“Ya kai tsaye ga wani ya tsaya
Yanzu gwanin wani zai tafi lahira
Ya kashe ka ya taka ma wuya,
Mu ko mu bi shi a baya da tambura”
– Sarki Usaini a taken Raba-Gardama
A LOKACIN da mu ke jimamin mutuwar Alhaji Bashir Tofa, Dakta Datti Ahmad, da Sheikh Ahmad Bamba, sai kuma ga shi a daren nan Allah ya karɓi ran ɗaya daga cikin manyan ‘yan damben da tarihin dambe a Nijeriya ba zai taɓa mantawa da su ba, wato Muhammadu Ɗansanyinna wanda aka fi sani da Muhammadu Raba-Gardama.
Muhammadu ya yi tashe a shekarun 1980 zuwa na 1990, tun bayan da manyan ‘yan dambe irin su Shago, Ɗandunawa da Ado Ɗankore su ka kwanta dama a fagen. Shaharar sa da nasarorin da ya samu a zamanin da ya ke tashe sun sanya ya zama wani abin kwatance a wannan lokaci.
Ban dai iya tuna ko a wane ɓangare Muhammadu ya ke a zamanin sa, Kudu ko Arewa, ko Guramaɗa (Jamus) ne. Amma dai ba na zaton Guramaɗa ne, tunda su zallar Fulani ne a cikin su.
Muhammadu ya zama jagoran wasu manyan ‘yan dambe na zamanin sa, irin su babban hafsan sa, Amadu Gurɗe, Sani Ƙanin Basafce, wanda kowane ɗaya a cikin su babbar gayya ne.
Koda yake Muhammadu ya yi agar a zamanin sa, amma bai ci karen sa babu babbaka ba, domin sai da ya samu kishiya, wato Duna na Indabo, wanda aka fi sani da Ɗancana, da kuma wasu manyan yaran sa irin su Ciroma Adamu Ɗansarki.
Muhammadu ya shahara da juriya da rashin tsoro. A iya sani na, in ban da Ɗancana mutum biyu na taɓa sanin sun kashe Raba Gardama a dambe, ɗaya a Sakkwato, ɗaya a Kazaure.
Na sha ganin damben su da Ɗancana; dambe ne kamar ana yaƙi, kuma kowanne a wannan lokaci shegen kan sa ne.
Akwai abubuwa biyu da ba na mantawa da su a game da Muhammadu. Na farko rikicin sa da Ɗandunawa a Ɓaɓura, a wannan lokaci ina zaton Ɗandunawa ya haura shekara goma da barin dambe, amma a tsaurin ido na Muhammadu ya nemi sai ya yi dambe da shi. Wannan fitsara da Muhammadu ya yi masa ta sanya Ɗandunawa ya haɗa shi dambe da wani yaron sa daga cikin Guramaɗa, inda su ka yi damben ya buge Muhammadu a Kazaure. Wannan kisa ya rikita Muhammadu ƙwarai, inda ya tare ƙofar shiga sitadiya ɗin, ya hana kowa shiga ko fita, har sai da Sarki Usaini ya zo ya na kaɗa masa taken sa:
“Zuciya tasa in ta birkita,
Ka ga farar hula ba ta masa,
Ni makaɗin ma har tsoro na ke!”
A wannan rikici sai da Muhammadu ya sumar da jami’an ‘yan sanda har biyu a sakamakon ƙoƙarin su na su kama shi.
Abu na biyu shi ne wani dambe da su ka yi a Sakkwato, inda nan ma bai sa’a ba, aka buge shi. Hakan ta harzuƙa shi, ya nemi lallai a sake damben, amma aka ƙi. Ya hargitsa filin, sai a mota aka sanya abokin damben nasa aka fita da shi. Ganin haka ya bi motar da gudu, ya kai mata naushi, ya samu gilashin motar, duk ya yanke hannu.

Muhammadu mutum ne karimi, mai kyauta, kuma ga iya kwalliya. In ya gama dambe ya ci kwalliya, kai ba ka ce shi ba ne.
A da, na ɗauka Muhammadu ya rasu, sai a ‘yan shekarun nan aka ce min ya na nan da ran sa, har ma ya kan je kallo. Na so in gamu da shi, domin rabo na da ganin sa tun cikin shekarun 1990 lokacin bai ajiye akayau nai ba. Sai dai Allah bai yi hakan za ta tabbata ba.
Allah ya jiƙan shugaban damben Nijeria, ya yafe kurakuran sa, ya sa mutuwa hutu ce.