• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Na sha gamuwa da masu sha’awa ta – Nafisa Salisu, jarumar ‘Macen Sirri’

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
March 16, 2021
in Taurari
3
Na sha gamuwa da masu sha’awa ta – Nafisa Salisu, jarumar ‘Macen Sirri’
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

NAFISA Salisu matashiyar jaruma ce a Kannywood. Jarumar, wadda ake yi wa laƙabi da Sarauniya, kyakkyawa ce wadda kuma ta nuna ƙwarewa a aktin. Duk da yake ta fito a wasu finafinai da waƙoƙi a baya, amma ta fara shanawa ne lokacin da ta fito a matsayin ƙanwar Sahabi Madugu ɗan jarida a shirin ‘Kwana Casa’in’ na gidan talbijin na Arewa24. A yanzu kuma an ƙara sanin ta saboda ita ce jarumar shirin nan mai dogon zango mai suna ‘Macen Sirri’ wanda ake haskawa a YouTube. Fitowar ta a wannan shirin ya sanya mutane da dama su ke so su san ko ita wace ce, wato tarihin ta.

To, mun yi sa’a, kwanan nan ta tattauna da mujallar Fim a game da tarihin nata da yadda aka yi ta shigo wannan masana’anta ta shirya finafinai, kamar haka: 

FIM: Masu karatu za su so sanin wacece Nafisa Salisu.

NAFISA SALISU: To ni dai an haife ni a cikin garin Kano, sannan na yi makarantar firamare gami da sakandire a Excellence Classic College da ke unguwar Hotoro. Iyaye na ba ‘yan Jihar Kano ne su ba, ‘yan Jihar Kogi ne wanda kuma kasuwanci ya kawo su nan, sannan ni yaren Igala ce.

Bayan na kammala sakandire ne kuma na fara sha’awar shiga harkar fim, a inda na samu nasarar shiga a 2017, da kuma yaddar iyaye na. Sai dai kafin in fara yin fim na samu ƙalubale da dama, musamman wurin mahaifi na wanda da farko da na zo masa da maganar zan fara fim bai amince ba. Haka na haƙura, sai daga baya na fara nuna masa cewa ga matasa nan mata masu tasowa a cikin harkar kuma sun ɗaukaka. Da haka da haka na fara shawo kan sa har ya yarda tare da gargaɗi na a kan cewa na kare mutunci na.

FIM: Ta hannun wa ki ka shigo Kannywood?


NAFISA SALISU: E to, gaskiya farko Ali Gumzak na fara sani a masana’antar Kannywood sakamakon mu na catin da shi a Facebook kuma ina nuna masa sha’awa ta na son shiga masana’antar fim ta Kannywood. Amma fa ba mu taɓa haɗuwa da shi a fili ba sai a wani lokaci sun je lokeshin kusa da wani asibiti, ya kira ni ya ce min ina ina, na ce masa mu na kusa da asibitin da su ke. A nan ne na je mu ka fara haɗuwa, sai na gaya masa ga shi ga shi. Sai ya ce yanzu abin da za a yi shi ne na fara sayen fom sannan na kawo hotuna na; ya dai gaggaya mani hanyoyin da ake bi. 

Haka dai na sayi fom na yi ƙananan hotuna na kai mishi. To tun daga lokacin idan ana wani aikin haka zai kira ni don in je in ga yadda ake wannan sana’a na kuma koya domin akwai ranar da ni ma za a kira ni na yi.

FIM: Zamantowar ki baƙuwa a cikin wannan masana’an ta, ga ki kuma mace, ko akwai wani ƙalubale da ki ka fuskanta a farko-farkon shigowar ki, musamman wasu su nuna su na da sha’awa a kan ki?


NAFISA SALISU: To ai irin wannan rayuwar babu inda za ka je da ba za ka fuskanci irin wannan matsalar ba, ba ma a  masana’antar Kannywood ba ko a ma’aikatun gwamnati ka je; kai, ko wani kasuwanci ka ɗan buɗe shago ka na samun jama’a su na zuwa, dole akwai wanda za su yi maka maganar da ba za ta yi maka daɗi ba. Wani sai ya zo maka da wata manufa ta daban. Wannan ni a gani na ya zama dole.


FIM: Ki na nufin kin ci karo da irin waɗannan mutane kenan?


NAFISA SALISU (dariya): Uhmm! Gaskiya na ci karo da irin su. Sannan kuma duk wanda ya nuna mani haka a matsayi na na wadda ta shigo harkar na ke son kuma harkar, haka zalika na ke son na yi abin, ka ga ba zai yiwu mutum ya nuna mun ga irin abin da ya ke so da ni kawai na fito na yi masa rashin kunya ba, kawai dai ina fitowa na gaya wa mutum cewa kawai ka yi haƙuri ni ba na irin wannan harkar sannan ba don ita na shigo Kannywood ba.

FIM: A matsayin ki na sabuwar jaruma, a iya cewa ba a taɓa ɗora maki kyamara ba, amma ya aka yi lokacin da aka fara sa maki kyamara?


NAFISA SALISU: Abdul’aziz Ɗansmall shi ya fara dasa mani kyamara yayin ɗaukar wata waƙar gaɗa da za mu yi ‘background’. Da aka ce na yi murmushi, na kasa! Sun yi iya ƙoƙarin su amma na kasa yin murmushi ko fara’a.


Sai kuma lokaci na biyu wanda waƙa ta ce ta kai na wacce mu ka yi da Ali Ali. Shi ma haka na kasa yin ‘yar fara’ar nan da ‘yan mata su ke yi, har ta kai sai da na ce masa kawai ya sa mun wani a kusa da kyamarar ya dinga sa ni dariya. Duk da hakan ma abin mamaki aka yi aka yi na yi fara’ar amma na kasa, sai haƙura aka yi aka ɗauki waƙar a haka. Daga nan kuma shi kenan sai na dawo daidai, ba na jin wani tsoro ko wani abu in aka sa mini abin ɗauka.


FIM: Da wane fim ko waƙa ki ka fara?


NAFISA SALISU: Na fara da waƙa wadda tun da fari wata jaruma ta hau waƙar daga baya kuma na sake hawa waƙar, wato waƙar ‘In Ana Dara’. Sai kuma  fim mai suna ‘Asiya’ wanda kamfanin Global Times Movies su ka ɗauki nauyi a shekarar 2019.

FIM: Bayan yin fim ɗin ki na farko, shin ko furodusoshi ko daraktatoci sun nuna sha’awar su na kiran ki ki yi masu fim?


NAFISA SALISU: Ana yawan kira na, domin na fito a cikin bidiyon waƙoƙi haka da kuma ɗan fitowa a fim haka bai fi na yi fitowa ɗaya zuwa uku ba saboda ka san ni ɗin sabon shiga ce, sai a hankali.

Nafisa Salisu (Sarauniya), jarumar shirin ‘Macen Sirri’


FIM: Duba da yadda yanzu masana’antar kusan kacokam ta koma yin finafinai masu dogon zango (series), shin ko ke ma ki na irin waɗannan finafinan?


NAFISA SALISU: E, ina yin fim mai dogon zango. Ga duk masu bibiyar shirin talbijin na Arewa24 akwai wani fim da ake yi mai dogon zango mai suna ‘Kwana Casa’in’, na fito a matsayin ƙanwar Sahabi ɗan jarida. Sannan ina yin wani wanda shi wannan ma ni ce na ke jan ragamar fim ɗin mai suna ‘Macen Sirri’.


FIM: Duk da cewa a mafi yawan lokuta idan aka ce ga wance ta na fim, a unguwa za ki ga wasu su na yi mata wani kallo. Shin a naki ɓangaren yaya abin ya ke?


NAFISA SALISU: Ba zan ce ba a yi ba, amma dai ni gaskiya ban fuskanci haka ba. Hasali ma duk inda na shiga za ka ji ana kira na da sunan waƙar da na hau ta ‘In Ana Dara’. Sai kuma bayan na fara fim ɗin ‘Kwana Casa’in’ sai mutane su ka fara kira na da ƙanwar Sahabi Madugu. Abin ma bai yi yawa ba sai lokacin da na fara wannan fim ɗin da na ke jagoranta na ‘Macen Sirri’, a nan na fara jin abin da waɗanda su ka shahara su ke ji.


FIM: Shin Nafisa na da aure?


NAFISA SALISU: A’a, ba ni da aure kuma ban taɓa yi  ba. Amma ina da niyyar yi in-sha Allahu.


FIM: Bayan harkar fim akwai wata sana’a da ki ke yi?


NAFISA SALISU: Bayan harkar fim ina aikin gyaran gashi da kuma yin ɗinki. Da man kuma shi na gada daga gurin mahaifiya ta.


FIM: Da me za ki ƙarƙare a ƙarshe?


NAFISA SALISU: To a ƙarshe ina yi wa masoya na fatan alkhairi tare da yin kira ga jarumai iri na masu tasowa, musamman yadda wasu su ke yi wa manya rashin kunya, wato ina nufin waɗanda su ka daɗe a cikin wannan masana’antar saboda rashin kunya ba abu ne mai kyau ba. Kuma ko da a ce a yanzu ka fi su samun wani abu, mutum ya na tunawa su ma a lokacin su su ma sun samu, kamar yadda su ka ja baya to kai ma wata ran haka za ka koma. Kuma duk abin da mutum ya yi sai an yi masa, idan kuma aka yi ma bai zama lallai ka ji daɗi ba. Na gode.

Nafisa Salisu a lokeshin
Nafisa Salisu jaruma ce mai tasowa
Previous Post

An fara rukunin ‘C’ na shirin N-Power tare da matakan da matasa za su bi

Next Post

Ba abin da marigayiya Rabi’atu S. Haruna ta fi so kamar yabon Annabi, inji mijin ta

Related Posts

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Sayyada Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi)
Taurari

Fim riga ce ta arziki – Raihan Imam Ƙamshi

November 20, 2023
Saratu Abubakar
Taurari

Yadda ɗaukaka ta sa na ke rufe fuska – Saratu Abubakar

October 1, 2023
Safna Lawan
Taurari

Buri na a Kannywood ya kusa cika, inji Safna Lawan

August 24, 2023
Cewar Fanan Buzuwa: "Ba zan iya auren ɗan fim ba"
Taurari

‘Yan fim kada mu riƙe sana’a ɗaya – Fanan Buzuwa

June 11, 2023
Next Post
Ba abin da marigayiya Rabi’atu S. Haruna ta fi so kamar yabon Annabi, inji mijin ta

Ba abin da marigayiya Rabi'atu S. Haruna ta fi so kamar yabon Annabi, inji mijin ta

Comments 3

  1. Kabiru usman ahmad says:
    4 years ago

    Labari yayi

  2. Kabiru usman ahmad says:
    4 years ago

    Labariyayi

  3. Abdulmajeed Abubakar says:
    4 years ago

    Ta yi kokari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!