INNA lillahi wa inna ilaihir raji’un! Masana’antar Kannywood ta ƙara yin babban rashi na shugaban Ƙungiyar Mawaƙa ta Jihar Kaduna, Alhaji Sani Ciyaman Ɗangiwa, wanda Allah ya yi wa rasuwa ɗazun nan.
Wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa Alhaji Sani, wanda ya na ɗaya daga cikin shugabannin haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kaduna, ya rasu sakamakon rashin lafiya.
Za a yi jana’izar sa gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Tuni ɗimbin ‘yan fim su ka fara tura saƙwannin ta’aziyya tare da addu’ar Allah ya jiƙan shi.
Mu na fatan Allah ya rahamshe shi, amin.