BABBAN jarumi, furodusa kuma marubuci Malam Ado Ahmad Gidan Dabino ya bayyana cewa nasarar da ya samu kwanan nan ta zama na ɗaya a wata gasa ta ƙasa baki ɗaya mai suna ‘Nigerian Most Respected CEOs Awards’, ba tasa ba ce shi kaɗai, ta masana’antar Kannywood ce ko ma Arewa baki ɗayan ta.
Gidan Dabino ya bayyana haka ne a hirar sa da mujallar Fim bayan ya dawo daga taron karramawar gasar wanda aka yi a Abuja ran Asabar da ta gabata inda ya doke mutum 12 da su ka shiga gasar daga ko’ina a Nijeriya.
Ita dai wannan gasa an yi ta ne a soshiyal midiya inda aka ba mutane damar su zaɓi jarumin da ya yi masu ta hanyar cike fom a intanet, ba tare da an san wajen da mai zaɓen ya ke ba.
Gidan Dabino ya halarci taron don karɓar tasa kyautar.
Bayan dawowar sa, mujallar Fim ta tuntuɓe shi domin jin ta bakin sa game da taron.

Jarumin ya fara bayani ne kan yadda gasar ta ke, ya ce: “To, ita wannan gasa dai ana kiran ta da ‘Nigerian Most Respected CEOs Awards’. Kuma ana zaɓar mutane ne ta hanyar ‘online’ a ce a jefa musu ƙuri’a. Kuma ina cikin mutane goma sha uku waɗanda aka zaɓo a cikin masu harkar fim. Kuma dukkan su ma daga kudancin Nijeriya su ke, ni kaɗai ne ɗan Kannywood.
“Saboda haka da aka jefa ƙuri’a, ni na samu mafi rinjaye, wadda hakan ta sa aka ba ni kyauta a matsayin wanda ya yi nasara a gasar.
“Kuma ka gane, a kowane matsayi ana zaɓar mutum ɗaya da ya yi nasara ne, don ba a kan fim kaɗai aka yi ba. An yi a kan noma, an yi a kan injiniya, an yi a kan ƙirƙira da kwalliya. Haka dai abin ya kasance, maza da mata.
“Kowane ɓangare na sana’a mutum ɗaya ake zaɓa. Amma dai ina ganin mu a ɓangaren fim, mu mu ka fi kowa yawa da har mu ka kai mu goma sha uku, don a sauran duk babu waɗanda su ka kai haka a cikin waɗanda su ka shiga gasar.”
Da mu ka tambaye shi ko me ya bambanta wannan karramawar da sauran waɗanda aka saba yi masa a baya kuwa, cewa ya yi: “To, abin da ya bambanta su shi ne su waɗanda su ka shirya wannan gasa ba su san ni ba, ban san su ba. Kuma ni ban ma taɓa jin labarin su ba, sai daga lokacin da na ga an sako hotunan mu mu goma sha uku kuma an tura aka ce mutane su jefa musu ƙuri’a.
“Kuma su asali su na da ofishin su ne a Legas, su na da shi a Abuja da Ghana, don haka su na shirya taron ne a duk in da ofishin su ya ke.
“Kuma bambancin shi ne ban da taron ‘WAMMA Awards’ da aka yi a Nijar ban taɓa karɓo wata kyauta daga nesa ba; mafi yawa ba ta wuce Abuja, Kaduna, Kano, Sokoto, da sauran wurare, amma ban taɓa zuwa kudancin Nijeriya don karɓar kyauta ba sai a wannan karon. To wannan shi ne ya bambanta su.
“Sannan kuma wani abu da aka yi na bambancin an shigar da mutane ne ta yadda masoya za su jefa ƙuri’a su zaɓa, ba waɗanda su ka shirya abin ba, don haka sun tura ne, kuma da su ka tattara su ka duba wanda ya fi kowa yawan jama’a, to shi ne bambancin, ba kamar gasar fim da za a zaɓi jarumi ba ta hanyar alƙalanci.”
Gidan Dabino ya yi nuni da muhimmancin wannan nasara da ya samu ga masana’antar Kannywood baki ɗaya, ya ce: “Abin da zan faɗa, mutane, musamman ‘yan fim na Kannywood, su sani wannan gasa da na samu nasara ba nasara ta ce ni kaɗai ba, ta masana’antar finafinai ta Kannywood ce duka, domin kuwa akwai jarumai da furodusoshi da daraktoci da su ka zo daga Kudu, amma ni kaɗai aka zaɓa daga Arewa kuma ɗan Kannywood da ake ganin an fi mu iyawa. Don haka mutane su ɗauki wannan gasa tasu ce. Don kuwa bayan gasar na je da fim ɗin ‘Juyin Sarauta’ an haska shi a wajen, kuma abin ya burge su, su na ganin fim ɗin ya bambanta da waɗanda su ka saba gani na Kannywood na rawa da waƙa, don haka sun yaba da aikin.

“To, ka ga za mu iya yi idan mun dage, kuma za mu iya yin takara da waɗanda su ke ganin sun sha gaban mu.
“Don haka kiran da zan yi shi ne a samu haɗin kai ko haɗin gwiwa na kamfanoni ba ɗaya ba, a samu wasu kamfanoni da za su haɗu su yi babban fim wanda za su fitar da mu kunya, a daina raina mu, domin mu na da labarai masu yawa da ingancin da za mu iya nuna shi a duniya. Ina ganin wannan shi ne kiran nawa.”