SHUGABAN riƙo na Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Alhaji Habibu Barde Muhammad, ya taya Sakataren Yaɗa Labarai na ƙungiyar, Malam Al-Amin Ciroma, murnar samun muƙamin Janar Manaja na gidan talabijin na Tozali da ya yi.
Alhaji Habibu ya ce, “Alhamdu lillah da naɗin mafi dacewa na Babban Sakataren Yaɗa Labarai na MOPPAN na ƙasa, Malam Al-Amin Ciroma, a matsayin sabon Janar Manaja na ‘Tozali TV’ a nan Abuja.
“Kamar yadda a ko yaushe mu ke mutuntawa da kuma amincewa da kuzarin ka a cikin wannan kyakkyawar sana’a tamu, mu na da ƙwarin gwiwa kan tsayin daka da ikon ka na isar da abin da kowa ke tsammani a matsayin sabon Janar Manajan gidan talbijin na Tozali mai daraja.”
Barde ya yi wa sabon shugaban addu’a da cewa, “Allah ya tsare ka, ya kare ka kai-tsaye yayin da ka ke ɗaukar rigar jagoranci wanda zai buƙaci mafi kyawun aikin ka a kowane lokaci.”
A madadin ɗaukacin MOPPAN shugabannin ƙungiyar, ya yi fatan Ciroma zai karɓi mafi girman gaisuwa da taya murna yayin da ya fara wani sabon babban nauyi baya ga kasancewa amintaccen sakataren yaɗa labarai na MOPPAN na ƙasa.
Ya ce, “Na yi imani da gaske cewa ka cancanci ɗaukar ayyuka biyu masu buƙata tare. Ci gaba da kasancewa cikin albarka.”