HUKUMAR Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta dakatar da mawaƙi kuma jarumi a Kannywood, Usman Umar (Sojaboy), da wasu jarumai mata biyu, Shamsiyya Muhammad da Hasina Suzan, daga shiga duk wasu harkoki da suka shafi Kannywood a Kano.
Hukumar ta yanke wannan hukunci ne bayan ɓullar wasu fayafayen bidiyo na sabuwar waƙar sa mai suna ‘Bugun Zuciya’ da ke yawo a soshiyal midiya, wanda ke nuna fasikanci da ya saɓa wa addini, al’ada, ƙa’idoji da ɗabi’un Kano.
Hukumar ta ce ta samu ƙorafe-ƙorafe da dama daga al’umma da kuma malaman jihar a kan wannan lamari.
A cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun jami’in yaɗa labarai na hukumar, Malam Abdullahi Sani Sulaiman, wadda ya fitar a yau Litinin, hukumar ta bayyana cewa an sha gargaɗin Sojaboy a kan abubuwan da suka shafi lalata da kuma rashin mutunci.
Babban Sakataren hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, ya umurci sashin tacewa da su tabbatar da cewa Sojaboy da jaruman mata ba su shiga cikin duk wani shiri na Kannywood ba.
Ya kuma umurci duk wuraren shirya finafinai da nishaɗi su lura.
Doka ta ba Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ikon daidaita duk wani nau’in magana, tare da tabbatar da cewa sun yi daidai da addini, al’ada, ƙa’idoji da ɗabi’un jihar.

Hukumar ta ce wannan mataki yana ɗaya daga cikin ƙoƙarin da take yi na kiyaye kyawawan halaye a masana’antar shirya finafinan.
Ta ce: “Ya kamata jama’ar gari da masana’antar shirya finafinai ta Kannywood su sani cewa hukumar mu ba za ta amince da duk wani nau’in lalata a kano ba, daga ko wanene. Kuma daga yau Sojaboy da abokan aikin sa ba sa cikin masana’antar nan.”