RAHAMA Sadau ta bayyana cewa ba za ta daina fitowa a ba fim idan ta yi aure.
Jarumar ta Kannywoodta bayyana haka ne a lokacin tattaunawar da ta yi da masu bin ta a kafar sada zumunta ta Twitter a zaren saƙo da ta ƙirƙira mai taken #AskRahama.
A zaren saƙon, wani ya tambaye ta idan za ta iya barin yin fim saboda aure, ita kuma ta amsa da tambaya cewa, “Saboda me zan daina fim don na yi aure?” Ta kuma ƙara da cewa: “Shin yin fim ba sana’a ba ce?”
Sanin kowa ne cewa ɗabi’ar matan Kannywood ce idan sun yi aure ba sa ci gaba da yin harkar fim.
Rahama ta yi mamakin yadda mata su ke taka rawa a wasu fannoni na ayyuka amma sai a yi ta kyarar matan da ke shirin finafinai.
Ta ce, “Me ya sa ba a ganin matsala idan mace ta na yin wata sana’a ko aiki a wata ma’aikata, amma ban da harkar fim?”
Jarumar ta bada misali da mata masu yin aikin jarida.
Bugu da ƙari, ta ce wane dalili ne ya sa ake samun matan aure a wasu masana’antu da dama, amma ba a son hakan a masana’artar fim?