FURODUSA kuma darakta a Kannywood, Malam Sani Muhammad Sani, ya ƙaryata masu cewa ‘Abin Sirri Ne’ fim ɗin Ali Nuhu na farko.
Sani, wanda ya yi fice a Kannywood tun farkon kafa ta, ya yi wannan kalami ne bayan ya karanta wani taƙaitaccen tarihin Ali Nuhu da aka bayar a Facebook.
Sani mazaunin Jos ne a farkon kafa Kannywood, inda ya shirya finafinai da dama har ya fito a wasu daga cikin su a matsayin jarumi, amma daga baya ya koma Kano da zama.
Haka kuma shi ne wakilin mujallar Fim na Jos a tsawon shekaru daga shekarar 1999. Daga baya ya zama wakilin jaridu da su ka haɗa da Leadership, Blueprint, da Nation a jihohin Yobe, Bauchi, da Zamfara a lokuta daban-daban.
A martanin da ya wallafa a Facebook a yau, daraktan ya ce, “Ƙarya ce tsantsa idan Ali Nuhu ko muƙarraban sa su ka ce fim ɗin sa na farko shi ne ‘Abin Sirri Ne’. Idan wani ya ce fim ɗin Ali Nuhu ne na farko a matsayin babban jarumi, babu laifi.
“Idan mutane su ka cimma da yawa a rayuwar su, sai a riƙa canza tarihin su, musamman ma dai a Nijeriya.”
Sani ya ci gaba da cewa, Ali Nuhu “ya fara a fim ɗi na mai suna ‘Jumma’ ne, ba a matsayin jarumi ba, sannan ya yi ”Yancin Ɗan Adam’ na Waziri Zaiyanu, kafin ya shiga wasu finafinan Nollywood, inda ya yi wasu ƙananan rol a Jos kafin ya koma Kano riƙe da sikirif ɗin ‘Abin Sirri Ne’ da ‘Dijengala’ lokacin da wani furodusa ya baƙanta masa rai da aka gabatar masa da waɗannan sikirif ɗin.
“Ali Nuhu ya je Kano da sikirif ɗin biyu ne cikin ɓacin rai lokacin da furodusan ya ƙi shirya fim ɗin saboda duhun launin fatar Ali Nuhu. Ya fi so a sa ɗan wasa mai hasken launin fata ya ja fim ɗin, Ali Nuhu kuma ya dage kan cewa lallai sai ya ja finafinan.”
Sani ya ce, “Ali Nuhu ya taɓa faɗa mani cewa ya ɗauko sunan ‘Abin Sirri Ne’ daga wata magana da na ke yawan furtawa a kai a kai. Ina furta wannan kalamin a kusan kowace magana a lokacin.”
Ya ƙara da cewa, “Abin takaici ne yadda ake gurɓata da lalata tarihin rayuwa a Nijeriya saboda marubuta ba su damu su yi tafiya domin su binciko sahihan bayanai kan mutumin da za su rubuta tarihin sa, ko kuma marubucin ya na so ne ya gamsar da wanda ya ɗauke shi aiki ko kuma wanda ake rubuta tarihin rayuwar sa ɗin ko kuma ya na so ya ɓoye wani abu da zai iya zama abin kunya ko kuma ya yi niyyar hana wasu mutane samun yabo kan nasarar da ya samu.”
A ƙarshe ya ce, “Yawancin tarihin Kannywood ƙarya ne kawai wasu da ake kira furofesoshi da masu son kai, marubuta masu nuna ɓangaranci, marasa ƙwarewa, waɗanda ba su damu da su ƙosar da jama’a da ƙarya a yayin da su ka hakimce cikin ofisoshin su ba.”