ƘUNGIYAR Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), ta ƙasa, ta bada sanarwa ta musamman na fara saida fom ɗin takarar babban zaɓen ƙungiyar da zai gudana a watan Janairun 2025.
Sakataren kwamitin zaɓen, Malam Ibrahim L. Ibrahim shi ne wanda ya fitar da sanarwar a safiyar yau Litinin.
A cikin sanarwar, Malam Ibrahim ya ce, “Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), na farin cikin sanar da cewa za ta fara siyar da fom ɗin tsayawa takara ga duk mai sha’awar tsayawa takara a zaɓe mai zuwa a yau Litinin, 28 ga Oktoba, 2024.
“Za a iya samun fom ɗin a sakatariyar kwamitin zaɓen, za kuma a ci gaba da siyarwa da dawo da fom har zuwa tsakiyar dare na 31 ga Disamba, 2024 (makonni biyu kafin ranar taron).
“Ofisoshin zaɓe – Zaɓen zai ƙunshi ofisoshi kamar haka:
-Shugaba
-Mataimakan shugaban guda uku (kowanne yana wakiltar shiyya)
-Sakatare
-Mataimakin Sakataren
-Ma’aji
-Sakataren Kuɗi
-Sakataren Tsara-tsare
-Mai binciken kuɗi (auditor)-1
-Mai binciken kuɗi na biyu (Auditor)-2
-Jami’in walwala (welfare officer)
-Jami’in Hulɗa da Jama’a (PRO)
-Jami’in Hulɗa da Jama’a (PRO2)
“Ga farashin fom ɗin kowane mataki:
Ofishin Shugaban – N100,000.
Mataimakin Shugaban da Sakatare – N50,000 kowanne.
Sauran ofisoshi: N30,000 kowanne.
“Ba za a dawo da kuɗi ba, bayan sayen fom ɗin takara.
“Sharuɗɗan cancantar shiga takara:
“Duk mai sha’awar tsayawa takara a kowane ofishi, dole ne ya zama memba mai rijista na ƙungiyar.
“Muna kira ga duk masu neman takara da su garzaya sakatariyar kwamitin zaɓe domin sayen fom ɗin su cikin gaggawa.
“Ko a tuntuɓi waɗannan lambobin:
08038690968 – 08064269908”