• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, July 20, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Nijeriya za ta fara aiwatar da yarjejeniyoyin haɗin gwiwa da kafofin watsa labarai na Chana – Ministan Yaɗa Labarai

by WAKILIN MU
March 6, 2025
in Nijeriya
0
Nijeriya za ta fara aiwatar da yarjejeniyoyin haɗin gwiwa da kafofin watsa labarai na Chana – Ministan Yaɗa Labarai

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya tabbatar da hakan yayin da ya karɓi Jakaden Chana a Nijeriya, Mista Yu Dunhai, a lokacin ziyarar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GWAMNATIN Nijeriya za ta fara aiwatar da yarjejeniyoyin fahimtar juna guda biyu da aka rattaba wa hannu tsakanin Hukumar Watsa Labarai ta ƙasar Chana (China Media Group) da Hukumar Talabijin ta Nijeriya (NTA) da Hukumar Rediyon Tarayyar Nijeriya (FRCN) a Taron Haɗin Gwiwa tsakanin Chana da Afrika (FOCAC) wanda aka gudanar a birnin Beijing.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya tabbatar da hakan yayin da ya karɓi Jakaden Chana a Nijeriya, Mista Yu Dunhai, a wata ziyarar ban-girma da ya kai masa a ofishin sa ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa yarjejeniyoyin za su ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ta fuskar kafofin watsa labarai da sadarwa.

Ya ce: “Nijeriya da Chana sun kai matakin haɗin gwiwa mafi girma a tarihin dangantakar su. Wannan ne ya sa aka rattaba hannu kan yarjejeniyoyi guda goma a taron FOCAC, kuma guda biyu daga cikin su suna da alaƙa da ma’aikatar nan.

“NTA ita ce babbar tashar talbijin a Afrika baki ɗaya, tana da tashoshi sama da ɗari a faɗin ƙasar nan, tana isar da shirye-shiryen ta ga sama da mutane miliyan 200.

“Hakan ya sa muke da buƙatar amfani da wannan haɗin gwiwa don musayar bayanai da fasaha, tare da amfana da juna.”

Ministan ya bayyana cewa yarjejeniyoyin sun haɗa da musayar bayanai, shirye-shirye, da fasaha domin inganta ayyukan gidajen watsa labarai na Nijeriya tare da ƙarfafa aikin jarida bisa kyawawan ƙa’idojin duniya.

Haka nan, ya jaddada buƙatar haɗin gwiwa da Chana domin yaƙi da labaran ƙarya da yaudara ta hanyar yaɗa bayanai marasa tushe.

Ya ce: “Labaran ƙarya da yaudara manyan barazana ne ga duniya. Mun san cewa ƙasar Chana tana da matuƙar damuwa game da wannan batu, haka nan kuma Nijeriya.

“Wannan ba matsala ce da ta shafi ƙasashen mu biyu kawai ba, matsala ce ta duniya baki ɗaya. Saboda haka, muna son yin aiki tare da ƙasar Chana domin yaƙi da labaran bogi da yaɗa ingantattun bayanai da za su amfani al’umma.”

Idris ya tabbatar wa jakaden na Chana cewa Nijeriya na kiyaye ‘yancin ‘yan jarida, wanda wani muhimmin ɓangare ne na jajircewar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya.

Ya ce: “A Nijeriya, ‘yan jarida suna da ‘yancin aikin su. Duk da yake akwai matsaloli a wasu lokuta, muna aiki a kai a kai domin gyara su. Nijeriya tana da ‘yancin watsa labarai mai yawa, kuma muna son ci gaba da hakan.”

Har ila yau, ya buƙaci kamfanonin ƙasar Chana da su yi amfani da damar da manufofin Tinubu ke samarwa wajen zuba jari a Nijeriya.

A nasa jawabin, Jakada Yu Dunhai ya jaddada aniyar sa ta ƙara ƙarfafa alaƙa tsakanin Nijeriya da Chana, tare da yaba wa Ajandar Sabunta Fata ta Shugaba Ƙasa Tinubu.

Ya ce: “Ina da sa’a sosai kasancewa jakada a lokacin da Shugaban Ƙasa Tinubu yake aiwatar da Ajandar Sabunta Fata don ƙarfafa Nijeriya. Haka nan, a ƙasar Chana, Shugaba Xi Jinping yana jagorantar ƙasar zuwa cigaba ta hanyar sauye-sauyen zamani na ƙasar Chana.”

Jakaden ya bayyana cewa a taron FOCAC da ya gabata a Beijing, Shugabannin Nijeriya da Chana sun amince da ɗaukaka alaƙar ƙasashen zuwa matakin haɗin gwiwar dabarun cigaba.

Haka nan, ya nuna muhimmancin aiwatar da yarjejeniyoyin tsakanin NTA, FRCN, da China Media Group, yana mai cewa kafofin watsa labarai suna taka muhimmiyar rawa wajen gina al’umma.

Ya kuma yaba da yadda kafofin watsa labarai na Nijeriya ke gudanar da ayyukan su bisa gaskiya, daidaito, da riƙon amana.

A ɓangaren zuba jari, jakaden ya bayyana cewa Shugaba Xi Jinping ya ware dala biliyan 50 ($50bn) domin zuba jari a Afrika cikin shekaru uku masu zuwa a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyoyin da aka cimma a taron FOCAC.

Loading

Tags: Alhaji Mohammed IdrisJakaden ChanayarjejeniyaYu Dunhai
Previous Post

Kasafin kuɗin 2025 taswira ce ta ƙarfafa tattalin arziki da cigaban ƙasa – Minista Idris

Next Post

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

Related Posts

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano
Nijeriya

Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano

July 8, 2025
Next Post
Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!