* ‘Ya yi fama da hawan jini’
* Za mu yi kewar Ubale sosai, inji Mansurah
BABBAN aminin marigayi Ubale Ibrahim a Kannywood, fitaccen jarumi kuma mawaƙi Yakubu Mohammed, ya bayyana zaman da ya yi da marigayin, ya ce sun shekara sama da ashirin kamar ‘yan’uwa na jini.
A rubutun ta’aziyyar da ya yi a soshiyal midiya, Yakubu ya bayyana Ubale, wanda sunan sa na yanka Muhammadu Auwal, da cewa mutum ne wanda abin duniya bai dame shi ba.
Ubale dai ya rasu a daren jiya a Kano, aka yi jana’izar sa a yau. Mutuwar sa ta girgiza ‘yan fim matuƙa.
A ta’aziyyar da ya yi, Yakubu ya kuma bayyana cewa Ubale ya yi fama da ciwon hawan jini wanda a bara ma da ciwon ya tashi sai da ya shafe wata ɗaya ba ya iya gane hatta iyalin sa.
Yakubu, wanda ya riƙa gwamutsa Hausa da Turanci a rubutun da ya yi, ya fara da bayyana cewa ya na yin rubutun ne cike da hawaye.
Ya ce: “I am writing this with tears in my eyes. I can’t stop crying.
“Allah ya jiƙan ka Ubale. Mun yi babban rashi.”
Jarumin ya faɗi yadda shi da Ubale su ka yi waya a daren jiya bayan shan ruwa, su ka aje magana cewar za su haɗu a yau.
Amma daga baya sai matar Ubalen ta kira shi a waya bayan mijin nata ya yanke jiki ya faɗi, ya je su ka garzaya da shi asibiti.
Yakubu ya ce: “Mu na buɗe baki ya kira ni, mu ka yi magana a kan da safe za mu haɗu. Ya yi sallar Isha, sun ci abinci da abokan sa a unguwar su, ya yanke jiki ya faɗi. Ashe tafiyar kenan.
“Maiɗakin sa ta kira mu, sai asibiti. Mu na isa, ‘doctors’ su ka ce ai ya rasu.
“Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un!”
A cewar Yakubu, Ubale ya girme su shi da Sani Musa Danja, to amma ya kasance a sana’ance ya na ƙarƙashin su a kamfanin su na ‘Two-Effects Empire’.
“Duk abin da ka sa shi, ba girman kai ba ɗagawa zai je ya yi; wanda bai kai shi ba ma sai ka ga ya sa Ubale aiki ko kuma ka ga ya aike shi kuma ka ga ya je,” inji Yakubu.
Ya ci gaba da bayyana cewa: “Ubale a wajen marigayiya mahaifiyar Sani Danja ya girma. Duk da ba ‘yan’uwantaka ta jini, unguwa ce kawai ta haɗa su, sai da ya zama kamar ita ta haife shi.
“Idan aka nemi Sani ko Yakubu ba ma nan, to Ubale shi ne wakilin mu.
“A ɗawainiyar mu bai taɓa nuna gazawa ko ƙosawa ba. Ya yi ɗawainiya da mu da ‘ya’yan mu.”
Haka kuma ya faɗi irin yadda abokantar su ta ke, ya ce, “Duk inda na je, ina shigowa Kano shi na ke fara kira a waya. Ya girme ni, amma ‘Yallaɓai ya ke ce min. Sai ka ji ya ce, ”Yallaɓai ga ni nan zuwa’. Ko me ya ke zai bari ya zo inda na ke.”
Mawaƙin kuma jarumi ya yi tsokaci kan irin rashin lafiyar da marigayin ya yi fama da ita, inda ya ce, “Dole ne in yi kuka; Ubale ya sha wahala sosai. Last year daidai wannan lokacin – azumin bara – hawan jinin sa ya tashi har sai da ya yi ‘losing memory for over a month’, ba ya iya gane komai, hatta iyalin sa da ‘ya’yan sa. Mu ka yi ta magani har Allah ya ba shi lafiya.”
A cewar Yakubu, Ubale mutum ne mai kawaici, wanda abin duniya bai dame shi ba.
“Sau tari ba shi da kuɗi, babu abinci da za su ci a gidan sa, amma ba zai taɓa buɗe baki ya ce ga halin da gidan sa ya ke ciki ba, sai dai in mun lura da yanayin sa mun tambaye shi sannan zai faɗa mana, a magance masa matsalar.
“Bai damu da abin duniya ba. Idan na dame shi da bai son kazar-kazar wajen neman kuɗi sai ya kalle ni ya yi murmushi ya ce, ‘Yakubu kenan!’
“He was always comfortable with the little da ya samu.
“Ubale kwalliya da riga ba su dame shi ba. Idan ya yi wata shigar sai na yi ta masa surutu in ce, ‘Kai fa ‘actor’ ne, ‘television star’. Ya kamata ka dinga yin gayu.’ Sai ya yi dariya ya ce, ‘Yakubu kenan!’
“Ko Ubale ya yi fushi, lokaci ƙanƙani za ka ga ya huce, komai ya wuce.”
Saboda zurfin shaƙuwar su ne da Ubale ya fara samun haihuwa sai ya raɗa wa ɗan suna Yakubu, ga shi har yaron ya girma zai shiga jami’a, inji Yakubu Mohamned.
“Haihuwar sa na farko ya yi min takwara, ya sa wa jariri Yakubu.
“Yakubu is now 17 years old, about to go to university. RIJF Ubale.”
Ita ma a ɓangaren ta, maiɗakin ɗaya aminin na Ubale, wato Sani Danja, Hajiya Mansurah Isah, ta bayyana alhinin ta game da wannan rashi da aka yi, ta na faɗin lallai za su yi kewar Ubale.
A wani saƙo da ta aiko wa da mujallar Fim, tsohuwar fitacciyar jarumar ta ce mutuwar Ubale aba ce mai raɗaɗi, to amma Allah shi ya san daidai.
“Mutum ne nagari, mai sauƙin kai, tsarkakke,” inji ta.
Mansurah ta yi kira ga jama’a da su taya su addu’ar samun rahama ga marigayin.
Shi dai Ubale, memba ne na gidauniyar agajin talakawa wadda Mansurah ke jagoranta, wato ‘Today’s Life Foundation’. An sha ganin sa wajen aikin raba kayan tallafi ga masu ƙaramin ƙarfi wanda ƙungiyar tasu ta ke yi.