• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ranar 31 ga Oktoba za a yi zaɓuɓɓukan cike gurabe, inji INEC

by DAGA WAKILIN MU
August 12, 2020
in Nijeriya
0
Zaɓen Edo: INEC za ta yi amfani da rajistar 2019, inji kwamishina
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa a ranar 31 ga Oktoba, 2020 ne za a yi zaɓuɓɓukan cike gurbi na mazaɓu guda 12 waɗanda su ka rage a dukkan faɗin Nijeriya.
 
Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa wadda Babban Kwamishina kuma  shugaban kwamitin wayar da kan masu zaɓe na hukumar, Mista Festus Okoye, ya bayar a Abuja ranar Talata.
 
Mista Okoye ya ce in ba domin annobar korona (Covid-19) da ake fama da ita ba, to da tun tuni hukumar ta aiwatar da zaɓuɓɓukan.
 
Ya ce: “Tun daga lokacin, hukumar ta fito da sabon tsari domin gudanar da zaɓe a cikin yanayin annobar korona.
 
“Haka kuma ta sake yi wa ƙa’idoji da dokokin ta kwaskwarima tare da haɗa gwiwa da hukumomin kiwon lafiya da sauran masu ruwa da tsaki don tabbatar da cewa an yi zaɓe cikin kare lafiya da tabbatar da adalci.
 
“Bayan haka, hukumar ta samu nasarar gudanar da zaɓe don cike gurbi a Mazaɓar Tsakiya ta Jihar Nasarawa, sannan za ta ci gaba ta gudanar da zaɓuɓɓuka na gwamnoni a jihohin Edo da Ogun a ranakun 19 ga Satumba da 10 ga Oktoba.”
 
Zaɓuɓɓukan cike gurbin da su ka rage su ne na Yankin Tsakiya na Mazaɓar Sanata a Jihar Bayelsa; Mazaɓar Yamma ta Sanata a Bayelsa; Mazaɓun Nganzai da Bayo a Jihar Borno; Mazaɓar Arewa ta Sanata a Jihar Kuros Riba; da Mazaɓar Obudu a Kuros Riba.
 
Sauran su ne Mazaɓar Arewa ta Sanata a Jihar Imo; Mazaɓar Gabas ta Sanata a Jihar Legas; Mazaɓar Kosofe II a Jihar Legas; Mazaɓar Kudu ta Sanata a Jihar Filato; Mazaɓar Bakura a Jihar Zamfara, da Mazaɓar Ibaji a Jihar Kogi.
 
Okoye ya ce an yanke shawarar hakan ne bayan an gama duba tsare-tsaren da aka yi don gudanar da zaɓuɓɓukan gwamnoni a jihohin Edo da Ondo da kuma sauran zaɓuɓɓukan cike gurabu.
 
Kwamishinan ya ƙara da cewa za a yi zaɓuɓɓukan cike gurabun na majalisun tarayya da na jihohi ne a dalilin aje aiki ko mutuwa na membobin majalisun a jihohin takwas da abin ya shafa.
 
Ya ce: “Bisa ga daidaitaccen jadawalin lokuta da ke akwai, hukumar za ta bada sanarwar zaɓen a ranar 17 ga Agusta a yayin da kuma  jam’iyyun siyasa za su gudanar da zaɓuɓɓukan share fagen su don fitar da ‘yan takara a tsakanin ranar 24 ga Agusta da ranar 8 ga Satumba.
 
“Za a fara miƙa fom-fom da sauran takardun ‘yan takara a ranar 9 ga Satumba sannan a rufe da ƙarfe 6 na yamma a ranar 13 ga Satumba.”
 
Okoye ya ƙara da cewa har an ɗora jadawalin lokutan zaɓen da ayyukan da za a gudanar na zaɓuɓɓukan cike gurbin a gidan yanar hukumar zaɓen da kuma kafofin soshiyal midiya.
 
Ya ƙara da cewa an kuma ja hankalin hukumar zaɓe ga samuwar guraben da za a cike a Mazaɓar Isi-Uzo ta Jihar Enugu da Mazaɓar Bakori a Jihar Katsina.
 
To amma, a cewar sa, Kakakin majalisar kowacce daga cikin waɗannan jihohin bai bayyana wa duniya samuwar waɗannan guraben ba tukuna.
 
Ya roƙi waɗanda abin ya shafa, musamman jam’iyyun siyasa, da su kula da jadawalin lokutan zaɓuɓɓukan kuma su yi aiki sosai da shi.

Loading

Previous Post

Matasa miliyan 5 sun yi rajistar shiga shirin N-Power kashi na 3

Next Post

Gwamnati za ta kafa Cibiyar Dattawa ta Ƙasa

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post

Gwamnati za ta kafa Cibiyar Dattawa ta Ƙasa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!