajen yaɗa lamurran ƙasa.

Idris ya ci gaba da bayyana cewa ajandar kawo sauyi na gwamnatin Tinubu na ci gaba da gudana, ya kuma roƙi kafafen yaɗa labarai da su bayyana abubuwa masu kyau, yana mai cewa Nijeriya na kan hanyar zuwa wani sabon zamani na ci gaban zamantakewa da tattalin arziki, wanda ke zuwa da ƙalubale.

Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa ɓangaren yaɗa labarai ta hanyar ayyuka na musamman kamar bayar da lamuni ta Bankin Masana’antu da magance tsadar buga jaridu.

A nasa jawabin, Anaba ya bayyana muhimmancin taron ANEC da ke tafe a Jihar Bayelsa, inda ya bayyana cewa taken sa, “Haɓaka Tattalin Arziki da Dabarun Ci Gaba a Ƙasa Mai Ɗimbin Albarkatu,” ya yi daidai da buƙatun da Nijeriya ke da shi a halin yanzu da kuma buƙatar neman mafita don samar da ci gaba.

Loading

Tags: dimokiraɗiyyadimokiraɗiyyareditociEze AnabaMohammed IdrisNGE
Previous Post

Ali Nuhu ne ya yi min aure, ya kuma ba ni jari, inji Alolo

Next Post

Gwamnati da kafafen yaɗa labarai abokan hulɗa ne, ba na adawa ba, inji Minista

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Gwamnati da kafafen yaɗa labarai abokan hulɗa ne, ba na adawa ba, inji Minista

Gwamnati da kafafen yaɗa labarai abokan hulɗa ne, ba na adawa ba, inji Minista

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!