FITACCEN mawaƙi Aminuddeen Ladan Abubakar (ALA) ya bayyana cewa ya tsaya takarar zama ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ADP a zaɓen shekarar 2023.
Ya ce ya na neman kujerar memba ne mai wakiltar Mazaɓar Tarayya ta Nassarawa, Kano.
Sha’irin ya bayyana haka ne a saƙwanni uku da ya wallafa a Facebook da Instagram inda ya yi jawabi kamar haka: “Mulki na Allah ne, ya na bai wa wanda ya so a san da ya so.
“Mun fito da ƙarfin Allah tare da goyon bayan mutane don mu wakilci mutane daga cikin mutane zuwa ga mutane don mutane. Mu na nemar yardar Allah tare da roƙon Allah ya sa mutane su yarda da manufofin matuƙar ba su kauci tafarkin nagarta ba.”
A saƙo na biyu da mawaƙin ya wallafa a soshiyal midiya, ya ci gaba da yin addu’ar cewa: “Kamar yadda Allah ya ba mu damar bayyana kai a rukunin masu shirin wakilcin jama’a, mu na neman tallafawar Allah a cikin dukkan motsi da gilmawar mu a kan wannan ƙudiri.
“Allah ka ƙaddara wannan yunƙuri ya zama alkhairi ga al’umma.

“Allah ka sa ya zama cigaban ƙasa ta, Allah ka sa ya zama alfanu a gare ni da al’ummar yankin Nassarawa kafatanin su.
“Cikakken misali ga masu niyyar takara duba da cancanta da nagarta. Masoya ga ranar ku daga duk inda ku ke za ku bai wa wannan tafiya gudunmawa. A duk inda ka ke ba ka rasa ɗan’uwa ko masoyi a Ƙaramar Hukumar Nassarawa ba.
“Ku zaɓi jam’iyyar ADP, Action Democratic Party, don karya manufar tsarin mulkin bayan-na-yi ɗa-na-ya gaje-ni.”
Haka kuma a rubutun sa na uku Ala ya ce: “Kada ka yi taraddadi da abin da idon ka ya nuna maka zahiri ne.
“Lokaci na a cirata a fidda ɗan takara daga cikin mutane ya yi wakilci don mutane.
“Ka sa a ran ka mulki na Allah ne kuma ya na bai wa wanda ya so.
“Ka sami nutsuwa da ƙarfin gwiwa a kan nasara ta jajirtattun bayi ce waɗanda su ka kamaci kamata.
“Mu na neman goyon bayan ku masoya, kamar yadda ɗimbin nasarori da su ka faru su ke kan faruwa da gudunmawar ku da hannun ku, wannan karon ma mu na neman goyon baya da addu’a a duk inda ku ka kasance.”
Taken takarar Ala dai shi ne: “Mu Gudu Tare Mu Tsira Tare”, wanda ya rubuta a jikin fastocin da ya wallafa tare da saƙwannin.
Wannan takara da ya fito, ya bi sahun abokin sa Dauda Adamu Abdullahi Rarara a ƙarƙashin ƙungiyar 13×13, ganin ADP ce Rarara ɗin ya ke yi a Jihar Kano, inda ya bi ɗan takarar gwamna na jam’iyyar, wato Sha’aban Ibrahim Sharaɗa.
Ɗimbin masoya sun taya Ala fatan alheri da addu’ar samun nasara a wannan niyya da ya ɗaura.