DARAKTA Salisu Mu’azu ya bayyana cewa ba a fim ɗin ‘Jumma’ ba ne Ali Nuhu ya fara shiga fim kamar yadda furodusa Sani Muhammad Sani ya yi iƙirari.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba da labari kan wani rubutu da Sani ya yi a Facebook inda ya yi martani ga masu cewa a shirin ‘Abin Sirri Ne’ da aka shirya a Kano ne Ali ya fara yin fim.
Malam Sani ya ce akasin hakan, a fim ɗin sa mai suna ‘Jumma’ ne jarumin ya fara fim, a Jos, kafin ma ya je Kano.
Wannan magana ta Sani ta samu gyara daga wani fitaccen mashiryin fim daga Jos, wato darakta Salisu Mu’azu.
A rubutun martani da ya yi kan labarin da mujallar Fim ta buga, Malam Salisu, wanda shi ma furodusa ne, ya ce: Tarihi abu ne mai matuƙar muhimmanci, musamman idan ya samu gurin da aka bi matakan rubuta shi daki-daki. Ɗaya daga cikin tarihi shi ne sahihancin labarin.
“Na ji daɗin rubutun Sani Muhammed Sani da ya yi tsokaci kan wannan gaɓa da na ke magana a kai. A dalilin haka ne ya sa na ga ya dace na fitar da abin da yake na gaskiya kuma sahihi game da shigowar Ali Nuhu masana’antar finafinai, musamman mataki na farko na shigowar sa.
“Ali Nuhu ya fara da wani fim mai suna ‘Hadarin Masoya’. Shi wannan fim, shi ne dalilin haɗuwar mu guri guda, don kafin wannan fim wasun mu ma ba su san juna ba.
“Waɗanda su ka taka muhimmiyar rawa wajen shirya wannan fim akwai irin su marigayi Ibrahim Achimota, Ali Nuhu (wanda shi ya fara rubuta labarin, kafin daga baya ni ma na rubuta wannan ɓangare na fim ɗin), akwai ni (Salisu Mu’azu), Tijjani Sani, marigayiya Hadiza Ɗanjuma, Salamatu, Ladi Salisu (marigayiya), sai Magaji Mijinyawa wanda shi ne darakta na fim ɗin.
“Shi wannan fim Hadarin Masoya shi ya haifar da masana’antar shirya finafinai a Jos, don kafin ita television drama kawai mu ka sani. Wanda yayyin mu irin su Auwalu Salihu, Sani Mu’azu, Waziri Zaiyanu, Magaji Mijinyawa da sauran su suke fitowa a ciki, mai suna ‘Bakandamiya’.
“Shirin ‘Bakandamiya’ shiri ne da lokacin ya fi irin shirye-shiryen wasan kwaikwayo na talabijin kamar su ‘Ƙarƙuzu Na Bodara’ kyau da inganci. Amma shi ba a yi shi don kasuwanci ba.
“Shi kuma ‘Hadarin Masoya’ an shirya shi ne don kasuwanci kawai. Kuma shi ne fim ɗin da New Era Cinema su ka fara nunawa na Hausa.
“Shi ma yadda aka nuna shi wani dirama ne wanda sai wani lokaci zan rubuta. Amma tsololon labarin shi ne bayan wahala da mu ka sha kafin mu shawo kan mahukuntan gidan sinimar da su yarda a nuna. Ranar da su ka amince za su nuna babban ƙalubalen mu shi ne yadda za a yi poster. Don a lokacin babu poster idan ba na finafinan waje ba.
“Na taƙaita dai, a ƙarshe dai da zanen pencil (drawing) da shi mu ka nuna fim ɗin.
“Mu koma kan shigar Ali Nuhu fim. Bayan ‘Hadarin Masoya’ shi ne Sani Muhammed Sani ya zo da ‘Jumma’ da kuma ”Yancin Ɗan Adam’ na Waziri Zaiyanu. Shi ya sa idan mutum ya kalli duk finafinan uku duk mu ne a cikin su.
“Alal haƙiƙa, duk wanda sunan shi ya bayyana a rubutu na na sama ya na daga cikin waɗanda su ka ba da gagarumar gudunmawa wajen samar da masana’antar finafinai a Jos. Kuma tarihi ba zai taɓa mantawa da su ba.
“Watakila a ajizanci irin na ɗan’adam (ya sa) na manta da sunan wasu. Idan an samu irin wannan akasin, ina neman afuwar ko waye.”