SANANNEN mawaƙi, Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara), ya ba da aikin gyaran waɗansu tituna da ke yankin garin su a jihar sa ta Katsina.
Mai taimaka wa mawaƙin a ɓangaren soshiyal midiya, Rabi’u Garba Gaya, ya bayyana cewa titunan da za a gyara su ne: hanyar Tudun Wakili zuwa Sundu zuwa Ɗanja zuwa Dabai, sai hanyar Kahutu zuwa Ceɗiya, daga Ceɗiya kuma zuwa Zarewa.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa a halin yanzu aikin hanyoyin sun kankama gadan-gadan.

