HAJARA Idris, wadda aka fi sani da Hajjo a Kannywood, sabuwar mawaƙiya ce kuma jaruma. Ba ta jima da bayyana a masana’antar ba, to amma tun ta na ƙanƙabuwa ta ke waƙa.
Hajjo dai ‘ya ce ga fitaccen mawaƙin asharallen nan da aka yi a Kaduna, marigayi Idi Moris, hasali ma dai ita ce babbar ‘yar sa.
Hajara yarinya ce son kowa ƙin wanda ya rasa domin akwai ta da diri da kyan fuska. Haka kuma ba ta da girman kai, ba ta da ƙin mutane, sannan ga ta da fara’a da haba-haba da mutane.
Mujallar Fim ta zanta da wannan ‘yar gado ɗin domin jin yadda ta shiga harkar waƙa da ra’ayoyin ta kan abubuwan da su ka jiɓinci sana’ar da kuma burin ta a nan gaba. Jarumar ta amsa tambayoyin da aka yi mata kamar haka:
FIM: Ki faɗa wa masu karatu tarihin ki a taƙaice.
HAJJO: Ni suna na Hajara Idris, wato Hajara Idi Moris, wadda aka fi sani da Hajjo. Ni haifaffiyar Tudun Wada ce. An haife ni a shekarar 1992. Na yi firamare na a Abubakar Mahmud Gumi a Tudun Wada, sannan na yi sakandare na a Shehu Abdullahi Gwandu. Na fara waƙa tun ina ƙanƙanuwa.

FIM: Me ya ja hankalin ki har ki ka fara waƙa?
HAJJO: Gaskiya ni ba zan iya cewa waƙa ba ta yi min rana ba, domin kuwa tun ina ƙarama na ci arzikin waƙa. Mahaifi na mawaƙi ne, amma na gargajiya. A garin Kaduna da kewaye ko ƙaramin yaro ka faɗa wa sunan mahaifi na zai ce maka ya san shi; ko bai taɓa ganin sa ba, zai san sunan sa.
To, dalilin haka, ka san an ce wani ka na iya gado, wani kuma haye ya ke yi. Sanadiyyar haka zan iya haɗa abu a makaranta ina buga tebur, ni ce mawaƙiyar su. Wannan shi ya ja ra’ayi na na fara son waƙa.
FIM: Kenan gadon waƙa ki ka yi?
HAJJO: Sosai kuwa, gadon waƙa na yi, kuma ina alfahari da haka.
FIM: Ki na yin waƙoƙin gargajiya irin na mahaifin ki ko kuma na zamani kawai ki ke yi?
HAJJO: E, ina iya yin waƙoƙin gargajiya da mahaifi na ke yi, amma da ya ke ni mace ce, kuma an san cewa wancan na gargajiya ne maza kawai ke yi, ban taɓa ganin mace ta na yin irin wannan waƙar ba, shi ya sa ni ma ban mai da hankali ina yi ba, sai na maida hankali na a kan na situdiyo.
FIM: Wane lokaci ne ki ka fara waƙa?
HAJJO: Gaskiya na fara waƙa ban wuce shekara goma sha biyar ba a lokacin. Saboda ba zan taɓa mantawa ba, Allah ya jiƙan mahaifi na, a lokacin ya na nuna min kada in yi waƙa saboda ni mace ce ƙarama, in bari sai na mallaki hankalin kai na, kada in zo in samu wani abin duniya ya sa ba zan yi sha’awar aure ba ko kuma ba zan iya kyautata wa iyaye na ba ko in yi masu biyayya ba.
A lokacin ina ɗan yi a ɓoye. In na dawo gida aka tambaye ni daga ina ki ke, sai na ce daga sitidiyo na ke, sai a yi min faɗa da cewa in kiyaye duk abin da zan yi in yi tsakani da Allah. Ina jin daɗin addu’ar da mahaifi na ya ke yi min. Ka ga wasu iyayen su na matsa wa ‘ya’yan su, kuma wannan matsawar ba shi zai sa su ji tsoron su ba, nasiha shi ne mafita. Ni mahaifi na ya yi min nasiha sosai, a ko da yaushe maganar sa in ji tsoron Allah. “Ni ba na ganin ki, amma Allah na ganin ki a duk inda ki ke.” Wannan nasihar na yi min tasiri sosai a cikin zuciya ta. To, tun a lokacin na fara waƙa, kuma na fara waƙa ne sanadiyyar soyayya.
FIM: Ko za ki iya faɗa mana wasu daga cikin waƙoƙin ki?
HAJJO: Akwai waƙar ‘Share Hawaye’, ‘Masoyi Na’, akwai kuma wata waƙa da na yi mai suna ‘Ɗangata’, da sauran su.
FIM: Idan mu ka koma ɓangaren fim kuma fa. Ki na fitowa a fim?
HAJJO: Alhamdu lillahi. Ka san an ce da wani sanadin ka ke samun wani. Yanayin rayuwa da kuma zama da kowa lafiya, ta dalilin wani da ka ke ganin mutuncin sa, zai sa ka yi wani abin da ba ka yi tsammani ba. Da farko na fara fitowa ne a waƙoƙi, idan mutum zai yi bidiyon waƙar sa, sai ya kira ni mu yi tare. So, daga haka sai abin ya ja ra’ayi na in fara fitowa a fim, saboda hakan ya na da muhimmanci a wuri na, don na san abu mai kyau ne, sai dai in kai ka ke so ka ɓata harkar ka.

FIM: Zuwa yanzu kin fito a finafinai kamar nawa?
HAJJO: Gaskiya ba su da yawa, don ba su wuce uku zuwa huɗu ba. A cikin su akwai ‘Kaico Na’, akwai ‘Sanadi’, na manta sauran gaskiya.
FIM: Ki na da ubangida?
HAJJO: E to, ba zan iya cewa kai-tsaye ga wane shi ne ubangida na ba, amma dai na san an tallafa min sosai gaskiya, an kuma taimake ni da kuma ba ni shawarwari idan na yi abin da ba daidai ba.
FIM: Ki na da kamfani naki na kan ki ne ko kuma ki na da wani kamfani da ki ke zama a ƙarƙashin sa?
HAJJO: Ni ba ni da kamfani na kai na, amma ina zama a kamfanin ‘Wassh Production’. Ina ƙarƙashin wannan kamfani, kuma da shi na dogara.
FIM: Ya mu’amalar ki ta ke da sauran ‘yan matan?
HAJJO: Ka san ana cewa duk wanda ya zauna lafiya a rayuwa shi ya so, kuma zama lafiya ya fi zama ɗan sarki. Ina da kyakkyawar alaƙa da su, saboda ina ɗaukar kowa a matsayin ɗan’uwa na, kuma in na yi abin da ba daidai ba ina so a gyara min, haka ni ma idan na ga ka yi ba daidai ba, in ina da dama zan kira ka ni da kai in faɗa maka ka yi ba daidai ba. Amma kuma in na gama zan ba ka haƙuri in na yi ba daidai ba.
FIM: Wane fitaccen jarumi ki ke so ki ga kin yi aiki da shi?
HAJJO: Ba ni da wani jarumi da na ke so in yi aiki da shi, ni duk ɗaya na ɗauke su. Ko wane jarumi da ka gani Allah ne ya ɗaga shi. Duk wanda Allah ya haɗa ni da shi ina maraba da zuwan sa.
FIM: A ɓangaren mawaƙa kuma fa, kin taɓa waƙa da wani fitaccen mawaƙi?
HAJJO: E to, wanda na ke yin waƙa da shi ya fita, amma ka san halin rayuwa. Da Ɗayyabu D.Y. na ke waƙa, domin a situdiyon sa na ke waƙoƙi na.
FIM: Menene burin ki a kan wannan harka?
HAJJO: Buri na shi ne Allah ya sa min albarka a cikin kasuwanci na da sana’a ta, domin ni sana’a ta ina alfahari da ita. Sannan ina roƙon Allah ya sa alkahairin da ban samu ba a baya in samu a gaba. Kuma ina so in zama wata da ma sauran abokan sana’a ta baki ɗaya in-sha Allah.
FIM: Kin taɓa aure?
HAJJO: Na taɓa aure.
FIM: Yanzu ga ki a cikin wannan masana’anta, kuma ki na son ki ɗaukaka a masana’antar. Idan miji ya zo a yanzu za ki bar harkar ki yi aure?
HAJJO: Ai ɗaukakar Allah ta fi ta kowa. Mu duk abin aka ce Allah da Manzon sa, magana ta ƙare. Ai Allah ne ya ce a yi aure, kuma za mu yi aure. Ɗaukakar Allah ya fi komai, in na samu ɗaukaka zan samu kuɗi kuma in yi suna a duniya, in yi suna a duniya in kasa yin suna a lahira, wane ka ga ya fiye min? Suna a lahira shi na ke nema. Idan Allah ya sa na samu miji, kuma ina da shi a hannu na zan zauna da zuciya ɗaya babu tunanin wani abu.
FIM: Bayan rasuwar mahaifin ku, akwai wanda ya gaje shi a cikin ku?
HAJJO: Alhamdu lillahi, ƙane na ya fara yi, amma bai fiya yin na gargajiya irin na mahaifin mu ba. Akwai wanda ya ke tare da shi, Surajo Sanfal, kuma wannan soyayya ta faro ne tun ya na yaro mahaifin mu ya ke son shi. Bayan rasuwar mahaifin mu akwai ɗan abin da ya faru wanda bai yi min daɗi ba, don a lokacin na yi fushi sosai, na yi kuka har na ke cewa me ya sa ni ba zan iya yin abin ba, sai kuma na duba cewa ni mace ce, sannan wata rana zan je gidan wani. Amma dai ƙane na ya na yi, sai dai bai cika yin wanda baban mu ya ke yi ba, ya fi yin na fiyano. Amma in aka kira shi irin wancan ɗin ma ya na yi, kuma salon mahaifi na ya ɗauka tsaf.
FIM: Amma kuma idan ki ka duba akwai irin su Barmani Choge, Uwani Zakirai da sauran su, mata ne, kuma duk sun yi irin wannan harka, kuma sun yi suna a duniya. Ba ki ganin cewa idan ki ka ɗauki salon mahaifin ki za a ga cewa kin ɗauko sabon salo da ba a saba gani ba a wannan zamani?
HAJJO: Gaskiya haka ne, ina yawan tunanin haka. Amma ni na fi so in yi aure ne, don mahaifi na ya rasu da burin haka.

FIM: A ƙarshe, wace shawara za ki ba abokan sana’ar ki?
HAJJO: Shawara ta guda ɗaya ce: duk inda babba ya ke, ya ja ƙarami a jiki. Akwai abubuwan da ke faruwa da mu mawaƙa, idan Allah ya ba ka dama ka tashi, idan ƙarami ya zo sai a riƙa nuna bai isa ba. Alhali baiwar da Allah ya ba babban, shi ƙaramin ya na da shi. Kuma mutane da yawa akwai abin da ke faruwa ba ma ga mu mawaƙa ba kawai, a lokacin da mutum ya ke tashe za ka ga an fi son waƙar sa, ka ga wannan na Allah ne. Ya kamata a ce duk lokacin da mutum ya yi waƙa in da gyara a ciki wani babban mawaƙin zai iya kiran sa ya gyara masa, ba laifi ba ne. Sannan mutane ya kamata su amshi waƙar, saboda su ne jagora, su za su fidda ta duniya ta san ta. Don haka ina roƙon na saman mu su riƙa ɗora mu a kan daidai.