BARI in yi da Hausa saboda kowa ya samu. A gaskiya wannan industiri tamu ta Kannywood sai a hankali! Duk abin da mutum zai aikata, komai kyawun sa da alherin abin sai dole an samu masu gutsiru-tsoma.
A tarihin Kannywood, tun daga lokacin waɗanda su ka kafa ta irin su Iyan-Tama, Auwal Sarauniya, Dan’azimi Baba da sauran su, kawo ya zuwa yau, ba a taɓa samun mutum wanda ya ke ɗibar tsabar dukiyar sa, gumin sa da ya nema wa kan sa ya ke rarraba wa jama’ar masana’antar kamar Dauda Kahutu Rarara ba. A irin wannan lokaci da ake cikin matsalar ƙuncin rayuwa da tsabar talauci, ya bai wa mutane da dama kyautar motoci kala-kala. Ban da sunayen jama’a ‘yan fim na da da na yanzu da ake jerowa ake raba musu kuɗaɗe daga dubu ɗari-ɗari, hamsin ko talatin wanda ta hakan ya ke kashe miliyoyin kuɗaɗe. Ya na yi ne fisabilillah a dukiyar sa, a aljihun sa, ba tare da neman komai a wajen waɗanda ya bai wa ba. Yi kawai ya ke don Allah. Ba siyasa ya ke ba bare ka ce ya na neman ƙuri’ar ka.
Irin waɗannan halaye nasa na yi magana a rubutun da na yi masa a jaridar Turanci yau fiye da wata shida baya. Amma maimakon mu yaba masa, wasu na faɗar ai riya ne abin da ya ke yi. In dai haka riya ta ke, to don Allah su ma sauran masu hali irin sa su dinga irin wannan riya in dai al’umma za su amfana!
Ba maganar riya. Hakan da ya ke zai ba wasu ƙwarin gwiwa su ma su fito su taimaka, kuma ana nuna wa duniya cewa mu na kishin junan mu.

A yanzu a industiri, ko dai ka yabi alherin irin su Rarara da Abdul Amart a cikin jama’a ko ka yi shiru. Idan zagi ko baƙa za ka faɗa a kan su, to ka ɓuya kai da abokin yin ka ku yi tare ku tashi ku bar azumin ku a wajen. Amma idan ka yi cikin mutum uku ko huɗu, wallahi sai wani ya ci mutuncin ka.
Wasu sun ce ai kuɗin waƙa ne, kuɗon banza. Tirrr! Ai wani ko tsinko kuɗin ya ke ba zai iya abin da Rarara ya ke yi ba, bare waƙa. To waƙa ai ba ƙaramin aiki ba ne. Abu ne ne na ‘creativity and talent’. Waƙa aba ce da sai an ji jiki, an ba kai wahala wajen tunani da ƙirƙira. To a harkar ‘showbiz’ (nishaɗantarwa) ba wani abu na sauƙi.
Ko ma meye, halak ɗin sa ne, dukiyar sa ce, gumin sa ne ya ke nemowa ya ke yi wa al’umma. Ban da wanda ya ke yi a ɓoye, waɗanda Allah kaɗai ya san yawan su. Fatan mu, sauran masu motsi su yi koyi da shi.
*Ahlan fitaccen jarumi ne kuma furodusa a Kannywood