A gida daji da tsauni,
Ko a gona ko a hanya,
Haƙuri ke sanya bawa,
Rabo ya tarar da nasa.
Rabo bai cin amana,
Yaudara ko karuwanci,
Don bai da halin kilaki,
Akuyar wawa ta kurmi.
Rabo ya san halacci,
Kamar bawa da fata,
Ta jiki nasa ce fa tasa,
Haka nan ita ce rabon sa.
Ko da dai yai bilicin,
Fatar ta sauya launi,
Bai kwaɓe fatar jikin sa,
Ya je juji ya yada.
Lokaci tsanin hawa ne,
Kuma shi ke sanya yaro,
Dangin sa da ma abokai,
Su zo ajon bikin sa.
Amma dai shi rabon ka,
Wani sa’in in ka lura,
Gona ce sai da noma,
Ko da da ruwa da taki.
Ita gona babu gyara,
Ba noma ko da taki,
Da wuya tai shar da kore,
Ran girbi tai yabanya.
Yau rabo ya zo gare ka,
Zakin mu Aminu Ado,
Sarki na Kano garin mu,
Giwa bukka a daji.
Duniya yau ta yi shaida,
Rawani malafa ta kan ka,
Ta Dabo ƙasa da Ado,
Ado ɗan Abdu gwarzo.
Rimi ado ga birni,
Dattijo kwanin nagarta,
Mai karamci ga mutunci,
Tamkar Ado fa ba shi.
San Kanon mu Aminu Ado,
Saurayin zaki a daji,
Kuraye na ganin ka,
Su kalla nan su bar ka.
Aminu Ado gwanin mu,
Addu’ar yaran garin mu,
Sai kai sarkin Kanawa,
Jallah ya amsa da ran mu.
Gado da rabon ka ga shi,
Sun sa yau ka yi sarki,
Ka gaji gadon gidan ku,
Tilas kowa ya bi ka.
Sai ka yi Aminu sarki,
Addu’ar kowa gare ka,
Yau ka yi Aminu zaki,
Riƙe kowa da kyawu.
Arziki jarin mutum ne,
Kirkin ka ya sa Kanawa,
A birni har a ƙauye,
Kowa ke son ganin ka.
Ƙasar shuri sani na,
Babu mai ci sai fa wawa,
Marar mafaɗi da wauta,
Ke jayayya da Allah.
Hassada tabbas mutane,
Na sa mai yi ya taɓe,
Shi ko dai zaki Aminu,
Ta zame taki gare shi.
Ɗan gogarman mu Ado,
Zakin duniya sadauki
Dutse wallahi Allah,
Na sanya gara hawaye.
Kukan zuci da fili,
Gara sai dai ta yi shi,
Dare safiya da hantsi,
Don dutse ba ta cin shi.
Ga muruci yau na dutse,
Ya shirya kan ya ɓullo,
Dogaron sa guda Ilahu,
Gatan bayi gaba ɗai.
Jika na Abashe sarki,
Da Dabo uba masoyi,
Ɗan Abdullahi haske,
Magani na duhu saraki.
© Khalid Imam
6/7/2021
