ƊAYA daga cikin jaruman shirin ‘Daɗin Kowa’ na tashar Arewa24, Raliya, wadda sunan ta na zahiri Amina Lawan, ita ma ta yi sallama da harkar fim, domin kuwa a jiya Asabar, 23 ga Yuli, 2022 aka ɗaura mata aure.
An ɗaura auren jarumar da sahibin ta Habibu Abdullahi a masallacin Juma’a na Tsohuwar BUK da ke Kano.

Tun a ranar Juma’a aka yi taron shagalin bikin, inda abokan sana’ar ta, wato jaruman shirin ‘Daɗin Kowa’, da dama su ka halarta.
Mujallar Fim na yi wa ma’auratan fatan Allah ya bada zaman lafiya da ƙaruwar arziki.