• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Shugabar matan Kannywood ta kare masu karakaina a ƙasashen waje

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
January 24, 2020
in Labarai
0
Hauwa A. Bello

Hauwa A. Bello

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
SHUGABAR Ƙungiyar Matan Kannywood ta masu shirya finafinan Hausa (‘Kannywood Women Association of Nigeria’, K-WAN), Hajiya Hauwa A. Bello, ta kare ‘yan’uwan ta jarumai mata waɗanda ke karakaina a ƙasashen ƙetare.
 
Ta ce kallon da ake yi masu ba haka ba ne.
 
Hauwa ta na magana ne a kan wani rahoto da mujallar Fim ta buga a makon jiya mai taken “Ina Matan Kannywood Ke Samun Kuɗi Su Na Zarya A Ƙasashen Waje?”
 
A rahoton, mujallar ta yi labarin yadda ake ganin wasu ƙalilan daga cikin fitattun jarumai mata su na yawace-yawace a ƙasashen waje da sunan yawon buɗe ido ko zuwa Umrah, inda ta yi ayar tambaya kan inda su ke samo maƙudan kuɗaɗen da su ke kashewa a tafiye-tafiyen bayan kuma yanzu ba fim su ke sosai ba.
 
Irin waɗannan jaruman sun haɗa da Hadiza Gabon, Rahama Sadau, Nafisat Abdullahi, Fati Washa, Sapna Aliyu Maru, da ma wasu.
 
A cikin 2019 kaɗai an ga wata ko wasun su a ƙasashe da su ka haɗa da Amurka, Ingila, Faransa, Cyprus, Indiya, Dubai, Saudiyya, Ethiopia, Spain, Masar, da sauran su. 
 
Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da harkar fim ba ta ci saboda lalacewar kasuwa, babu mai samun wani abin a zo a gani.
 
A martanin da ta turo wa mujallar, Hauwa A. Bello ta ce, “Su na da hanyoyin samun kuɗi duk da cewar a yanzu harkar kasuwar finafinai ta na cikin wani yanayi na durƙushewa, a sakamakon halin da ƙasar ta ke ciki.”
 
Ta ce ba shakka ba daga harkar fim jaruman ke samun manyan kuɗaɗe ba.
 
Shugabar, wadda aka fi sani da Hauwa Edita, ta ce waɗannan jaruman su na samun talla daga manyan kamfanoni, kuma an koyar da su yadda za su caji maƙudan kuɗi a kan kowace talla.
 
Ta yi nuni da cewa kamar Hadiza Gabon da aka bada misali da ita, ai ta na tallar kamfanoni irin na su Ɗangote, ta ce, “To nawa ta ke samu a wannan tallar?” 
 
Haka kuma ta ce ‘yan fim ɗin sun yi tallar ‘yan siyasa a zaɓen da aka yi bara, don haka idan sun je yawon shaƙatawa ai don su na samun kuɗin ne.
 
Ta ƙara da cewa, “Ko da aka ce su na yawan fita, to sau nawa su ke fita ɗin? Ai ba ko da yaushe su ke tafiyar ba; wasu ma sai shekara-shekara su ke zuwa.”
 
 
Haka kuma ta ce ya kamata Fim ta tambaye su inda su ke samun kuɗin, ba kawai ta rubuta labari a kan su ba, “domin na san duk wacce aka samu ana so a yi hira da ita babu wacce za ta ƙi.”
 
Sai dai kuma kamar yadda labarin ya nuna, wakilan mujallar sun tuntuɓi wasu daga cikin waɗannan jaruman kan lamarin, amma su ka ƙi magana in ban da Sapna wadda ta ce ita da ma ta saba zuwa Dubai saro kayan da ta ke sayarwa a shagon ta.
 
Hauwa Edita ta ce, “Mata su na son idan sun samu kuɗi su ji daɗi, su killace kan su, to shi ne su ma ‘yan fim ɗin su ke tafiya su zagaya duniya.
 
“Kamar sauran mutane ne, su na son su ji daɗi, don haka tun da Allah ya riga ya ɗaukaka su su na da wajen da za su samu kuɗi.”
 
Tambarin Ƙungiyar Matan Kannywood ta Nijeriya
Sannan a kan zargin da wani ya yi a cikin labarin mujallar cewa matan kan samu kuɗi ne a wajen maza, Hauwa ta ce, “Kowa ya san mace a wajen namiji ta ke samun kuɗi, to haka ma su ‘yan fim mata a wajen maza su ke samun kuɗin su.” 
 
Sai dai ta ce maza kan yi wa matan hanyar samun kwangilar talla, ba kamar yadda ake tunani ba.
 
Ta ce: “Kuma akwai abubuwa da dama da za a yi a samu kuɗi, ba sai an yi fim ba. Kamar mu ƙungiyar mu ta Matan Kannywood akwai hanyoyi da dama da mu ka bijiro da su na talla da sauran su.”

Loading

Previous Post

Ban bar Kannywood ba, inji Hadiza Kabara

Next Post

Gwamna ya naɗa furodusa Al-Kenanah shugaban hukuma a Kano

Related Posts

AFMAN ta taya Sarari murnar samun damar halartar taron baje-kolin finafinan Nijeriya a Toronto da fim ɗin ‘Kakanda’
Labarai

AFMAN ta taya Sarari murnar samun damar halartar taron baje-kolin finafinan Nijeriya a Toronto da fim ɗin ‘Kakanda’

June 16, 2025
Naɗa ni jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry Powder da aka yi zai amfani Kannywood baki ɗaya, inji furodusa Abubakar Galadima
Labarai

Naɗa ni jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry Powder da aka yi zai amfani Kannywood baki ɗaya, inji furodusa Abubakar Galadima

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
Next Post
Abdallah Tahir Al-Kenanah

Gwamna ya naɗa furodusa Al-Kenanah shugaban hukuma a Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!