• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Nijeriya da Nijar: Ala da Fati Nijar sun shirya kalankuwar waƙoƙi a Kano

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
August 25, 2023
in Labarai
0
Aminu Ala da Fati Nijar su na rera waƙoƙi a taron

Aminu Ala da Fati Nijar su na rera waƙoƙi a taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SAKAMAKON cacar bakin da ake yi tsakanin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar, wanda ya sa su ke zaman doya da man ja, fitattun mawaƙa Aminu Ladan Abubakar Ala da Fati Nijar sun jagoranci wata kalankuwa da baje-kolin waƙoƙin da su ka shafi ƙasashen biyu masu alaƙar zumunci da ‘yan’uwantaka.

Sanin kowa ne cewa sakamakon juyin mulkin da sojojin Nijar su ka yi wa Firaminista Mohammed Bazoum, Nijeriya ta yanke hulɗar diflomasiyya da Nijar kuma ta ƙaƙaba mata takunkumin tattalin arziki, a bisa wani mataki da ƙungiyar ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) ta ɗauka.

Matakan sun haifar da rashin jituwa tsakanin mutanen Nijeriya da Nijar har ana zancen yaƙi da juna.

An yi taron na su Ala ne a ranar Asabar, 16 ga Agusta, 2023 a harabar gidan Rediyon Premier FM da ke titin filin sukuwar dawaki a Kano, kuma ya samu halartar mawaƙa da  malamai da masu sarauta da sauran jama’a.

Tun da farko da ya ke jawabi  a game da alaƙar ƙasashen biyu, shugaban Majalisar Malamai ta Arewa da kuma ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya bayyana ƙasashen biyu a matsayin wani yanki da ke da alaƙar da ba za su rabu ba duk kuwa da cewa Turawa sun raba su. 

Bashir Ɗandago (a hagu) da Adam M. Kirfi

Ya ce ta fuskar mu’amalar ciniki da auratayya kuma har yanzu mutane na ci gaba a matsayin mu na ‘yan’uwan da  halitta ta haɗa mu, addini ya haɗa mu, yadda ya haɗa mu da sauran abubuwa tsawon tarihi, don haka waɗannan abubuwa da su ke tasowa ba za su yi tasiri ga alaƙar mu ba a matsayin mu na ‘yan’uwa. 

Malamin ya yi kira da a fahimci wannan abin da ilimi da kuma basira don kada mu bar abin da zai lalata wannan kyakkyawar alaƙar ga yara masu tasowa.

Sheikh Ibrahim Khalil

Mujallar Fim ta ruwaito cewa a taron an fi mayar da hankali ga waƙoƙin da su ka shafi alaƙar ƙasashen biyu, inda mawaƙa irin su Ala, Fati Nijar, Bashir Ɗandago, Miftahu Umar, da Adam M. Kirfi kowa ya gabatar da waƙoƙin sa.

An yi taron an gama lafiya, kuma mahalarta  sun nuna farin cikin su da shirya shi da aka yi.

Aminu Ala a gaban taron jama’a da su ka halarci kalankuwar
Fati Nijar da ‘yar amshin ta
Aminu Ala da ‘yan amshin sa

Loading

Previous Post

Shekarar mu 20 da Zulaihat, mun zama mutu-ka-raba – Lilisco

Next Post

Gidan Dabino zai aurar da ‘yar sa Fatima ranar Asabar mai zuwa

Related Posts

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
Next Post
Amarya Fatima Ado Ahmad Gidan Dabino

Gidan Dabino zai aurar da 'yar sa Fatima ranar Asabar mai zuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!