• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rashida Lobbo: Aure na yi a Thailand, shi ya sa na bar Kannywood

by DAGA IRO MAMMAN
January 16, 2020
in Tattaunawa
0
Auren soyayya: Rashida Lobbo tare da Abubakar

Auren soyayya: Rashida Lobbo tare da Abubakar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

AN shafe sama da shekara ɗaya yanzu tun da aka daina ganin gilmawar jaruma Rashida Lobbo a fagen shirya finafinai na Hausa, wato Kannywood. Hatta ‘yan fim da dama ba sun dalilin hakan ba.

 Sai dai kuma ana yawan ganin hotunan ta a wata ƙasa da za a iya kira can a bangon duniya, wato Thailand. Rashida kan turo hotunan ta a Instagram daga Bangkok, babban birnin ƙasar. Hakan ya sa an yi ta tambayar me ya kai ta can, kuma me ta ke yi?

Mujallar Fim ta daɗe da sanin cewa Rashida ta yi aure, domin tun a cikin 2018 da aka yi auren ya so ta ba shi labarin auren, musamman da yake an yi shi ne kusan a asirce. Amma sai jarumar, wadda ake yi wa laƙabi da ‘Shishi Mama’, ta ce a dakata tukuna, sai nan gaba.

Kwatsam, a ranar 19 ga Disamba, 2019 sai Rashida ta tuntuɓi wakilin mu, ta ce masa ta shirya tattaunawa. Ba tare da ɓata lokaci ba kuwa su ka zanta, inda ta fayyace masa bayanai game da auren soyayya da ta yi, da yadda mijin ta ke kula da ita, da batun kaɗaici musamman yadda nisan duniya ya hana ta ganin mahaifiyar ta, da kuma uwa-uba tunanin ta game da Kannywood da masoyan ta masu kallon fim. Ga yadda hirar ta kasance: 

FIM: An samu shekara ɗaya kenan ba a ganin ki a industiri ko ma a Nijeriya baki ɗaya. Sai aka riƙa ganin hotunan ki daga Bangkok, babban birnin ƙasar Thailand. Wasu sun ce aure ki ka yi a can. Ya gaskiyar maganar ta ke? 

RASHIDA LOBBO: E, aure na yi a can.

 FIM: Ikon Allah! Ashe auren ki ka yi. To me ya sa ki ka ɓoye maganar auren har tsawon shekara ɗaya tunda abin farin ciki ne? Ba ki so a taya ki murna ne?

 RASHIDA LOBBO: Ra’ayi na ne kawai wallahi.

 FIM: Ba a yi taron ɗaura aure ba kenan? Domin ba mu ga ko da hoton taron kin ɗora a shafukan ki na soshiyal midiya ba.

 RASHIDA LOBBO: An yi, ban ɗora ba ne saboda ‘is my private life’. 

FIM: Ya sunan mijin naki, kuma shi mutumin ina ne? 

RASHIDA LOBBO: Sunan shi Abubakar, kuma ɗan Mali ne.

 FIM: Wane irin aiki ya ke yi? Sannan me ya kai ku zama a Bangkok har tsawon wannan lokaci?

 RASHIDA LOBBO: Aikin gwal ya ke yi kuma shi a can ya ke zama. Ya yi shekaru misalin 26 a can. 

FIM: Ku nawa ne matan mijin naki?

 RASHIDA LOBBO: Ni kaɗai ce.

 FIM: To yaya rayuwa ta kasance maki a Bangkok inda ba a Hausa? Ko akwai irin mutanen mu a can?

 RASHIDA LOBBO: Akwai irin mutanen mu, amma rayuwa can ba daɗi saboda zaman kai kaɗai.    

 FIM: Kewar gida ba ta riƙa damun ki a can kuwa?

 RASHIDA LOBBO: Ta na yi, sosai ma, musamman tunanin mahaifiya ta.      

 FIM: Sau nawa ki ka zo gida tun da ku ka tafi can?

 RASHIDA LOBBO: Ban zo gida ba har yanzu.

 FIM: Amma kwanan nan mun ga kin ɗora hotuna tare da nuna cewa ki na Dakar, ƙasar Senegal. Me ya kai ki Dakar?

 RASHIDA LOBBO: Aiki ya kawo ni ƙasar Senegal saboda ina aiki a Thailand. 

FIM: A yanzu ki na wane gari ne?

 RASHIDA LOBBO: Ina Bangkok.

 FIM: Ko kun samu ƙaruwa ta haihuwa a zaman auren naku?

 RASHIDA LOBBO: A’a, Allah bai kawo ba.   

FIM: Za mu so ki ba masu karatu tarihin ki a taƙaice saboda wanda bai sani ba ya sani.

 RASHIDA LOBBO: Ni dai asali na ‘yar ƙasar Kamaru ce, amma na zauna a Abuja wurin ‘yan’uwan mahaifiya ta. A nan na yi karatu na na gama har na shiga harkar fim. 

 FIM: A matsayin ki na Bafulatanar Kamaru, ya aka yi ki ka iya harshen Faransanci da kuma Ingilishi?

 RASHIDA LOBBO: Na yi Faransanci ne saboda uwa ta ta na zama a ƙasar Kamaru kuma ina zuwa hutu. Ingilishi kuma a Najeriya na yi karutu na, shi ya sa. 

Rashida Lobbo da Abubakar a birnin Bangkok

FIM: Ya aka yi ki ka shigo harkar fim?

 RASHIDA LOBBO: Ina so na zama ‘yar jarida in yi aiki a gidan TV. To  da ban samu ba shi ne na shiga harkar fim.  

 FIM: Faɗa mana sunayen finafinan da ki ka yi.

 RASHIDA LOBBO: Na yi ‘Azeema’, ‘Tenants of the House’, ‘Maigida’, da dai sauran su.

 FIM: Kafin ki bar Kannywood, mun gan ku ku na ɗaukar wani fim na ‘yan Kudu, wato Nollywood. Ya sunan fim ɗin, kuma ko ya fito kuwa?

 RASHIDA LOBBO: Sunan shi ‘Tenant of the House’. Bai fito ba, amma an yi firimiya ɗin shi.

 FIM: Yanzu dai kin bar harkar fim gaba ɗaya ko? 

RASHIDA LOBBO: E, a yanzu dai na bari gaskiya.  

FIM: Me za ki faɗa wa ‘yan’uwan ki ‘yan fim game da barin su babu ko bankwana da ki ka yi? 

RASHIDA LOBBO: Haƙuri zan ba su kuma in ce ‘I missed them all’.  

FIM: Wane saƙo gare ki ga masoyan ki masu kallon finafinan ki?

 RASHIDA LOBBO: Saƙo na shi ne su taya ni da addu’a kawai.  

 FIM: A ƙarshe, mecece fatan ki game da wannan aure da ki ka yi?

 RASHIDA LOBBO: Fata na shi ne Allah ya ba ni zaman lafiya da yara masu albarka.

 FIM: To amin Rashida. Mun gode.

Kallon soyayya: Rashida Lobbo da mijin ta Abubakar

Loading

Tags: aureazeemabangkokhausa actorsKannywoodRashida Lobboshishi mamatenants of the housethailand
Previous Post

MOPPAN: Maikano ya yi wa Sarari raddi kan sukar da ya yi masa

Next Post

Ina matan Kannywood ke samun kuɗi su na zarya a ƙasashen waje?

Related Posts

Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 
Tattaunawa

Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 

March 1, 2025
Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah
Tattaunawa

Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah

November 13, 2024
Bikin auren ‘ya’ya na ya ɗaga daraja ta – Aminu Ala
Tattaunawa

Bikin auren ‘ya’ya na ya ɗaga daraja ta – Aminu Ala

August 2, 2024
Buri na in samar wa MOPPAN tsarin shugabancin da za a riƙa tunawa da ni – Habibu Barde
Tattaunawa

Buri na in samar wa MOPPAN tsarin shugabancin da za a riƙa tunawa da ni – Habibu Barde

March 13, 2024
Mahaifiyar Afakallahu ta kwanta dama
Tattaunawa

Afakallahu: Abin da mahaifiyar mu ta karantar da mu

March 11, 2024
Gaskiyar abin da ya faru gare ni a haɗarin da na yi – Jarumar Kannywood Maryam CTV
Tattaunawa

Gaskiyar abin da ya faru gare ni a haɗarin da na yi – Jarumar Kannywood Maryam CTV

February 14, 2024
Next Post
Daga hagu: Rahama, Gabon da Washa a London

Ina matan Kannywood ke samun kuɗi su na zarya a ƙasashen waje?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!