MINISTAN Sadarwa Da Tattalin Arziƙi na Fasahar Zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, ya amince da naɗin jarumin Kannywood, Nuhu Abdullahi, a matsayin jakaden Hukumar Shaidar Ɗan Ƙasa ta Tarayya, wato a turance, ‘Ambassador for National Identity Management Commision’.
Takardar naɗin, mai ɗauke da kwanan wata 14 ga Satumba, 2022, ta na ɗauke da sa hannun Darakta-Janar kuma babban shugaban gudanarwa na hukumar ta NIMC, Injiniya Aliyu A. Aziz.
Hukumar ta ce an naɗa Nuhu ne domin ya taimaka wajen inganta wayar da kan jama’a dangane da haƙƙin su, ayyuka da damar su a tattalin arzikin ƙasa.
Ta ce wannan wata dama ce da za ta nuna ayyukan gwamnati ƙarara dangane da NIMC.

Jakadancin da aka naɗa jarumin na shekara ɗaya ne, daga 2022 zuwa 2023, kuma ya fara aiki ne a ranar 16 ga Satumba, 2022, sannan zai ƙare a ranar 15 ga Satumba, 2023.
Za a iya sabunta naɗin, amma sai an ga irin ƙwazon da ya yi a aikin.
A sharuɗɗan naɗin, hukumar ta NIMC za ta iya gayyatar sa lokaci-lokaci domin ya shiga gangamin faɗakarwa dangane da aikin katin shaidar ɗan ƙasa da kuma harkoki masu kama da hakan da sauran su na hukumar.
Wannan kaɗan ne daga cikin bayanan da ke ƙunshe a cikin takardar naɗin da aka miƙa wa Nuhu Abdullahi.