HUKUMAR Tace Finafinai ta Jihar Kano (KSCB) ta janye dokar nan da ta nemi ƙaƙaba wa ‘yan fim kwanan nan wadda ta soke lasisin dukkan masu yin harkar fim a jihar.
Yanzu za a sabunta wa kowane mai yin harkar fim rajista ne ta hanyar ƙungiyoyin ‘yan fim waɗanda ke ƙarƙashin Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya, wato MOPPAN.
Hakan ya biyo bayan saka bakin da MOPPAN ɗin ta yi inda ta ba da shawarar cewa a sabunta wa kowa rajista ta hanyar ƙungiyar da ya ke ciki.
Wannan bayanin ya na ƙunshe ne a cikin takardar sanarwa ga manema labarai wadda kakakin MOPPAN na ƙasa, Malam Al-Amin Ciroma, ya rattaba wa hannu kuma ya turo wa da mujallar Fim a ranar Laraba inda a ciki ya ce an cimma wannan matsayar ne lokacin da Shugaban MOPPAN, Dakta Ahmed Sarari, ya kai ziyarar ban-girma ga Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Malam Abba El-Mustapha Inuwa, a ofishin sa domin ya taya shi murnar naɗin da aka yi masa, sannan ya sanar da shi manufofin kafa MOPPAN.
Idan an tuna, dokar da hukumar ta so ƙaƙabawa ta gamu da ra’ayoyin jama’a mabambanta; yayin da ‘yan fim su ka soki lamirin dokar, wasu kuwa sun cewa ta yi daidai.
Ciroma ya ce a lokacin ziyarar, Dakta Sarari ya faɗa wa El-Mustapha cewa MOPPAN ce kaɗai ƙungiyar da Gwamnatin Tarayya ta sani a Arewa ta hanyar Hukumar Tace Finafinai ta Nijeriya (NFVCB), kamar yadda sashe na 17(2) da (3) na dokar hukumar ta 2008 ya tanada.
Haka kuma Sarari ya ce ya kamata dukkan dokokin jiha da na tarayya su yi aiki tare, maimakon su riƙa cin karo da juna.
Ya kuma tunatar da hukumar cewa sashe na 84 na kundin dokokin KSCB ya ce, “Dukkan ma’aikatan shirya fim za su kasance membobi masu rajista a ƙungiyoyin da Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta amince da su.”
Ya ce alfanu ne ga ita kan ta hukumar da kada ta soke lasisin masu harkar fim a Kannywood kamar yadda aka so a yi da fari, ya na mai roƙon KSCB da ta duba yiwuwar sabunta wa jama’a rajista domin a samar da kyakkyawar fahimta da yanayi mai kyau tsakanin ta da ‘yan fim.
Bugu da ƙari, ƙungiyar ta shawarci hukumar da ta duba yiwuwar ƙirƙiro da wani sashe da zai kula da ba da gudunmawa ga masana’antar da kuma haɓaka ta domin a ƙarfafa masu sana’ar ta hanyar inganta hanyoyin sayar da fim, horas da masu harkar da kuma ƙara masu ilimi kan yadda ake yin harkokin ta matakin ƙasa da na ƙasashen ƙetare.
A nasa jawabin, El-Mustapha ya bayyana jin daɗi tare da godiya ga shugabannin MOPPAN da su ka hanzarta su ka shigo cikin maganar kuma ya ɗauki shawarwarin da Sarari ya kawo, sannan ya ce a shirye hukumar ta ke ta haɗa gwiwa da MOPPAN don a haɓaka harkar fim baki ɗayan ta.
Babban sakataren ya ƙara da cewa hukumar tasa ta ɗauki shawarar a sabunta wa jama’a rajista kamar yadda MOPPAN ta nema.
Ya yi godiya ga shugabannin MOPPAN kuma ya faɗa masu cewa ƙofar sa a buɗe ta ke a kullum domin karɓar suka ko shawarwari masu ma’ana tare da gudunmawa da fahimtar juna.
Ina taya Abba El mustapha murna zama shugabanmu