WANI sabon rikici ya ɓarke a shugabancin ƙungiyar ‘yan kasuwar finafinai waɗanda aka fi sani da ‘yan dawunlodin a Kano.
Mujallar Fim ta gano cewa rikicin ya biyo bayan wani yunƙurin juyin mulki da ɓangaren shugaban ƙungiyar, Auwal Badi, su ke zargin tsagin Abdulhadi Madubi da yi masu wanda hakan su ke ganin ba abu ne mai yiwuwa ba. Su kuma ɓangaren Abdulhadi Madubi su na ganin ai tuni ma sun gama kifar da shugabancin sai dai a jira sabo.
Ɓangaren Abdulhadi Madubi su na zargin shugabancin Auwal Badii da yin babakere da kuma sama da faɗi da kuɗin ƙungiyar da ake karɓa na bin layin sakin fim wanda su ka ce sun bincika ba su samu wata shaida a rubuce da ta tabbatar da yadda aka yi da kuɗin ba.
Da mujallar Fim ta tuntuɓe shi kan lamarin, Abdulhadi Madubi ya ce: “Da man ita wannan harkar tamu ce, mu mu ka fara yin ta, sai daga baya da ta kafu wasu su ka zo daga baya gwamnatin da ta gabata da ta zo ta rinƙa yin amfani da su don biyan buƙatar kan su wanda kuma an samu canjin gwamnati da ta zo da niyyar gyara don haka matasa da su ke son a yi gyara su ka ba mu haɗin kai aka rushe shugabancin.
‘Kuma an yi zama a ofishin Hukumar Tace Finafinai, abin bai yiwu ba. Sai Abba El-Mustapha ya ce mu je mu sasanta a tsakanin mu. Wannan ya sa mu ka yi zama a ranar Juma’ar nan bayan an sauko daga masallaci, amma zaman bai yiwu ba saboda sun tayar da rigima da zage-zage.
“Don haka dai a yanzu babu shugabanci, sai nan gaba idan an sama. Hakan ya sa ma a wannan satin ba a saki finafinai ba, sai nan gaba idan an daidaita tare da samar da shugabanci. Amma dai a yanzu ƙungiyar mu ba ta da shugaba.”
Sai dai da mu ka waiwayi Auwal Badi kan batun sai ya ce, “Har yanzu ina nan a matsayin shugaba, babu wanda ya rushe shugabanci na. Kawai dai wasu ne su ka zo da son zuciyar su, kuma idan ka na shugabanci dole sai ka yi haƙuri da irin wannan matsalolin.
“Don haka nan gaba kaɗan za a shawo kan su. Amma dai har yanzu shugabanci ya na nan ba a rushe ba, kuma ni ne dai a matsayin shugaba.”