MAI Martaba Sarkin Ƙaraye a Jihar Kano, Alhaji Abubakar Ibrahim II, ya bayyana matakin da ƙungiyar mawaƙan gargajiya da ƙungiyar mawaƙan zamani su ka ɗauka na farfaɗo da ragowar al’adun gargajiya na Hausa a matsayin wani abin a yaba ne.
Tun tuni ake ganin al’adun gargajiya na Hausa sun fara fara ɓacewa a wasu yankuna na ƙasar nan inda ake aro ɗabi’un wasu mutanen.
Alhaji Ibrahim Abubakar II ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin ƙungiyar a yayin wata ziyarar ba da shawara da su ka kai wa Sarkin a fadar sa.
Jami’in yaɗa labarai na masarautar, Haruna Gunduwawa, ya shaida mana ta cikin wata sanarwa da ya aiko da ita a ranar Alhamis, cewa Sarkin ya tabbatar wa da ƙungiyoyin goyon bayan masarautar domin cimma burukan da su ka sanya a gaba, “don ganin cewar an bai wa al’adun mu muhimmanci ta ko wanne fanni.”