KUNGIYAR Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta bayyana ƙudirin ta na faɗaɗa tuntubar da take yi zuwa jama’a a fadin duniya, wanda hakan zai daga matsayin ta a ciki da wajen Nijeriya.
Don haka ne ma ta shiga aikin haɗa ƙarfi tare da musayar al’adu da sanin makamar aiki.
Saboda haka, Shugaban kungiyar na ƙasa, Malam Umar Maikuɗi (Cashman), kwanan nan ya kai wasu takardun neman haɗin gwiwa ga Jakaden ƙasar Philippines a Nijeriya, wato Merleso J. Mallejor, a madadin ƙungiyar.
Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na ƙungiyar, Ibrahim Amarawa, ya faɗa a takarda ga manema labarai a yau Juma’a cewa: “Wannan ƙoƙarin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da MOPPAN ke yi wajen inganta ayyukan ta, tana faɗaɗa sanin da aka yi mata a fadin Nijeriya da ƙetare.
Ya ce: “Bisa tafarkin kirarin nan na ‘Kannywood Ce Farko,’ a shirye MOPPAN take domin haɗa gwiwa da ɗaiɗaikun mutane da hukumomin gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kan su domin ta cimma burin ta na haɓaka Kannywood ta zama ƙaƙƙarfar masana’anta finafinai ta duniya.”