• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ranar Iyalai ta Duniya: Ma’aikatar Jinƙai za ta agaza wa iyalai mabuƙata 30

by DAGA ALI KANO
May 17, 2022
in Nijeriya
0
Hajiya Sadiya Umar Farouq

Hajiya Sadiya Umar Farouq

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAR Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa ma’aikatar ta za ta kai wa aƙalla iyalai 30 da ke cikin ƙuncin rayuwa ɗauki.

Ta bayyana haka ne a ranar Litinin domin bikin Ranar Iyalai ta Duniya (International Day of Families) ta 2022, a cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktar Yaɗa Labarai ta ma’aikatar ta bayar, wato Madam Rhoda Ishaku Iliya.

Ministar ta ce babban burin ma’aikatar shi ne ta inganta yanayin rayuwar iyalai, da masu fama da fatara da rashin galihu a cikin al’umma.

Hajiya Sadiya ta ce: “Inganta rayuwar iyalai talatin ɗin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da wannan ma’aikatar ke yi wajen kyautata rayuwar iyalai a ƙasar nan saboda  Ranar Iyalai ta Duniya.

“Wasu daga cikin nasarorin da ma’aikatar ta samu ta fuskar kyautata rayuwar iyalai sun haɗa da bincikowa tare da sake haɗa fuskokin iyalan da su ka daɗe ba su ga juna ba, ƙarfafa rayuwar iyalai, sulhunta ma’auratan da su ka samu saɓani, saisaita iyalan da ke zuwa aiki, da samar da rancen kuɗi domin yin sana’a.”

Ministar ta yi nuni da cewa Majalisar Ɗinkin Duniya, a cikin Ƙudirin ta mai lamba 47/237 wanda ya fara aiki daga shekarar 1993, ita ce ta ware ranar 15 ga Mayu na kowace shekara a faɗin duniya domin membobin majalisar su yi bikin Ranar Iyalai ta Duniya.

Ta yi bayanin cewa manufar Ranar Iyalai ta Duniya ita ce ta samar da wayar da kan jama’a da ƙara masaniya kan yadda tsarin zamantakewa da tattalin arziki ke shafar iyalai a ko’ina a duniya.

A cewar ta, kula da wannan ranar za ta ƙara wayar da kan jama’a dangane da al’amuran da su ka shafi iyali a matsayin su na cibiyar farko kuma ginshiƙin gina al’umma.

Ta ƙara da cewa ware ranar ya kuma nuna muhimmancin da ƙasashe su ka ɗora kan iyalai da halin da su ke ciki a duniya.

Yayin da ta ke nanata jigon Ranar Iyalai ta Duniya ta 2022, wato “Iyalai da Tsarin Zaman Birni” (“Families and Urbanisation”), ministar ta ce jigon zai ƙara wayar da kan al’umma kan muhimmancin inganta rayuwar iyali – wajen kyawawan tsare-tsaren zaman birni.

Ta ce: “Tsara zaman birni ya na daga cikin manyan ayyukan da su ka shafi duniyar mu da kyautatuwar rayuwar iyalai a faɗin duniya.

“Inganta zaman birni ya na da alaƙa da nasarorin da ake samu a ɗaya daga cikin Ƙudirorin Inganta Cigaban Rayuwa, wato ‘Sustainable Development Goals’ (SDG) da manufofi irin su SDG 1 (rage fatara), SDG 3 (kyakkyawan kiwon lafiya da jin daɗin rayuwa); SDG 11 (kyautata zaman mutane a birane ta fuskar zaman tare, zaman lafiya, juriya da ɗorewa), da SDG 10 (rage fifiko a zaman jama’a a tsakani da kuma cikin ƙasashe). 

“Dukkan waɗannan manufofi da aka lissafa sun dogara ne kan irin yadda aka gudanar da tsare-tsaren zaman birni domin amfanar iyalai da inganta zamantakewar mutane masu bambancin shekaru da ke zaune a cikin birane.”

Hajiya Sadiya ta yi kira ga kowane ɗan Nijeriya da ya sadaukar da bikin Ranar Iyalai ta Duniya ta bana ga neman maganin matsalolin da su ka shafi ɗorewar iyalan Nijeriya tare da cigaban su.

Ta ce: “Ina kira ga dukkan iyalan Nijeriya da su tashi tsaye wajen sa ido sosai tare da yin addu’o’i domin kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ƙasar mu ke fuskanta a yau da yadda su ka tarwatsa al’ummomi.”

Ministar ta yaba da irin damuwa da kuma goyon bayan da ƙungiyoyi masu zaman kan su da hukumomi na duniya da sauran masu ruwa da tsaki su ke bayarwa wajen kula da Ranar Iyalai ta Duniya.

Ta yi kira ga jihohi da ƙananan hukumomi da kuma ƙungiyoyi masu zaman kan su da su yi amfani da ƙarfin ikon su tare da fito da wasu shirye-shirye wajen yin bikin wannan ranar.

Haka kuma ta yi kira ga iyalai da su riƙa sa ido kan abubuwan da ‘ya’yan su ke aikatawa don tsare su daga faɗawa cikin tarkon masu amfani da yara da matasa wajen aikata laifuffuka a cikin al’umma.

Loading

Tags: Internation Day of Families 2022Majalisar Ɗinkin DuniyaMinistry of Humanitarian AffairsRanar Iyalai ta DuniyaRhoda Ishaku IliyaSadiya Umar FarouqSDGsUN General Assemblyurbanisationzaman birni
Previous Post

Ko abin da ya faru ga Maijidda Ibrahim zai zama izina ga ‘yan fim?

Next Post

Fashewar gas a Kano: Ministar Jinƙai na so a ɗau matakan hana aukuwar bala’o’i

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
'Yan kallo a bakin ginin da ya ruguje (Hoto daga: NEMA)

Fashewar gas a Kano: Ministar Jinƙai na so a ɗau matakan hana aukuwar bala'o'i

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!