• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Na dawo fagen waƙa gadan-gadan – Asiya Baba

by DAGA ABBA MUHAMMAD
September 3, 2022
in Mawaƙa
0
Asiya Baba

Asiya Baba

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ASIYA Baba tsohuwar mawaƙiya ce a Kannywood, amma kuma mawaƙa da dama na wannan zamani ba su san ta ba, sakamakon daina ganin ta da aka yi a masana’antar. Ta yi fice a shekarun baya lokacin da tauraruwar ta ke haskawa, musamman a Kaduna. Ta na ɗaya daga cikin manyan mawaƙa mata a garin, irin su marigayiya Halima ‘Yarzaki, Maryam Oloni, Maryam Kwangila, Fati Khalil da sauran su. Sai dai lokaci guda aka neme ta a industiri aka rasa. Haka kuma aka daina jin waƙoƙin ta gaba ɗaya. 

Kwanan nan wakilin mujallar Fim ya nemo mawaƙiyar, inda ya tattauna da ita game da ɓatan da ta yi a industiri da kuma inda ta sa gaba.

FIM: Ganin cewa ke tsohuwar mawaƙiya ce a fagen waƙa, amma kuma yawancin mawaƙan zamani ba su san ki ba, wataƙila sai dai sunan ki. Ki gabatar da kan ki ta yadda za a gane ki kafin mu ci gaba.

ASIYA BABA: Assalamu alaikum. Kamar yadda ka ambata, suna na Asiya Baba ko kuma in ce mutane sun fi kira na da Sayyada Asiya Baba. Ni haifaffiyar garin Kaduna ce, kuma zan iya cewa ni mawaƙiya ce a baya kuma a yanzu ma zan iya ce maka ni mawaƙiya ce. Wannan shi ne taƙaitaccen tarihi na.

FIM: Tsawon shekaru ina ki ka shiga?

ASIYA BABA: Gaskiya daga baya na janye daga tafiyar saboda ina so in tsaya in yi karatu na yadda ya kamata. Wannan shi ne ya ɓoye ni. Bayan kuma na kammala sai na yi tunanin babu mamaki ƙila har yanzu masoya na neman ina na ke, domin na kan samu saƙo, “Bba mu ga Asiya Baba ba. Ina waƙoƙin Asiya Baba?” Sai na ce bari in dawo. To yanzu na dawo wannan tafiya ɗari bisa ɗari.

FIM: Tsawon wane lokaci ki ka ɗauka ki na karatun?

ASIYA BABA: Na ɗauki tsawon shekara huɗu ina karatu. Na yi karatun NCE, kuma da ma za ka yi ‘cycle’ 1, 2, 3, 4. Yanzu da na kammala shi ne na dawo tafiyar gadan-gadan.

Sayyada Asiya Baba

FIM: Bayan kammala karatun naki, kin fara aiki ne? In ki na aiki, ya za a yi ki ci gaba da waƙa da kuma aikin naki?

ASIYA BABA: A yanzu haka ina koyarwa. Kuma koyarwa ba zai taɓa min harka ta ta waƙa ba, haka kuma waƙa ba za ta taɓa min aikin koyarwa na ba. Yanzu haka ni malamar makaranta ce. Wannan shi ne.

FIM: A baya waɗanne waƙoƙi ne ki ka yi, waɗanda duk wanda ya ji su zai gane cewa Asiya Baba ce ta rera su?

ASIYA BABA: Kai-tsaye dai akwai album ɗi na na yabo mai suna ‘Turbar Yabo’, a ciki akwai waƙoƙi kusan biyar. Bayan shi akwai ‘Mai Tsada’. Albums ɗin Asiya Baba kenan. Na san duk wanda ya tuna ‘Turbar Yabo’ da ‘Mai Tsada’ na tabbata zai tuna da Asiya Baba.

FIM: Tsawon lokacin da ki ka ɗauka ba ki harkar, yaya alaƙar ki ta ke da abokan sana’ar ki?

ASIYA BABA: Lokaci zuwa lokaci mu na haɗuwa da wasu mu gaisa ido da ido, wasu kuma su na kira na a waya, wasu kuma ‘online’ ta chat mu gaisa. Tun lokacin da na daina har zuwa yanzu ina da kyakkyawar alaƙa da abokan aiki na.

FIM: Ga shi kin dawo masana’antar. Za ki ga sababbin abubuwan da ba ki saba gani ba a baya. Za ki ga sababbin mawaƙa da sauran su. Ta yaya za ki fuskanci wannan ƙalubalen?

ASIYA BABA: E, ƙalubalen mai girma ne, saboda yadda ake tafiya a da, a yanzu an zamanantar da abin. Amma in-sha Allahu ina da ƙwarin gwiwar fuskantar tafiyar. Kuma ina fatan in Allah ya yarda zan samu nasara a kan ta.

FIM: A dawowar ki a yanzu waɗanne waƙoƙi ki ka yi?

ASIYA BABA: A dawowa na a yanzu na yi wata waƙar yabo da na yi wa laƙabi da ‘Rahamar Allah’, sai kuma wadda na yi a kan tsaro da na yi wa laƙabi da ‘Tsumagiya’. Waɗannan su ne manyan waƙoƙin da na ke alfahari da su.  

FIM: Wasu mawaƙa mata a yanzu idan su ka fara waƙa a Kaduna, daga baya sai su koma Kano. Akwai wasu waɗanda wataƙila kin yi zamani da su yanzu sun koma Kano saboda neman ɗaukaka ko ke ma ki na da tunanin haka?

ASIYA BABA: Ɗaukaka a hannun Allah ya ke; duk inda ki ka je ɗaukakar ki na wurin Allah. Saboda haka ba na tunanin cewa in canza gari. Duk inda ki ke Allah zai kawo maki ɗaukaka. Don haka ina nan a Kaduna, sai dai kuma idan ƙaddara ta zai sa in koma Kano. 

FIM: Bayan dawowar ki ɗin nan, an fara kiran ki ayyuka?

ASIYA BABA: E, ai tun da na dawo na sanar da mutane cewa in-sha Allahu na dawo tafiyar gadan-gadan. Kuma yadda aka karɓe ni wallahi na yi mamaki, na ce ashe ana so na har yanzu! Masha Allahu, na karɓu daga dawo na. 

FIM: A yanzu ki na da situdiyon da ki ke zama ko kuma ki na da ubangida?

ASIYA BABA: Kamar yadda na ke a baya, a wannan dawowar ma a haka na ke. Gaskiya ni ba na zaman situdiyo, sai dai idan za a yi aiki a neme ni. Maganar ubangida kuma, gaskiya da ba ni da ubangida, kuma ko a yanzu ba ni da ubangida. Amma kuma ba wai ba zan yi ba ne, da zarar na tantance wanda na ke so ya zama ubangida na ko kuma wani ya ga na dace ya zama ubangida na wanda zai ga ya dace in zauna a ƙarƙashin sa zai tallafa min in-sha Allahu zan karɓi hakan. 

FIM: Kasancewar kasuwar finafinai da waƙoƙi ta mutu, duk an koma intanet, ke wace hanya za ki bi don ganin ki na samun kuɗin shiga?

ASIYA BABA: Dawowar da na yi tunda na ga an zamanantar da abin, sai ni ma na yi ƙoƙari na zamanatar da ‘system’ ɗi na. Farko dai bayan na dawo sai na buɗe YouTube channel, bayan na buɗe sai na fara karanta littattafan Hausa. Cikin wannan tsarin sai na fara saƙa waƙoƙi na. To cikin saƙa waƙoƙin da na ke yi sai na ga mutane na karɓa. Wannan shi ne ‘system’ ɗin da na ɗauka, kuma in-sha Allahu zai ɓulle min.

FIM: Wane albishir ki ke yi wa abokan sana’ar ki?

ASIYA BABA: Ina yi wa abokan sana’a ta albishirin na dawo harkar ɗari bisa ɗari. Kuma in-sha Allahu za su same ni fiye da yadda su ka san ni a baya. Ina nan, ni ce dai Asiya Baban. Kuma kamar yadda na yi a baya, zan yi abin da ya fi haka. Wannan shi ne albishirin da zan yi masu.

FIM: A ƙarshe, mecece shawarar ki ga abokan sana’ar ki?

ASIYA BABA: Shawara ta ga abokan sana’a ta ita ce su samu natsuwa, babu mai yi sai Allah. Kuma duk abin da za ki yi ki riƙa tuna gaba, ki na kuma hangen bayan ki. Saboda haka ki tsaftace sana’ar ki, ki riƙe mutuncin ki. Komai lalacewar abu da zagin da ake yi idan ki ka tsare mutuncin ki, ki ka tsare kan ki, in-sha Allahu ba za ki samu matsala ba. Shawara dai kai-tsaye mu riƙe mutuncin mu, kuma mu san Allah ke yi.

FIM: Me za ki ce wa masoyan ki?

ASIYA BABA: Masoya na ina yi maku albishir cewa Asiya Baba ta dawo. Kuma a yanzu in-sha Allah zan yi maku abubuwan da za ku ji daɗi fiye da yadda ku ka ji daɗi a baya. Amma ina roƙon ku abu ɗaya: don Allah ku zama masu uzuri a gare ni. Sannan duk lokacin da na yi abin da bai dace ba, a neme ni a faɗa min cewa ban yi daidai ba, haka kuma a ba ni shawarwari da zan gyara. Idan kuma na yi abin da na yi daidai, ina buƙatar yabo daga gare ku.

FIM: Mun gode, Asiya Baba.

ASIYA BABA: Ni ma na gode.

Loading

Tags: Asiya BabadawowaKadunamawaƙayabo
Previous Post

Abin da ya sa ‘yan fim ke rungumar ‘yan siyasa a ƙungiyance – Gidaje

Next Post

Ina alfahari da baiwar da Allah ya yi mani a harkar fim – Hadiza Muhammad

Related Posts

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi
Mawaƙa

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi

April 19, 2025
Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala

October 28, 2024
Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala

July 16, 2024
Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara
Mawaƙa

Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara

May 13, 2024
Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 
Mawaƙa

Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 

December 7, 2023
Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala
Mawaƙa

Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala

December 3, 2023
Next Post
Hadiza Muhammad

Ina alfahari da baiwar da Allah ya yi mani a harkar fim - Hadiza Muhammad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!