SHUGABAN Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, ya bayyana cewa Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) da Kungiyar Masu Shirya Finafinai ta Arewa (AFMAN) su ne gwamnati ta yarda da su su yi wa kowane ɗan fim ɗin Hausa rajista.
Ya faɗi haka ne a lokacin da ya ke yi wa mujallar Fim ƙarin bayani kan yadda hukumar sa za ta yi wa ‘yan Kannywood rajista.
Idan kun tuna, jim kaɗan bayan ya ɗare kujerar shugabancin hukumar ya ba da sanarwar cewa hukumar za ta ba da lasisin ga duk wani mai sana’a a cikin kannywood, amma daga baya ya damka alhakin sabunta lasisin a hannun ƙungiyoyin ‘yan fim.
Tun daga lokacin jama’a su ke tambayar lokacin da za a fara yin rajistar da tsarin za a bi wajen sabuntawar.
A hirar sa da wakilin mu a ofishin sa kan al’amarin, El-Mustapha ya ce, “Wannan dama ce ta ƙungiyoyi da tun a baya su ka rasa, wadda a yanzu mu ka mayar musu da ita, saboda ‘yan fim su su ka san kan su a ƙungiyance, don haka zai fi sauƙi idan su su ka tantance kan su.”
Sai dai ya ce duk da haka damar da aka ba ƙungiyoyin, hukumar ba za ta zuba masu ido ba.
“Za mu samar da wakilai masu saka ido don ganin aikin ya tafi daidai, don haka akwai wakilai daga Hukumar Tace Finafinai, Hukumar Hisbah, Hukumar Shari’a da za su yi aiki tare don ganin abin ya tafi daidai,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, “Akwai ƙungiyoyi na ‘yan fim da yawa, amma dai a yanzu mun zaɓi ƙungiyar MOPPAN da ta Arewa domin gudanar da aikin wanda a ƙarƙashin su ne duk wani ɗan fim zai yi rajista ya zama halastaccen ɗan fim da hukuma a Jihar Kano za ta yarda da shi.
Kuma abin da na ke so mutane su sani, mun zaɓi waɗannan ƙungiyoyin guda biyu ne domin samun daidaito, domin da wuya ka samu wani ɗan fim a Kano da ba ya cikin waɗannan ƙungiyoyin.
“Ni kai na ai ka ga akwai ƙungiyar mu ta AHPIP kuma ta na nan har yanzu, akwai ƙungiyoyin mata ‘yan fim; duk ban saka su ba saboda ba na so abin ya yi yawa don kada ya haifar da rashin tsari. Don a yanzu so mu ke mu ga an haɗe kan ‘yan fim don su zama tsintsiya-maɗaurin-ki-ɗaya.
“Kuma ka gane, ni ɗan fim ne da na ke a matsayin jarumi, darakta, furodusa, don haka duk wani abu da ake gudanarwa a cikin harkar na sani. Duk wanda zai zo mana da wasa ba za mu saurara masa ba. Za mu yi abin mu ne cikin tsari domin samun nasarar da mu ke buƙata.”