FITACCIYAR jaruma Nafisa Abdullahi ta sake tayar da ƙura a soshiyal midiya, inda ta yi kira ga masu haihuwar ‘ya’ya ba tare da kula da su ba da su guji yin haka.
Jarumar ta bayyana haka ne a wani saƙo da ta wallafa a shafin ta na Tuwita ranar Asabar, 16 ga Afrilu, 2022 inda ta ce, “Ku daina haihuwar ‘ya’yan da ku ka san ba ku da halin kula da su.”
Ta ƙara da cewa, “Allah zai tuhumi mutanen da su ke haifar ‘ya’ya ba tare da sauke nauyin da ya ɗora masu ba.
“Kun ga dukkan mutanen da ke haifar ‘ya’yan da ba su ji ba, ba su gani ba domin kawai su aika da su almajiranci, kuma su ci gaba da haifar ƙarin ‘ya’ya, Allah sai ya saka wa yaran nan!”
Nafisa ta bayyana matuƙar ɓacin ran ta kan yadda wasu iyayen su ke tura ‘ya’yan su ‘yan shekara biyu zuwa uku almajiranci.
Jarumar ta taɓo inda ke yi wa jama’a da dama ƙaiƙayi, domin wannan lamari ne da ya daɗe ya na ɓata wa mutane da dama rai, musamman ganin cewa wasu na zargin ana amfani da irin waɗannan yara wajen aikata laifuka.
Sai dai kalaman jarumar sun tada ƙura matuƙa, domin sun jawo ce-ce-ku-ce, inda wasu ke yabon ta, wasu kuma na sukar ta.
A shekarun baya akwai wasu daga cikin gwamnonin Arewa da su ka so a dakatar da barace-barace, musamman irin na makarantun allo, sai dai a lokacin waɗanda ke da ruwa da tsaki a harkar makarantun allo su na ganin kamar za a toshe masu hanyar cin abincin su ne, har wasu daga cikin manyan ke faɗin cewa gwamnati ta na shirin faɗa da Allah ne in dai su na hana bara.
Amma kuma in aka koma magana ta gaskiya, akwai matsaloli da dama a cikin lamarin. Domin mutum ne zai haifi sama da ‘ya’ya goma, amma dukkan su bai san yadda su ke rayuwa ba, ya ɗauke su ya kai su wani gari karatun allo, a can ɗin kuma sai sun yi bara kafin su ci abinci. Wasu yaran ba su wuce ‘yan shekara uku zuwa biyar ba.
Don haka idan aka dubi maganar da Nafisa Abdullahi ta yi, lallai ta na da gaskiya. Dole mahukunta su dubi wannan lamari don neman yadda za a magance shi.