SHUGABAN Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Katsina, Comrade Lawal Rabe Lemo, ya yi kira ga ‘yan fim na jihar da su dunƙule su zama tsintsiya-maɗaurin-ki-ɗaya domin su gudu tare su tsira tare.
Shugaban ya yi kiran ne a lokacin da ya ke tattaunawa da mujallar Fim sakamakon wani taron shiyya da su ka yi a garin Funtuwa a ranar Lahadi, 3 ga Satumba, 2023.
Sun yi taron a ɗakin taro na Focus International School da ke titin Sokoto Bypass kusa da Kasuwar Raguna ta Madalla a garin na Funtuwa.
A hirar sa da wakilin mu, Comrade Lawal Rabe Lemo, wanda shi ne ya jagoranci taron, ya yi roƙo ga ‘yan fim na jihar, inda ya ce, “Don Allah mu aje duk wani bambance-bambancen ra’ayi da mu ke da shi, mu zo mu zama tsintsiya-maɗaurin-ki-ɗaya, ba don komai ba sai don mu ciyar da harkar fim gaba, saɓanin kallon da ake yi wa harkar fim a da, wanda ana yi mata kallon wani abu daban, mu kuma mun fahimci harkar fim sana’a ce. Kamar yadda kowane mutum zai iya ɗaukar jarin sa ya sa a kowace sana’a don ya ci riba, haka ita ma harkar fim ta ke, ba wata aba ba ce ta sharholiya ba.
“Ina kira da su yi haƙuri mu haɗu, mu gudu tare, mu tsira tare. Wannan bambance-bambancen ba zai kai mu ga nasara ba. Ko gwamnati ta fi so ta gan ku a dunƙule, ko taimakon ku za ta yi, za ta fi jin daɗin taimakon ku.”
Da ya ke yi wa mujallar Fim ƙarin bayani kan maƙasudin shirya taron na Funtuwa, Lawal ya ce, “Maƙasudin taron, na farko, ya zama cewa mu na ‘updating’ membobin mu da ke shiyya-shiyya. Ka san taro in aka ce za a yi shi sau ɗaya a shekara, a kuma babban birnin jiha, misali Katsina, wani memban da ke Funtuwa ko shiyyar Daura ba zai sami zuwa ya san halin da ake ciki ba. Sai mu ka ga me ya kamata a yi, sai mu ka ce mu riƙa yin mitin ɗin a ‘zonal’, ya zama cewa za mu iya yin mitin a ‘Funtuwa Zone’ bayan wani ɗan lokaci mu yi, wanda mu ka sanya wata huɗu-huɗu; za mu iya zuwa Daura, za mu iya zuwa Katsina, sai ya zama cewa duk shiyyar da aka je, ko ba komai membobin da ke nan za a iya sanar da su halin da ƙungiya ta ke ciki ta ɓangaren nasarori da aka samu da kuma akasin haka nan.”
Dangane da idan da ma can sun saba yin irin wannan taron ne ko kuma wannan ne na farko, sai shugaban ya ce, “A’a, wannan ba shi ne na farko ba. Kamar Funtuwa can baya da daɗewa, kamar a shekarar 2020 mun yi a ranar 11 ga Oktoba. Ya kamata kuma a ce a shekarar 2021 mun yi, sai kuma aka samu matsalar rashin tsaro da ta dabaibaye wannan yankin, kuma lokacin aka datse mana ‘network’, sai ya zamana babu hanyar sadarwa balle a sake zuwa a yi wannan taron.

“To, da ma da mu ka yi a Funtuwar, a 2021 sai mu ka tafi Daura aka yi. Mu na gamawa Daura, sai mu ka tafi ‘Katsina Zone’ shi ma mu ka yi, a 2021 ɗin 8 ga watan takwas.
“Kuma ka san akwai lokacin da uwar ƙungiyar ta ƙasa ta ba mu umarnin a dakatar da duk wasu ayyuka na Kannywood, saboda matsalar korona. Wannan shi ma ya ɗan kawo tsaiko.”
Game da abin da su ka tattauna a wurin taron na Funtuwa, Lawal ya ce, “Kamar yadda na faɗa maka cewa na farko mu yi ‘updating’ membobi game da nasarorin da aka samu da kuma akasin haka nan, wanda kaɗan daga cikin nasarorin da mu ka samu ɗin, mun zauna da su membobi na wannan shiyyar cewa akwai cigaba da aka samu a jiha da kuma mataki na ƙasa.
“Na jiha akwai batun ofis, wanda a da ba na dindindin mu ke da shi ba, amma Allah cikin nashi iko mun yi ƙoƙari gwamnatin Jihar Katsina ta samar mana da ofis na dindindin a nan inda mu ke cewa, ‘Centre for Reserch and Documentation’, Rafukka ‘former office’. Ka ga wannan ba ƙaramar nasara ba ce samun wannan ofis ɗin.
“Akwai wasu finafinai kuma, wanda mu ka samu haɗin gwiwa wanda aka yi. Na farko akwai wani fim mai suna ‘Rashin Sani’, mun samu haɗin gwiwa da ‘Ministry of Information, Culture and Home Affairs, Katsina State. Membobi ne na MOPPAN su ka shiga cikin shi, su ka taka rawa, da ‘crew’ ɗin da ‘cast’ ɗin baki ɗaya.
“Sannan akwai batu na rantsar da shugabannin ƙungiya na jiha, wanda shi ma an yi shi 4 ga Satumba, 2022, shekara ɗaya kenan, a matakin jiha, wanda aka yi shi a ɗakin taro na tsohon Gidan Gwamnatin Jihar Katsina. Waɗannan su na daga cikin nasarorin da aka samu a jiha.
“Sai kuma matakin ƙasa. Akwai gayyata da mu ka samu daga uwar ƙungiya, na farko dai mun je an gudanar da zaɓe na ƙasa, wanda aka samu shugabanni na ƙasa, inda aka sake zaɓen Dakta Ahmed Sarari a matsayin sabon shugaban MOPPAN karo na biyu. Akwai taro na haɗin gwiwa da MOPPAN da hukumar NDLEA, shi ma an ba mu katin gayyata, mun je mun wakilci Jihar Katsina. Akwai kuma wanda aka yi da MOPPAN da National Censorship Board, an ba mu katin gayyata, shi ma mun je, an yi wannan taron da mu. Sannan nan baya-baya akwai issue da ta taso ƙila ka san shi kai ma, wanda sabon Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Abba El-Mustapha, ya ce ya soke lasisin duk ‘yan Kannywood, wanda mu ka ga ba daidai ba ne, uwar ƙungiya ta gayyace mu baki ɗaya, mu ka je mu ka zauna da shi, mu ka tattauna aka samu fahimta, inda ya sauko da matsayar shi ta soke lasisi, an koma sabunta lasisi. Wannan shi ma ya na daga cikin abin da su ka faru ne, wanda mu ka je mu ka sanar da su halin da ake ciki.”

Waɗanda su ka halarci taron dai sun haɗa da dukkan shugabannin MOPPAN na Jihar Katsina, irin su Aminu Musa Bukar, Yasir Abubakar, Halliru Daura, Ibrahim Sani Funtuwa, Umar Abubakar, da A’isha Adam daga Kaduna, wadda ta je domin ta sa albarka.