• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Mun rufe wajen shirya fim da kama ‘yan fim 30 masu yin aiki ba bisa ƙa’ida ba – Tijjani Asase

Cewar El-Mustapha: Ba mu kafa kwamiti don cin mutuncin kowa ba

by MUKHTAR YAKUBU
July 26, 2024
in Labarai
0
Mun rufe wajen shirya fim da kama ‘yan fim 30 masu yin aiki ba bisa ƙa’ida ba – Tijjani Asase

El-Mustapha (a tsakiya) tare da 'yan kwamitin

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAN Kwamitin tsaftace ayyuka a Kannywood, Malam Tijjani Abdullahi (Asase), ya bayyana cewa kwamitin ya samu nasarori a ayyukan da yake yi na fita waɗanda suka haɗa da rufe wuraren da ake shirya finafinai ba bisa ƙa’ida ba guda uku tare da kama daraktoci biyu da sauran ma’aikata da jaruman masana’antar har 30.

Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ce ta kafa kwamitin don tabbatar da ana bin dokokin ta sau da ƙafa.

Asase ya shaida wa shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, a wani zama da suka yi, cewa abin da suka yi wata babbar nasara ce ga masana’antar.

An yi zaman ne a ranar Talata, 24 ga Yuli, 2024, inda kwamitin ya ba da rahoto kan wasu daga cikin nasarorin da suka samu tun bayan da aka naɗa su a matsayin shugabanni.

Da yake nasa jawabin, El-Mustapha ya jinjina wa ‘yan kwamitin kan yadda suka jajirce wajen sauke nauyin da hukumar ta ɗora masu bisa cancantar su tare da kishin da suke da shi na ganin hukumar da masana’antar Kannywood sun samu cigaba mai ɗorewa.

Ya jaddada cewa ba a kafa kwamitin don a ci wa kowa mutunci ba sai don a tsaftace tare da fito da ƙima da darajar masana’antar.

Ya ƙara da cewa: “Manufar kafa kwamitin ita ce tabbatar da ana bin doka da ƙa’ida a masana’antar Kannywood sau da ƙafa tare da bin duk wata hanya da ake ganin masana’antar ta samu cigaba ta yadda za ta yi gogayya da sauran takwarorin ta na Nijeriya dama duniya baki ɗaya.”

El-Mustapha ya ƙara da cewa, “Tuni lokaci ya wuce da wasu za su rinƙa amfani da sunan masana’antar ta Kannywood suna yin abin da bai kamata ba domin cimma ƙudirorin ƙashin kan su.

“Don haka ina miƙa saƙon godiya ta ga ‘yan masana’antar Kannywood da al’ummar Jihar Kano baki ɗaya dangane da goyon baya da haɗin kai tare da goyon bayan da suke bai wa hukumar a ko da yaushe.”

Tijjani Asase (a hagu) tare da El-Mustapha

Loading

Tags: Abba El-MustaphakwamitiTijjani Abdullahi Asase
Previous Post

Batun zanga-zanga: Wasu ɓata-gari na iya amfani da damar su tada tarzoma – Idris 

Next Post

Darakta a Kannywood Usman Aphala ya auri jaruma Amina Miemie

Related Posts

AFMAN ta taya Sarari murnar samun damar halartar taron baje-kolin finafinan Nijeriya a Toronto da fim ɗin ‘Kakanda’
Labarai

AFMAN ta taya Sarari murnar samun damar halartar taron baje-kolin finafinan Nijeriya a Toronto da fim ɗin ‘Kakanda’

June 16, 2025
Naɗa ni jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry Powder da aka yi zai amfani Kannywood baki ɗaya, inji furodusa Abubakar Galadima
Labarai

Naɗa ni jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry Powder da aka yi zai amfani Kannywood baki ɗaya, inji furodusa Abubakar Galadima

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
Next Post
Darakta a Kannywood Usman Aphala ya auri jaruma Amina Miemie

Darakta a Kannywood Usman Aphala ya auri jaruma Amina Miemie

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!