ALLAHU Akbar! Rai baƙon duniya. A daren Laraba, 8 ga Mayu, 2024 Allah ya ɗauki ran Malama Salamatu Musa Makka, ƙanwar tsohuwar jaruma a Kannywood, Hajiya Safiya Musa.
Yayan ta, Malam Abdullahi Musa Makka, ya faɗa wa mujallar Fim cewa Salamatu ta rasu ne da misalin ƙarfe 11:18 na dare a kan hanyar kai ta Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, a Kano, sakamakon rashin lafiya mai tsanani da ya tashi mata a daren. Amma kuma da ma ta na fama da rashin lafiyar tsawon kwana huɗu kafin ranar.
Marigayiyar mai kimanin shekara 35 ta rasu ta bar mijin ta Alhaji Auwal da ‘ya’yan su guda biyu, Ahmad da Jannat.

An yi jana’izar ta a safiyar Alhamis da misalin ƙarfe 10:15 na safe a unguwar Ja’en, Sharaɗa, sannan aka kai ta gidan ta na gaskiya a maƙabartar unguwar.
Wakilin mu ya ruwaito cewa ‘yan fim da dama sun halarci jana’izar ta, haka kuma wasu sun je ta’aziyya.
Allah ya jiƙan ta da rahama, ya albarkaci dukkan abin da ta bari.