TSOHON mataimaki na musamman a ɓangaren farfaganda ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano kuma jarumi a Kannywood, Mustapha Badamasi Naburaska, ya bayyana dalilin da na ajiye muƙamin sa tare da komawa cikin rundunar Kwankwasiyya.
A lokacin tattaunawar sa da mujallar Fim a ofishin sa da ke Titin Audu Baƙo a cikin garin Kano, Naburaska ya ce akwai shawarar da ya ba Ganduje game da wani mawaƙi amma ya ƙi ɗaukar shawarar, wanda hakan ne ya sa da aka ci zaɓe ya tsallake ya koma inda ya fito, wato tafiyar Kwankwasiyya.
Jarumin barkwancin dai ya yi tsalle ya koma tafiyar Kwankwasiyya ne jim kaɗan bayan an bayyana Injiniya Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna da aka yi ranar Asabar da ta gabata.
Da dama mutanen gari su na ta tofa albarkacin bakin su da cewa lallai babu amana, yau Naburaska ne ya bar Gawuna? To yanzu ko ina labarin muƙamin sa na mataimaki na musamman a ɓangaren farfaganda na Ganduje?
A hirar sa da mujallar Fim a Kano, Naburaska ya amsa irin waɗannan tambayoyin, inda ya ce: “To ni a matsayi na a yanzu da na ke magana da kai na tsohon mai ba Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ko da yake na san wasu za su ce me ya sa na faɗi hakan, amma na fara kiran kai na da haka tun kafin mutane su fara kira na, saboda a yanzu an riga an yi zaɓe, Allah ya bai wa wanda ya nufa shi zai zama gwamna, don haka in ma ban kira kai na ba, nan gaba kaɗan rantsarwa za a yi a kafa sabuwar gwamnati, to ka ga wasu ne za su zo, mun zama tsofaffi. Don haka tun kafin lokacin na fara kiran kai na da haka.”
Dangane da taron da ya shirya da wasu su ke cewa na komawar sa Kwankwasiyya ne, cewa ya yi, “To, ni da man ba fita na yi daga Kwankwasiyya ba. Haka da na shirya walima na bikin Abba Kabir Yusuf ya ci zaɓe, ba dawowa Kwankwasiyya ba ne. Ni ɗan Kwankwasiyya ne. Aiki ne ya kai ni gwamnatin Ganduje kuma aka ɗauki muƙami aka ba ni.
“Shi kuma aiki idan aka ba ka, ka na tsakiyar aikin ma za ka iya ajiyewa ka ce ka daina domin ka je ka samu wani aikin na daban. Don haka walima da na haɗa ni ɗan Kwankwasiyya ne gaba da baya. Can aiki ya kai ni, kuma na gama aiki na dawo in da na ke, ba kuma don ba a buƙata ta ba ne sai dalilin wasu kurakurai da su ka faru da yawa wanda ba buƙata ta ba ne in cika surutu ba.
“Amma abin da zan kawo kaɗan don ya zama misali, Allah ya sani lokacin da mu ka ɗauko tafiyar nan da yadda ake yaƙin neman zaɓe, akwai wani mawaƙi wanda kowa ya sani ya yi waƙa ya ci mutuncin Gwamnan Jihar Kano da Gwamna Ganduje, amma haka mu ka riƙa yawo jiha-jiha mu na kare ƙima da martabar Gwamna Ganduje, mun shiga ko’ina lungu da saƙo. Amma lokaci guda sai kawai mu ka ga an daidaita da wannan mawaƙi ba tare da an tuntuɓe mu ba ko an yi shawara da mu ba.

“Sai da na kawo mutum 345 kuma dukkan su jiga-jigai ne a Kannywood da su ka isa. Amma yau saboda buƙata ta wani mawaƙi guda da aka daidaita da shi, sai aka wofantar da mutanen nan.
“Kuma na yi ta kiraye-kiraye da yin rubutu ta ƙarƙashin ofishi na na bai wa mai girma Gwamna Ganduje shawara. Kuma ni da kai na na je na samu mataimakin gwamna kuma ɗan takarar gwamna, na faɗa masa ga matsalar da ake ciki don ya sa a kirawo mu duka mu haɗu. Kuma ya yi mani alƙawarin amma sai alƙawarin ya ƙi cika.
“Don haka ya na ɗaya daga cikin abin da ya sa mutanen mu su ka ƙaurace wa wannan sabgar duka, saboda kowa ya riga ya yi fushi, saboda wannan mutumin ya ci mutuncin gwamnan Jihar Kano, kuma mutane sun zo su na kare gwamnati kuma an dawo da shi, kuma aka ji ya na cewa girman ka akwatin ka, sannan in ba ka ci akwatin ka ba, babu mai ɗaukar muƙami ya ba ka.
“To shi ya sa muka bar su da waɗanda za su kawo masu akwatin, da girman nasu da duk abin da su ke tunani, kuma aka yi addu’ar Allah ya zaɓa abin da ya fi alheri. Cikin waɗanda su ka yi addu’ar har da ni da Nasiru Yusuf Gawuna. Kuma ga shi Allah ya zaɓa abin da ya fi alheri, wato sabon gwamna, Abba Kabir Yusuf.”
A game da ziyarar da ya kai wa Kwankwaso, Naburaska ya ce: “Ai ba kai ziyara na yi ba. Da man gidan uba na ne, don haka ba wanda ya isa ya hana ni zuwa gidan uba na, don shi mai girma Rabi’u Musa Kwankwaso ya ɗauke ni a matsayin ɗa, na ɗauke shi a matsayin uba. Don haka duk lokacin da na ke so na shiga, zan shiga ne matsayin gidan uba na. A yanzu ma na kai masa mutane biyar zuwa shida, wanda kuma za a ci gaba da yaƙin neman shugaban ƙasa da izinin Allah.
“Don haka ni dai babban fatan da na ke yi, ina fatan Allah ya taimaki Abba Kabir Yusuf, kuma Allah ya ba shi abokan aiki na kirki.
“Kuma mu da mu ke gefe za mu ci gaba da bayar da gudunmawa da kuma shawarwari. Don ni a cikin wannan tsarin ba na buƙatar muƙami, kawai ni buƙatar da na ke da ita a yanzu na shiga saƙo da lungu ne don tallata takarar mai girma Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin takarar shugaban ƙasa a nan gaba.”
Duk wanda ya san Naburaska, ya san irin gwagwarmayar da aka yi da shi a zaɓen shekarar 2019, wanda a lokacin Abba ya na jam’iyyar PDP, babu irin surutai da Naburaska bai yi ba a wancan lokacin a kan rashin nasarar da ɗan takarar bai samu ba.
Da ma jarumin sarkin magana ne, wannan ya sa ya riƙa yin gajerun bidiyoyi ya na suka da yarfe a kan Gwamna Ganduje.
Da tafiya ta yi tafiya kuma sai ya koma ya yi mubayi’a ga Gandujen, wanda shi kuma ya naɗa shi mataimaki na musamman a ɓangaren farfaganda. Tun daga lokacin ya koma yabo da tallata dukkan abubuwan da gwamnan ya yi. Sannan da aka kaɗa gangar siyasa sai ya ci gaba da tallata ɗan takarar zama gwamna a jam’iyyar PDP, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, har zuwa lokacin zaɓe.
A baya, a daidai lokacin da mawaƙin siyasa Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) ya fice daga tafiyar Gawuna, ya koma tafiyar Sha’aban Sharaɗa, babu irin surutan da Naburaska bai yi ba; har cewa ya yi a gaban shi an ba Rarara kuɗi.
Naburaska ya ci mutuncin Rarara matuƙa a bidiyoyi mabambata da ya yi a lokacin, wanda hakan ya sa yaran Rarara su ka riƙa fitar da bidiyoyin Naburaskan a lokacin da ya ke tafiyar Kwankwasiyya ya riƙa cin mutuncin Ganduje da gwamnatin sa.
Sai dai kuma, kamar yadda wasu ke ganin mawaƙa da ‘yan fim ba su da kunya ko alƙibla, musamman a kan abin da ya shafi harkar siyasa, duk da cewa wasu daga cikin ‘yan fim da mawaƙa sun ɗauki harkar ne a matsayin hanyar neman kuɗi, ana sanar da Abba ya lashe zaɓe, sai Naburaska ya yi wuf ya dira gidan jagoran NNPP, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, inda ya kai masa ziyara tare da taya su murna, sannan kuma ya yi mubayi’a.

Haka kuma, shi ma mawaƙi Ado Isa Gwanja, wanda ya na ɗaya daga cikin mawaƙan da su ka tallata Gawuna a ƙungiyar su ta YBN Network Group, ƙarƙashin Abdul Amart, shi ma ya koma tsagin Abba bayan ya lashe zaɓe, inda har sun yi waƙar taya shi murna shi da abokin sa, Ali Isa Jita. Kuma shi ma ya je wajen Kwankwaso ya yi mubayi’a tare da Naburaska.
A ranar Laraba, 22 ga Maris, 2023 Naburaska ya shirya gagarumar walima, inda aka banƙare raguna na murnar komawar sa Kwankwasiyya tare da murnar cin zaɓen Abba.
Zuwa yanzu dai a Kannywood, Naburaska da Gwanja da Ali Artwork ne aka ji sun koma tafiyar Kwankwasiyya bayan lashe zaɓen Abba Kabir Yusuf, amma da alama wasu na nan za su biyo bayan su.
