CIKAKKEN sunan Bature Gagare dai shi ne Ibrahim Lawal. An haife shi a cikin Lamama da ke unguwar Galadunchi a tsakiyar birnin Katsina. Ya yi karatu a Makarantar Firamare ta Gobarau, Katsina (1966-1972), da kuma Kwalejin Barewa, Zariya (1973- 1977). Ya na ɗaya daga cikin haziƙai kuma masu matuƙar ƙoƙari da fahimta, ganewa da cin jarabawa a dukkan karatun da ya yi.
Mahaifin Bature, Alhaji Lawal Gagare, asalin sa mutumin Malumfashi ne. Aiki a hukumar Ene (Native Authority) ya kawo shi Katsina. Ya rasu a lokacin Bature na da kimanin shekara biyu da haihuwa.
Alhaji Tanimu Gagare Kafinta, mahaifi ga Kabir Tanimu Gagare, shi ne ya riƙe Bature Gagare har ya girma.
Binta (Atutu) ita ce mahaifiyar Bature Gagare. Mutunniyar sabon garin Eka ce da ke Ƙaramar Hukumar Rimi ta Jihar Katsina. Mai kimanin shekaru 85, yanzu haka ta na nan raye a garin Kaduna.
Sauran ‘yan’uwan Bature Gagare ciki ɗaya sun haɗa da mariganya Binta, mariganyi Aminu, sai mariganya Murja wadda ta rasu a ranar Juma’a, 26 ga Yuli, 2019, kwana biyu kacal bayan na yi hira da ita tare da wani ɗan’uwan ta mai suna Alhaji Ummaru inda na samu bayanai game da marigayi Bature.
Bature Gagare, wanda ake yi wa laƙabi da BT, bai yi wani dogon karatun boko ba duk da ƙwaƙwalwa da ƙoƙarin da Allah ya ba shi. Amma ya fara Advanced Teachers College, Kafanchan, a Jihar Kaduna, inda ya jagoranci wata zanga-zanga wadda ta yi sanadiyyar barin karatun nasa. Sai ya dawo gida Katsina, ya fara karatu a Makarantar Aikin Jinya (School of Nursing), to amma a nan ma aka samu wata matsala makamanciyar ta ATC Kafanchan, ya bar karatun.
Duk da haka, ya shiga ran malaman sa ƙwarai a dukkan makarantun da ya yi, ganin irin ƙwazon sa da hazaƙar sa a karatu.
BT ya yi fice ƙwarai a harkar rubuce-rubuce da tafiye-tafiye. Littafin sabon na hikaya, ‘Ƙarshen Alewa Kasa’, ya yi fice sosai inda a 1980 ya zamo na uku a gasar rubuta ƙagaggun labarai na Hausa ta ƙasa da aka yi a ƙasar nan, inji Dr Garba Ashiwaju a muƙaddimar littafin da ya rubuta lokacin shi ne Daraktan Ma’aikatar Al’adun Gargajiya ta Tarayya.
Bature ya rubuta wani littafin da ya sa wa suna ‘Tsuliyar Kowa Da Kashi’, to amma ba a samu damar wallafa shi ba sakamakon taƙaddama da aka yi da shi tun daga sunan littafin har ya zuwa bayanan da ke cikin shi.
Wani abu kuma game da Bature Gagare shi ne, shi mutum ne wanda ya iya zane matuƙa; an ce duk abin da ya kalla zai iya zana shi ba tare da kuskure ba balle ɓata lokaci.
Ya rayu da mata uku a lokuta daban-daban. Su ne Balaraba, Amina da Saadatu.
Ya na da ‘ya’ya shida, wato Kabir, Asma’u, Amina (Junior), A’isha, Laila da Zainab.
Bature mutum ne mai matuƙar tsafta. Kuma ya na son abinci na gargajiya kamar ɗanwake, koko, ƙosai, kwaɗo, alkubus, hura, wake da shinkafa.
Kaɗan daga cikin halayen BT sun haɗa da:
1. Son gaskiya da kamanta ta.
2. Mutum ne marar tsoro.
3. Abin shi ko abin duniya ba ya rufe masa ido.
4. Ya na da sada zumunci da son mutane.
Bayan haka, ya na da abubuwan ta’ajibi da ban-mamaki ƙwarai da gaske.
Ya yi tafiye-tafiye a ciki da wajen Nijeriya a ƙasashe da su ka haɗa da Saudi Arebiya, Aljeriya, Dubai da Maleshiya.
Allah ya yi wa Bature Gagare rasuwa a ranar 29/2/2002 a Lamama, Galadunchi, cikin birnin Katsina, sanadiyyar ciwon lamoniya (pneumonia), wato ciwon sanyin huhu. An yi masa sutura a tsohuwar maƙabartar Ɗantakun.
Malam Kabir Umar Saulawa (PRO) ya rubuto ne daga Katsina. Lambar waya: 07034610481