MAI Martaba Sarkin Kalshingi da ke cikin Ƙaramar Hukumar Yamaltu/Deba a Jihar Gombe, Alhaji Hussaini Abubakar Magaji, ya naɗa mawaƙi a Kannywood, Alhaji Aliyu Ibrahim, wanda aka fi sani da Ali Haidar, sarautar ‘Ɗan Adalan Kalshingi’.
A jiya Litinin, 5 ga Disamba, 2022, masarautar ta Kalshingi ta fitar da takardar sanar da Haidar sarautar da ta ba shi.
Takardar, wadda ke ɗauke da sa-hannun Sarkin Kalshingi, Alhaji Hussaini Abubakar Magaji, ta ce masa, “Duba da irin kyawawan halin ka na shugabanci da kyakkyawan alaƙa mai tsawo da sha’awa da ka ke nunawa da ya shafi al’umma da tattalin arziƙin gundumar Kalshingi da Jihar Gombe baki ɗaya, shugaban gundumar Kalshingi, majalisar gargajiya da kuma masu naɗa sarki, sun naɗa ka sarauta mai taken ‘Ɗan Adalan Kalshingi’.”

Sarkin ya ci gaba da cewa, “Tare da bayar da wannan sarauta, yanzu ka zama ɗaya daga cikin masu ba da shawara a gundumar Kalshingi da su ka shafi zaman lafiya, haɗin kai, cigaba, zamantakewar mutane da tattalin arziƙi.”
“A madadin gundumar Kalshingi, mu na taya ka murna, mu na kuma duba lokacin da ya dace a yi naɗi a hukumance.”
Mujallar Fim ta ruwaito cewa Ali Haidar mawaƙin siyasa ne, musamman a gidan tsohon gwamnan Kano Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso. Haka kuma ɗan Jihar Kano ne, amma mazaunin Kaduna.