ALLAH ya yi wa jarumin Kannywood, Malam Aminu Muhammad (AZ), rasuwa a yau Litinin, 8 ga Mayu, 2023 a asibitin Nassarawa da ke cikin birnin Kano.
Marigayi Malam Aminu, wanda ke taka rawar Kawu Mala a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ na tashar Arewa 24, ya gamu da ajalin sa ne a sakamakon matsalar ciwon zuciyar sa da ya tashi, kamar yadda matar sa da babban ɗan sa su ka bayyana.
Malam Aminu Muhammad (Mai Chemist) ya rasu ya bar mata ɗaya da ‘ya’ya 11, maza takwas da mata uku.
A cewar matar sa, Malama Amina Yusuf (Hajiya Umma), ya shafe kusan shekaru uku ya na fama da wannan matsala ta ciwon zuciya wadda cutar gyambon ciki (ulcer) ce musabbabin ta, kuma ciwon kan tashi masa a lokaci-lokaci ne, har zuwa wannan lokaci da ya sake tashi a ranar Asabar da ta gabata da dare. An garzaya da shi zuwa Asibitin Muhammadu Abdullahi Wase na Nassarawa, inda a nan ne kuma Allah ya karɓi ran shi da misalin karfe 3 na daren wayewar garin wannan rana ta Litinin.
An dai gudanar da jana’izar sa da misalin ƙarfe 8:30 na safiyar yau a gidan sa da ke unguwar Haye kan Titin Ring Road zuwa ‘Yankaba, a Kano, aka binne shi a makwancin sa na ƙarshe a maƙabartar ‘Yankaba.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa da dama daga cikin abokan aikin sa na masana’antar Kannywood ba su samu sallar jana’izar ba a dalilin ya rasu ne da tsakiyar dare, sai da gari ya waye labarin rasuwar ya ɓulla, musamman a soshiyal midiya bayan babbar ‘yar sa, Fatima Aminu Muhammad, ta wallafa Facebook sanarwar. Kuma sanarwar da ta biyo baya a kan sai ƙarfe 10:00 na safe za a yi jana’izar ta taimaka wajen rashin samun jana’izar.
Malam Aminu Muhammad AZ, wanda ‘yan unguwa musamman na Dakata su ka fi sani da Aminu Mai Chemist, kasancewar sa likita da ke bayar da magani da duba marasa lafiya, ya samu kyakkyawar shaida kan siffantuwa da kyawawan halaye da ɗabi’u nagari, wanda da wahala ka ji an ce ga abokin rigimar sa a ciki da wajen harkar fim. Maƙwaftan sa na unguwar ma duk sun tabbatar da hakan.
Wani abin al’ajabi kuma shi ne yadda ya bar rubutacciyar wasiyya kan wanda zai yi masa sallah a duk lokacin da ya bar duniya, kuma iyalan nasa su ka cika masa ita ta hanyar nemo wanda ya ayyana ɗin don sallatar sa.
Bayan jana’izar sa, tawagar abokan aikin sa na tashar Arewa 24 sun ziyarci gidan sa don yin gaisuwa ga iyalan sa. Daga cikin su akwai daraktan shirin ‘Daɗin Kowa’, wato Mujaheed Adamu Bello, da biyu daga cikin marubutan shirin, Nasir Umar (NID), Bashir Ɗan Rimi da Ɗan Bayero da darakta Kamilu Ibrahim (Ɗan Hausa), Sarah Alaysious (Stephenie) da Muhsin M. Baƙo da sauran su.
Da fatan Allah ya jiƙan shi da rahama, ya kuma ba iyalai da ‘yan’uwa haƙurin rashi, amin.