“Thank you Maigida Lilin Baba.”
SAƘON godiyar da da daraktan Kannywood Alfazazee Muhammad ya rubuta kenan tare da ɗora bidiyo na kyautar mota da fitaccen mawaƙi kuma jarumi Lilin Baba ya gwangwaje shi da ita a shafin sa na Instagram.
A daren jiya Talata, 10 ga Agusta, 2021 Lilin Baba ya ba daraktan kyautar mota ba zato ba tsammani.
A cikin bidiyon da Alfazazee ya ɗora, an jiyo ana yi masa addu’ar Allah ya sanya alheri, Allah ya sa rai aka yi wa.
Sa’annan kuma an nuna darakta Shehu Jaha a jikin motar, wadda ƙirar Toyota Avalon ce, ya yi da mai addu’ar ya ke tambayar ina Alfazazee ya ke? Nan take ya leƙo fuskar sa cike da murna.
‘Yan’uwa, abokan arziki da abokan sana’ar sa sun yi murna matuƙa da wannan kyauta da daraktan ya samu.
Tun a daren jiya duk inda ka leƙa a soshiyal midiya, hoton Alfazazee, Lilin Baba da motar ake yaɗawa, ana yi masu fatan alheri.

Da mujallar Fim ta tambaye shi abin da zai ce game da wannan ni’ima ta kyautar mota da ya samu, sai ya ce, “Alhamdu lillah! Haƙiƙanin gaskiya babu abin da zan ce sai dai in yi wa Allah godiya. Sannan kuma in yi wa Lilin Baba godiya. Domin ban taɓa tunani ba, ban kuma yi tsammani ba, kawai sai miƙo mani makulli ya yi ya ce mani ga mota. Wallahi sai na ga abin kamar a mafarki.
“Gaskiya babu abin da za mu ce masa sai dai Allah ya saka masa da alheri. Kuma Allah ya mayar sa da dubun alhairan da ya ke yi, domin shi mutum ne mai kyau, kuma idan ya yi ba ya so wani ma ya san cewa ya yi, kuma ya na yi ne domin Allah.”
To, yanzu dai Alfazazee ya yi bankwana da hawa mashin.
Lilin Baba mawaƙi ne wanda a yanzu kuma ya rikiɗe ya zama jarumi, kuma mai shiryawa. Shi ne ya shirya wannan fim ɗin mai dogon zango mai suna ‘Wuff’, wanda ake ɗorawa a YouTube ɗin sa mai suna Lilin TV.
Mawaƙin ya na ɗaya daga cikin mutanen da ya ke taimaka wa abokan sana’ar sa da kuɗi da sauran abubuwa don rage irin raɗaɗin da ake ji a masana’antar.