MAWAƘIYA kuma jaruma a Kannywood, Amina Abdullahi, wadda aka fi sani da Ummi B.Y., ta maka fitaccen mawaƙin nan El-Mu’az Muhammad Birniwa a kotu kan zargin tsoratarwa.
Ta shigar da ƙarar ne a Babbar Kotun Majistare da ke unguwar Rigachikun, Kaduna, a ranar 29 ga Satumba, 2022, ta hanyar lauyan ta, Abdulsaleem Umar na cambar ‘M.T. Mohammed and Co. (Pinnacle Chambers)’ da ke Titin Alƙali, cikin garin Kaduna.
Sammacin ƙarar, wanda mujallar Fim ta samu kwafen sa, ya nuna cewa Ummi ta yi ƙarar El-Mu’az ne bisa babban laifin barazana (direct criminal complaint for the offence of intimidation) wanda ya saɓa wa sashe na 377 na kundin finalkod na Jihar Kaduna na shekarar 2017.
A sammacin, jarumar ta faɗa wa kotun cewa ita mazauniyar garin Birnin Yero ce, yayin da shi El-Mu’az mazaunin Unguwar Kaji ne da ke garin Kaduna, don haka kotun na da hurumin sauraren ƙarar.
Ta ce a ranar 2 ga Satumba, 2022 ta kira wanda ta ke ƙarar a waya domin su gaisa a matsayin sa na abokin hulɗar ta, amma sai kawai ya shiga surfa mata zagi tare da yi mata barazanar sai ya sa yaran sa sun kashe ta kuma babu abin da za a yi tunda ya na da iko a cikin al’umma.

Ta ƙara da cewa a cigaba da barazanar da ya yi mata, da misalin ƙarfe 9 na dare a ranar 22 ga Satumba sai ga wasu ‘yan daba ya turo mata har gida domin su ɗauke ta su tafi da ita zuwa wani waje da ba ta sani ba, amma wasu bayin Allah su ka taimaka mata su ka hana ‘yan iskar shiga gidan.
“Yanzu wadda ke ƙarar ta na fargabar fita daga gida saboda tsoron kada wanda ake ƙarar ko yaran sa su da ya ɗauka su kai mata hari ba tare da wani dalili ba,” inji lauyan ta.
Ya ce a yanzu haka El-Mu’az ya na nan ya na neman Ummin ruwa a jallo a kan tunanin cewar shi wani isasshe ne wanda ko me ya aikata ba za a iya yi masa komai ba.
Lauyan ya nuna wa kotun cewa wannan abu da ake zargin El-Mu’az da aikatawa babban laifi ne wanda ya saɓa wa sashe na 377 na kundin finalkod na Jihar Kaduna na shekarar 2017.
Idan kun tuna, mujallar Fim a makon jiya ta ba da labarin yadda rigima ta kaure a tsakanin mawaƙan biyu.
Comments 3