Sabbin shugabannin Ƙungiyar Daraktoci ta Prossinal Film Directors Association, sun karɓi rantsuwar kama aiki bayan zaɓar su da aka yi a matsayin halastattun shugabanni domin gudanar da jagorancin ƙungiyar.
Taron rantsuwar kama aiki da aka gudanar da shi a ranar 24 ga Nuwamba 2024 a ɗakin taro na Millennium Hoall dake Tahir Guest Palace da misalin ƙarfe 1 na rana ya samu halartar manyan baƙi domin gane wa Idon su yadda bikin rantsuwar zai kasance.
Shugabannin dai da aka rantsar sun haɗa da Nasiru B. Muhammad a matsayin Shugaba, adiq N. Mafia Mataimakin Shugaba na ɗaya, Dakta Ashir Tukur Mataimakin Shugaba na biyu, Kamal S Alkali a matsayin Babban Sakatare, sai Ibrahim Elmu’azz a matsayin Mataimakin Sakatare.

Sauran sun haɗa da Ismael Khalil Ja’en Ahmad Bifa Almustapha Adam Muhd, Hassan Giggs Alfazazi Muhammad Abdullahi M Dausayi (Nalako) Bashir G. Sharif Aminu Munnir K-ezer Hauwa A Ballo Kamalu Mijinyawa da Ameen M Auwal.
Da yake jawabi bayan rantsar da su a matsayin shugabanni, sabon Shugaban Ƙungiyar Daraktoci ta PROPDA, Nasiru B Muhammad ya bayyana cewa “Abin da na sani shi ne, da yawan mu da muka karɓi wannan matsayi muka yarda za mu yi wannan tafiya shi ne kawo ci gaba. Saboda daman ita tafiya idan aka samu mutane da tunanin su ya zo daya, to tafiya za ta yi kyau, kuma muna da wannan fatan.
Yanzu abin da muke roko kamar yadda a baya aka yi kira da a yi kokari a bayar da hadin kai, to muna rokon wannan hadin kan ga ‘yan kungiya. Mu kuma za mu yi bakin kokarin mu, mu ga mun kai duk wani Daraktan da yake Arewacin Nijeriya matsayin da in sha Allah ba za a raina shi ba.
Saboda abin da muke fada a koda yaushe shi ne. Daya daga cikin abin da yake tsorata mu shi ne Turanci, wanda ba don tsoron Turancin ba na san akwai Daraktoci da yawa da abin da kawai za su nuna mana shi ne sun yarda za su iya da kuma Turancin, Amma dai mu basirar akwai ta. Kuma da yawa sai yanzu suka farga suka fahimci muhimmancin ilimin. Kuma da yardar Allah za mu yi bakin gwargwadon iyawar mu don mu ga yadda za a yi mu ma ilimin ya zo mana na zamani, wanda za mu iya cewa mun fara da tallafin Ameenu M Auwal da ya samar mana da wani horo da aka yi wa Daraktoci a sati biyu da suka gabata, Wanda kuma tun daga nan an fara gane cewa za a iya kaiwa inda ake so.
Don haka muna da shirin kulla Alaka da kungiyar Furosushi ta Kannywood da kuma kungiyar marubuta Jarumai da sauran kungiyoyin da suke cikin Kannywood, wanda sai mun samu kyakkyawar Alaka a tsakanin mu ne za mu tafiyar da sana’ar mu yadda ya kamata domin su ne abokan aikin mu.
Allah ya sa mu dace kuma Allah ya yi mana Jagora”.
Jama’a da dama ne dai suka halarci taron. Cikin manyan bakin da suka halarta akwai Farfesa Abdallah Uba Adamu wanda shi ne Shugaban kwamitin aminttatu na kungiyar (BOT) Wakilin Shugaban hukumar Fim ta Kasa NFC Shugaban Hukumar tace finafinai ta Jihar Kano Abba El-Mustapha Tsohon Shugaban kungiyar MOPPAN na Kasa Dakta Ahmad Muhammad Sarari. Da sauran manyan baki.