• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Na samu harkar fim ba yadda na ke jin ta ba – Fatima Fulani

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
March 2, 2020
in Taurari
0
Fatima Muhammad Fulani

Fatima Muhammad Fulani

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
DUK da halin rashin cigaba da masana’antar finafinai ta Kannywood ta samu kan ta a ciki a ‘yan shekarun nan, kusan a kullum sai ta samu sababbin masu shigowa ciki, waɗanda su ka haɗa da jarumai maza da mata da kuma masu gudanar da wasu ayyukan.
 
Fatima Muhammad Fulani na daga cikin irin waɗannan sabbin fuskar. Ita ma ta shigo ba da daɗewa ba domin ta jarraba sa’ar ta, ta ga ko za  ta zama babbar jaruma kamar yadda wasu su ka shigo kuma su ka yi fice aka san su a duniya.
 
Jarumar, ‘yar shekaru 20 da haihuwa, an haife ta ne a Kano, kuma a nan ta yi karatun ta na firamare da na sakandare. A halin yanzu ta na karatun NCE a Kwalejin Sa’adatu Rimi da ke Kano.
 
A hirar da ta yi da mujallar Fim, Fatima ta faɗi dalilin ta na shigowa harkar fim da kuma yadda ta samu harkar, inda ta ce: “To ni dai zan iya cewa harkar fim na shigo ta ne domin sha’awa da kuma faɗakarwa, saboda yadda na ga jarumai su na bayar da gudunmawa wajen wayar da kan al’umma, don haka ne ma na ga zan iya bayar da tawa gudunmawar. 
 
“Amma dai da man tun tuni ina da sha’awar na shigo, to saboda karatu, don haka na san ko a gida ma ba za a bar ni ba, don haka sai yanzu ne na samu damar shigowa, don yanzu ma ban fi wata biyu zuwa uku ba.”
 
To ko yaya ta yi wajen shigowar? Fatima ta amsa, “Da man akwai Abdullahi Aji Fafa, shi ne mu ke maganar da shi ya ke cewa da ni ya kamata na yi harkar don za ta dace da ni, to kuma da ya tashi yin fim sai ya saka ni a ciki. 
 
“A lokacin ma ni abin wasa na ɗauke shi, amma dai da Allah ya sa zan yi sai kawai na je na fara.”
 
Sabuwar jarumar ta faɗi yadda ta ji a lokacin da aka saka ta a fim: “Gaskiya abin ya zo mini da bazata, don sai na ji kamar ba zan iya ba. Amma dai a haka na daure har na yi abin da aka saka ni, amma dai da na zo yin na biyu to sai abin ya fi na baya, don sai na ji har na saba. Don har waɗanda su ke wajen ma sai da su ka yi mamaki na saboda ƙoƙarin da su ka ce na yi.”
 
Ya zuwa yanzu dai ta yi fim biyu, ciki har da wani mai suna ‘Ɗan Malam,’ inda ta fito a matsayin ƙanwar Sadiq Sani Sadiq, sai kuma ‘So Da So’ inda ta fito a matsayin budurwa.
 
Bayan waɗannan, akwai kuma waƙoƙi da ta yi.
 
Da mujallar Fim ta tambaye ta yadda ta samu harkar fim ɗin baki ɗaya, sai ta ce, “To gaskiya yadda na samu harkar fim ɗin ba kamar yadda na ke jin ta ba kafin na shigo. Na san dai komai na rayuwa za ka samu mutane nagari kuma akwai waɗanda ba nagari ba, don haka ni dai yadda na samu harkar fim abin ya burge ni.”
 
Kowane mutum ya na da wani buri a harkar da ya saka a gaba. Menene burin Fatima a cikin masana’antar fim?
 
Amsa: “To babban buri na dai kamar yadda na faɗa maka a baya shi ne faɗakarwa, don haka ina fatan ta silar fim ɗin da zan yi, mutane su farka daga abubuwan da su ke marasa kyau.
 
“Don haka na ke fatan na zama babbar jarumar da za a san ni a duniya ta hanyar wayar da kan jama’a.”
 
Ko Fatima ta taɓa yin aure?
 
“To gaskiya ban taɓa yin aure ba sai nan gaba.
 
“Don haka ina fatan yadda na shiga harkar nan lafiya na fita lafiya, yadda zan samu na yi aure cikin kwanciyar hankali.”
 
Daga ƙarshe, kyakkyawar jarumar ta bada wata shawara ga masu son shigowa harkar fim. Ta ce: “Ni dai shawarar da zan ba su ita ce su shigo da kyakkyawar niyya, shi ne zai sa su kare mutuncin su.
 
“Kuma su ɗauka faɗakarwa su ka zo yi ba wai su zubar da mutuncin su ba, domin duk inda mutum ya kare mutuncin sa to ƙimar sa ba za ta taɓa zubewa ba.”

Loading

Previous Post

Cutar ‘Coronavirus’: Aikin Firgitarwa Don Siyasa Ko Neman Kuɗi?

Next Post

Umar M. Shariff: Nasihar mahaifin mu kafin ya rasu jiya

Related Posts

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Sayyada Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi)
Taurari

Fim riga ce ta arziki – Raihan Imam Ƙamshi

November 20, 2023
Saratu Abubakar
Taurari

Yadda ɗaukaka ta sa na ke rufe fuska – Saratu Abubakar

October 1, 2023
Safna Lawan
Taurari

Buri na a Kannywood ya kusa cika, inji Safna Lawan

August 24, 2023
Cewar Fanan Buzuwa: "Ba zan iya auren ɗan fim ba"
Taurari

‘Yan fim kada mu riƙe sana’a ɗaya – Fanan Buzuwa

June 11, 2023
Next Post
Marigayi Malam Muhammad tare da ɗan sa Umar M. Shariff a wani lokaci can baya

Umar M. Shariff: Nasihar mahaifin mu kafin ya rasu jiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!