ALHAJI Umar Sa’idu Tudunwada ƙwararren ɗan jarida ne wanda ya taɓa aiki a Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) a Washington DC, kuma ya taɓa zama shugaban gidan Rediyo Freedom da ke Kano. A lokacin rasuwar sa, shi ne shugaban gidan Rediyo Kano. Ya rasu a ranar Lahadi, 30 ga Yuni, 2019 a wani haɗarin mota da ya ritsa da shi tare da matar sa Hajiya A’ishatu Sule da ‘yar sa Maryam da direban sa Malam Ado Gauta a cikin garin Kura, Jihar Kano, a kan hanyar su ta dawowa daga Abuja, amma shi kaɗai ya rasu.
Kafin rasuwar sa, ya ɗauki nauyin shirya fim mai nisan zango (‘series’) mai suna ‘Bilkisu’ a ƙarƙashin kamfanin sa na Amara.
Daraktan fim ɗin ‘Bilkisu’, Malam Balarabe Murtala Baharu, ya yi hira da mujallar Fim inda ya bayyana irin alhinin da ya shiga sakamakon rasuwar ubangidan nasa, kuma ya bayyana irin gudunmawar da marigayin ya ba Kannywood. Ga hirar:
FIM: Ka na ɗaya daga cikin manajojin kamfanin shirya finafinai na Amara, sannan kai ne daraktan fim ɗin ‘Bilkisu’, duka na marigayi Umar Sa’idu Tudunwada. Ko yaya ka samu kan ka a sakamakon jin labarin rasuwar sa?
BAHARU: To gaskiya ina ganin zan iya cewa ina ɗaya daga cikin waɗanda za a ce an yi masu rasuwar sa, saboda ya riƙe ni tamkar ɗan sa kuma ya ba ni damar da ba kowa ya same ta ba, ko da a cikin ’ya’yan sa ne. Don ya horar da ni mu’amala da mutane kuma ya nuna min tsayawa a kan gaskiya da kyautata wa mutane, kuma ya ɗauki amanar aikin da ya ke ganin al’umma za su kalla wanda zai zama ma’auni ta hanyar fim da zai canja harkar finafinan Hausa ya ba ni. Don haka wannan ta sa na ke ganin ba ni aikin ‘Bilkisu’ da ya yi na zama a matsayin mai shiryawa nashi da bada umarni wannan shi ne abin da ba zan taɓa mantawa da shi a rayuwa ta ba.
FIM: Da yake fim ɗin ‘Bilkisu’ bai riga ya fito ba, ko ina matsayin fim ɗin a yanzu?
BAHARU: To farko dai matsayin fim ɗin a yanzu ana matakin yanka hotunan da tace su, don haka an zo gaɓar ƙarshe ta kammaluwar aikin gaba ɗaya. Sai dai abin juyayi da alhini a kan wannan aikin shi ne marigayi bai taɓa zama ya kalli aikin ya ga ina aka tsaya ba. Sai dai ya kalli wani ɓangare na abin da aka ɗauko a lokeshin. Sai kuma sinasinai biyu da aka tace na ɗauka a waya na je na nuna masa, sai kiɗan bayan fage da na ɗauka ya yi masa zai saka a kwamfutar sa ya rinƙa ji. Abin da na sani kenan.
Kuma a yanzu bisa hasashe da mu ke yi, ba ma aikin ‘Bilkisu’ ba, duk wasu aikace-aikace na kamfanin Amara ba ma fatan abin zai tsaya da yardar Allah. Amma dai abu ne na magada, sai hukuncin da su ka yanke. Kuma a yanzu haka akwai mutanen da ya raina da su ke ƙoƙarin ganin wannan aiki na ‘Bilkisu’ ya kammala.
Kuma ƙarin bayanin da zan yi maka shi ne abubuwan da Umar Sa’id Tudunwada ya yi a harkar fim sai nan gaba za su ƙara fitowa, domin shi ne mutum na farko da ya ke kare masana’antar daga dukkan wani abu da zai taso mata na damuwa ba tare da ’yan fim sun sani ba. Kuma ya tsaya wajen ganin an tabbatar da zaɓen MOPPAN wanda ya gabata a Kano, kuma shi ne ya bada ofishin sa domin a rinƙa horas da ƙananan marubuta labarin fim domin su koya, kuma burin sa ya cika, domin wasu da yawa daga cikin su a yanzu su na cin gajiyar abin.
Amma abu ɗaya da zan ce ya tafi da burin tabbatuwar sa shi ne wannan fim ɗin na ‘Bilkisu’.
Ina fatan Allah Ya cika masa burin sa, kuma Allah ya jiƙan sa, ya yafe masa kurakuran sa, ya inganta zuriyar sa. Allah Ya jiƙan Umar Sa’id Tudunwada, amin.
