FITACCEN mawaƙin siyasa, Dauda Adamu Abdullahi (Rarara), shi ma ya fito da gidan yana inda za a iya kallon finafinai da waƙoƙin Hausa, wato ‘streaming’ a turance.
Sunan gidan yanar nasa ‘Arewa Cinema’, kuma shi ne na uku irin sa da aka buɗe, wato bayan Northflix na Jamilu Abdussalam da kallo.com na Maijidda Modibbo.
Mai taimaka wa Rarara a fagen soshiyal midiya, Rabi’u Garba Gaya, ya tabvatar wa da mujallar Fim cewa lallai ubangidan nasa shi ne mamallakin manhajar ‘Arewa Cinema’, wanda hakan amsa ce ga masu tambayar wanene ya ƙirƙiro ta kimanin mako biyu tun da aka fara tallata ta a soshiyal midiya.

A yanzu haka akwai finafinai da dama a kan manhajar, irin su ‘Mariya’, ‘Hafeez’, ‘Mujadala’, ‘Wutar Kara’, ‘Ana Dara Ga Dare’, ‘Salmah’, da sauran su. Akwai kuma finafinai masu dogon zango irin su ‘Wuff’ da sauran su, sannan akwai waƙoƙi.
Mujallar Fim ta gano cewa a tsarin biyan kuɗi kafin mutum ya fara kallo a manhajar, a shekara zai biya N9,500, sannan in duk wata ne zai riƙa biyan N1,000 ne.
Wakilin mu ya gano cewa su ma masu ‘Arewa Cinema’ sayen fim su ke yi a hannun masu shiryawa kamar yadda sauran su ke yi.
Sannu a hankali dai abubuwa na ƙara faɗaɗa a Kannywood, yanzu babban ƙalubalen da ke gaban ‘yan Kannywood shi ne su ma a fara ganin finafinan su a Netflix.