• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Na sha ƙalubale a Kannywood – Rahama A. Ibrahim, jarumar da ta musulunta

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
August 1, 2021
in Taurari
1
Na sha ƙalubale a Kannywood – Rahama A. Ibrahim, jarumar da ta musulunta
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

RAHAMA A. Ibrahim, sabuwar jarumar nan wadda kallon finafinan Hausa ya sa ta shigo addinin Musulunci, ta bayyana cewa ta fuskanci ƙalubale a gida saboda ta karɓi Musulunci, haka kuma ta fuskanci ƙalubale da ta shigo industiri. Bugu da ƙar, akwai wani babban buri da ta ke so ta cimmawa. 


Kun dai ji wani yunƙuri da haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa ta Nijeriya (MOPPAN) ta ce za ta yi don sama mata kyakkyawan yanayi a Kano. To, bayan kammala taron da MOPPAN ta yi da ita a shekaranjiya ne mujallar Fim ta tattauna da jarumar ‘yar asalin garin Kumo da ke Jihar Gombe. A hirar, ta bayyana cewar ta yi makarantar firamare da sakandire tare da makarantar gaba da sakandire inda ta samu shaidar ƙaramar Diploma a kan duba muhalli, wato ‘Community Health’ a turance. 

Ga yadda tattaunawar ta kasance:

FIM: Rahama, me ya ja hankalin ki ka shigo harkar fim?

RAHAMA A. IBRAHIM: To, da man dai tun farko ni ba Musulma ba ce, ni Kirista ce kuma ana kira na da Judith A. Ibrahim. Na taso a gidan malamai na addinin Kiristanci. To haka dai Allah ya sa mun son kallon finafinan Hausa har ta kai ga ina kllon wasu finafinan da su ke fito da kyawawan ɗabi’un Musulunci. Ta hanyar haka ne kuma su ka ba ni sha’awa har na ji ina ƙaunar na shiga Musulunci har ma na yi sha’awar shigowa ita karan kan ta masana’antar domin in faɗi abin da addinin ya yi min.

FIM: Tun tsawon wane lokaci ne ki ka shiga Musulunci sannan kuma wane irin ƙalubale ki ka samu tsakanin ki da iyayen ki ko ‘yan’uwan ki?

RAHAMA: Kusan shekara ta ta uku kenan da shiga wannan addinin na Musulunci.Na gamu da matsaloli ko in ce ƙalubale da dama daga wurin ‘yan’uwa na har ma da mahaifiya ta wadda a da ta daina yi mani magana; ko na yi mata magana ba ta mayar min. Sannan su kuma ‘yan’uwa na su ka tsane ni tare da ƙoƙarin kai ni wajen da ake yin hukunci wanda da a ce an samu nasarar yi mani hukunci kan wannan abu da na yi na barin addinin mu da tuni an juya mini tunani ko kuma an kulle ni, ba wanda zai san yadda na ke. Cikin taimakon Allah da taimakon mahaifiya ta, na tsallake wannan tarkon.

Duk da cewa mahaifiya ta ta yi fushi da ni lokacin da na shiga Musulunci, amma gaskiya daga baya ita ce wacce ta dinga ba ni kariya a duk lokacin da aka yi yunƙurin zuwa a kama ni, wanda mu ka yi ta haka har na tsawon shekara ɗaya, kafin daga bisani na samu wata dama na gudu daga garin, na zo nan Kano.

FIM: Lokacin da ki ka zo Kano da zummar za ki shiga wannan masana’anta ta Kannywood, da man kin san wani ne a nan ko kuma ku na da wasu ‘yan’uwa haka?

RAHAMA: Gaskiya ni ban san kowa ba a Kano, kawai dai na zo ne ina lalube wanda har ta kai ni zuwa yanzu. Amma kuma fa ba na iya sati biyu ban je gidan mu ba na ga mama na, domin abin da ban faɗa ba shi ne baba na Allah ya yi masa rasuwa tun ina yarinya.

FIM: A matsayin ki na baƙuwa a wannan masana’anta, wane irin ƙalubale ki ka samu da jarumai da masu shirya finafinai?

RAHAMA: Gaskiya na sha fama da wahala sosai, saboda na fuskanci ƙalubale da dama. Na faɗa hannun mutanen da gaskiya ba su da imani, amma daga ƙarshe Allah ya haɗa ni a hannun waɗanda su ka taimaka min kuma su ka ɗauke ni  har  kawo wannan matakin a yanzu. Na haɗu da wasu daraktoci waɗanda na same su a kan zan shiga wannan harka ta fim, na yi zaton cewa darakta shi ne sama da kowa, wanda ni ban san yadda karatun ya ke ba, a inda wasu su ka guje ni, wasu kuma ba su karɓe ni ba har ma da waɗanda su ka cuce ni ma, don na bada kuɗi bila adadin. 

FIM: Zuwa yanzu a tsawon shekara biyu da ki ka yi a wannan masana’anta, finafinan ki nawa?

RAHAMA: Bayan da na shigo har na samu waɗanda su ka karɓe nI da hannu biyu-biyu tare da yi mani wani fim, kuma ikon Allah fim ɗin ya na tafiya ana kuma kallon sa. Wasu kuma finafinan da na yi akwai irin su ‘Tawagar ‘Yan Mata’ da ‘Bautar Zuciya’, da dai sauran su da ba zan iya lissafawa ba.

Rahama A. Ibrahim

FIM: Tsawon wane lokaci ki ka ɗauka a garin ku kafin ki dawo nan Kano?

RAHAMA: Gaskiya a lokacin da na shiga addinin Musulunci ba a nan take na bar garin mu ba, amma ban samu ƙofar fita ba saboda ba hali domin an sa masu sa ido a kai na. Sannan da na ɗan samu ƙofa sai na fito na bar garin na dawo Kano. Kuma ba zan iya sati ban ga mahaifiya ta ba gaskiya saboda ba zan iya rayuwa ba in ba ita.

FIM: Wane buri ki ke da shi a wannan masana’anta ?

RAHAMA: Burin da na ke so na cimma a cikin wannan masana’anta gaskiya bai da yawa ko ma in ce guda ɗaya ne: tunda ni fim ne gata na, wato shi ne dalilin da ya zamto silar shiga ta addinin Musulunci, shi ne na ga wani ma mai irin tunani irin nawa shi ma zai iya zuwa ya karɓi Musulunci domin shi ma ya samu dama.

FIM:  Ya batun aure kuma?

RAHAMA: To, aure sai Allah ya kawo miji saboda ana cikin wani yanayi, dole sai ka samu miji nagari wanda ya san addini da tarbiyya, ba kuma zai tsangwame ka ba, tunda ni ka ga ban san addinin Musulunci sosai ba. To kuma a yadda na ke gani a maƙwabta aure sati ɗaya ko biyu ya mutu, to shi ne kawai tsoro na gaskiya.

FIM: Da me za ki ƙarƙare wannan tattaunawar tamu?

RAHAMA: Kira zan yi ga ‘yan masana’antar nan mu koyi haɗin kai, kuma ina roƙon Allah ya ƙara haɗa mana kan mu baki ɗaya. 

Sannan akwai wasu ƙananan masifu da su ke tasowa, dole sai an yi haƙuri, sai da yawaita addu’a da riƙe Allah.

Rahama ta ce burin ta shi ne: “… na ga wani ma mai irin tunani irin nawa shi ma zai iya zuwa ya karɓi Musulunci”.

Loading

Tags: hausa filmsKannywoodKumoMOPPANRahama A. Ibrahim
Previous Post

Rasuwar dattijuwar Kannywood Umma Ali: ‘Yan fim sun bayyana alhini

Next Post

Da ɗumi-ɗumi: Tsohuwar shugabar furodusoshi mata, Umma Ali, ta kwanta dama

Related Posts

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Sayyada Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi)
Taurari

Fim riga ce ta arziki – Raihan Imam Ƙamshi

November 20, 2023
Saratu Abubakar
Taurari

Yadda ɗaukaka ta sa na ke rufe fuska – Saratu Abubakar

October 1, 2023
Safna Lawan
Taurari

Buri na a Kannywood ya kusa cika, inji Safna Lawan

August 24, 2023
Cewar Fanan Buzuwa: "Ba zan iya auren ɗan fim ba"
Taurari

‘Yan fim kada mu riƙe sana’a ɗaya – Fanan Buzuwa

June 11, 2023
Next Post
Da ɗumi-ɗumi: Tsohuwar shugabar furodusoshi mata, Umma Ali, ta kwanta dama

Da ɗumi-ɗumi: Tsohuwar shugabar furodusoshi mata, Umma Ali, ta kwanta dama

Comments 1

  1. Pingback: Na sha ƙalubale A Kannywood – Rahama A. Ibrahim, jarumar da ta musulunta – HausaLoaded.Com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!