HAƊAƊƊIYAR ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa ta Nijeriya, wato MOPPAN, reshen Jihar Katsina, ta gudanar da zaɓen shugabannin ta a yau Asabar, 25 ga Janairu, 2020.
Zaɓen, wanda aka gudanar a ɗakin taro na ‘Katsina Vocational Training Centre’ da ke kallon gidan Alhaji Ladan Wapa a Ƙofar Durɓi, Katsina, ya samu halartar dukkan masu ruwa da tsaki da ke masana’antar Kannywood ta Jihar Katsina.
Sun haɗa da ƙungiyoyin furodusoshi, daraktoci, ‘yan wasa, masu kyamara, mawaƙa, editoci da marubuta.
An fara kaɗa ƙuri’a da misalin ƙarfe 11:00 na safe.
Duk da yake dukkan ‘yan takarar ba su da abokan hamayya, wannan bai sa a ƙi yin da zaɓe ba, wanda aka gudanar bisa ƙa’ida.
Wasu daga cikin waɗanda su ka kaɗa ƙuri’a sun haɗa da Isah Sani Randawa, Shamsu Surajo Ɗanzaki, Isah Bawa Doro, Kabir Muhammad Ultimate, Ibrahim Bala Al-Ihsan, da Bilkisu Sadi Dutsin-ma.
An tsaida jefa ƙuri’a da misalin ƙarfe 12:30 na rana, sannan aka ƙirga ƙuri’u, aka kuma bayyana sakamako.
Ga jerin sunayen sababbin zaɓaɓɓun shuwagabannin:
1. Lawal Rabe – Chairman
2. Aminu Musa Bukar – Vice Chairman
3. Yasir Abubakar – Secretary
4. Rabe Halliru – Assistant Secretary
5. Ibrahim Shehu – Treasurer
6. Amina Abdullahi – Financial Secretary
7. Ibrahim Sani – Auditor
8. Kabir Abdulƙadir – Organising Secretary
9. Ummulkhairi Abubakar – Welfare Director
10. Rabi’u M. Yaro – Publicity Secretary
Wata majiya ta ce kowa ya amince da cewa zaɓen da aka yi sahihi ne.


A halin yanzu tsofaffin shuwagabannin ƙungiyar na Jihar Katsina sai a watan Maris wa’adin su zai ƙare. Yanzu za a ci gaba da shirye-shiryen rantsar da sababbin shuwagabannin har zuwa lokacin da wa’adin tsofaffin shuwagabannin zai ƙare.
Malam Salisu Muhammad (Officer), wanda shi ne Mataimakin Sakatare na MOPPAN na ƙasa, shi ne malamin zaɓe, kuma shi ya wakilci shugaban MOPPAN na ƙasa.
Salisu Officer ya amince da zaɓen da aka yi.
Bugu da ƙari, ita ma uwar ƙungiyar MOPPAN ta ƙasa ta amince da zaɓen, har ta aika wa sabon shugaban da takardar taya murna.
A takardar, wadda Sakatare-Janar na MOPPAN na ƙasa, Malam Salisu Mu’azu, ya rattaba wa hannu a yau, ƙungiyar ta yi maraba da zaɓen sababbin shugabannin da aka yi.
Haka kuma ta bayyana farin cikin ta kan yadda sabon shugaban ya dage wajen haɗa kan ‘ya’yan ƙungiyar a jihar.
Ta ce, “Mu na sa ran mu ga ingantaccen jagoranci daga gare ka, musamman wajen ciyar da reshen MOPPAN na Jihar Katsina gaba.”
