IDAN ana maganar tattalin arziki da bunƙasar al’umma a ƙasar Hausa, dole ne a alaƙanta shi da tsarin gandu, wanda shi ne ginshiƙin farko da al’ummar Hausa ta gina tattalin arziƙin ta tun kafin bayyanar Turawan mulkin mallaka, ta hanyar yin noma da kiwo.
A wata lacca da Farfesa Adamu Idris Tanko ya gabatar a Jami’ar Bayero, Kano, a ranar Litinin, 13 ga Disamba, 2021, ya bayyana yadda ƙasar Hausa ta ginu a tsarin noman gandu da yadda ya samo asali.
Shehun malamin ya ɗora jawabin sa a kan zuwan Turawan mulkin mallaka ƙasar Hausa, da yadda su ka samu wannan tsari. Turawan mulkin mallaka cikin hikima sun sauya fasalin tsarin gandu zuwa yadda mutane ke yi masu bauta tare da noma abin da su ke buƙata daga gyaɗa da auduga, tare tsauwala kuɗin haraji da duk wani baligi zai biya. Hakan ya sare gwiwar manoma wajen noma irin abinci zuwa noman irin da zai kawo kuɗi, saboda kawai su iya biyan haraji.
Sai dai a jawabin Farfesa Abdalla Uba Adamu, ya yi iƙirarin cewa ƙasar Hausa ta fuskanci mulkin mallaka har guda biyu, waɗanda su ka taka rawa wajen mayar da ita koma-baya da dakushe cigaban ta.
Farfesa Abdalla ya kalli jihadin Fulani da Shehu Usman Ɗanfodiyo ya yi a matsayin mulkin mallaka na farko a ƙasar Hausa. A cewar sa, mulkin mallakan Turawan Birtaniya ya biyo bayan na Fulani ne.
Farfesa Abdalla ya ce shi asalin Bafulatani ne gaba da baya, amma Fulani da su ke yawo a jeji ba tare da sanin yadda tsarin gandu ya ke ba su su ka taimaka wajen taɓarɓara harkar gandu.
Wannan iƙirari nasa ya tada hazo, musamman yadda ya ke ganin kamata ya yi mai gabatar da takardar ya kalli wannan ɓangare a matsayin musabbabin tushen matsalar ƙasa da tsarin gandu a ƙasar.
Sai dai Farfesa Yusuf M. Adamu ya ƙalubalanci wannan iƙirari tare da cewa Fulani sun yi juyin-juya-hali ne, amma ba mulkin mallaka ba.
Haƙiƙa wannan batu ne da zai ɗauki hankali sosai, musamman duba ga halin da ake cikin na rashin tsaro tare da zargin Fulani ke kan gaba wajen tayar da ƙayar baya a ɓangaren satar mutane da garkuwa da su tare da haddasa rigima a tsakanin makiyaya da manoma a ƙasar nan.
Ban sani ba ko wannan hali da ake ciki ne na rashin tsaro ya sanya mutane su ka fara buɗe shafin wannan babi da aka jima ba a son a yi magana a kai.
Kamar wata shida baya a wata majalisar mu, mun tattauna da abokai inda wani yayan mu, Idris Bashir, ya yi fashin baƙi a kan wannan batu da Farfesa Abdalla ya buɗo a yanzu. A cewar sa, Fulani sun yi abin da ya kira ‘ta more’ a kan Hausawa tare da ƙoƙarin ruguza tarihin su.
Ya ce sarakunan da aka hamɓarar an same su ne a cikin Musulunci, wanda akwai sarkin da aka ci da yaƙi a ranar Sallah a yayin da ya fita filin Idi.
Ko yaya abin ya ke, wannan mahawara za ta iya zama nau’in tarihi wanda amfanin ta zai taimaka wajen haska wa al’umma yadda gobe za ta kasance.
An ƙalubalanci Farfesa Tanko cewa masana na ta kawo tarihin abin da mulkin mallaka ya haifar a ƙasashen Afrika, ba tare da damuwa da kawo yadda za a fita daga dabaibayin da su ka ɗora wa nahiyar ba.
Farfesa Tanko ya bada amsa da cewa masana na kawo tarihi ne a matsayin su na masu bincike don hakan ya zamo mabuɗi da za a yi amfani da shi a wajen buɗe hanyoyin da za a magance ƙalubale da ake fuskanta.
A nan, ina ganin ya kamata mu yi duba da idon basira a kan wannan batu na mulkin mallaka. Idan Fulani sun yi mulkin mallaka a ƙasar Hausa, sannan Turawan mulkin mallaka sun zo sun ɗora, to me hakan ya haifar a rayuwar mu?
A yanzu a halin da mu ke ciki, Fulani na kan gaba wajen tayar da ƙayar baya a wasu yankunan ƙasar. Da yawan waɗanda ake kamawa da laifin garkuwa ko satar mutanne da satar shanu Fulani ne. Kuma idan an kama su za ka ji sunan Musulunci a tare da su, amma a zahiri ko kaɗan babu siffofin Musulunci, babu sallah babu salati.
Maganar da ake ciki a yanzu a wasu sassan Nijeriya irin su Sakkwato da Zamfara, ‘yan ta’adda irin su Bello Turji ke da iko a wasu dazuzzuka. Kai, har wasu kasuwanni da ƙauyuka da tituna duk su na ƙarƙashin ikon su a fakaice, domin su na yin abin da suke so ne. Wannan kamar gwamnati ce a cikin gwamnati. Abin takaici ne a ce har mutanen wasu ƙauyukan kan tashi wakilai zuwa ga Turji domin samun maslaha.

Lokacin ina hidimar ƙasa a Jihar Kwara, na kan bi ta Minna a Jihar Neja, sannan in shiga Bidda. Daga nan sai in hau babur da zai kai ni bakin ruwa da zan haura zuwa Patigi. Mu kan yi tafiyar fiye da awa ɗaya cikin daji kafin mu isa bakin kwata (bakin ruwa).
Kwanakin baya na ke magana da abokin aiki da ya ke ɗan asalin Bidda. Bayan jin yadda na ke shiga Patigi a shekarun baya, ya koka min yadda abubuwa su ka ɓaci. “Ai Fulani sun lalata mana ƙasa, yanzu ba wanda ya ke yarda ya shiga dajin nan, domin sai a sace shi,” a cewar sa.
Wannan ita ce maganar zahiri da mu ke ciki, wanda dole mu gaya wa kan mu gaskiya tare da tunanin yadda za a magance wannan matsala.
An ce waiwaye adon tafiya. Ko shakka babu, Turawan mulkin mallaka sun bautar da iyaye da kakannin mu tare da tatsar arziƙin su. Sannan ko Fulani sun yi mulkin mallaka ko ba su yi ba, ya kamata mu kalli wannan maudu’i da idon basira.
Babban abin buƙata shi ne yadda za mu daina surutu, mu fahimci musabbabin matsalar mu tare da aiwatar da abin da mu ka fahimci shi ne mafita.
* Zaharaddeen marubuci ne kuma tsohon shugaban Ƙungiyar Marubuta Ta Nijeriya (ANA), reshen Jihar Kano. I-mel: zikallah@gmail.com
Ai nona dai ina shakka akan abin da Fulani suka yi lokacin kafa daulolin su, ana do a ce min a k ai zamanin da Fulani suka fi Hausawa ilimi da shiriya na Addini? To me ya faru bayan jihadin? Ya akayi wanda har ya kai yayi jihadi/ko Tajdidi aka wayi gari babu alama ko tasirin addinin tare da shi?
Sannan ma dai kuskure ne kiran abin da Jihadi… Don kamar yadda yake rubuce an kai hari Zaria ranar Juma’a, ne kuma Ranar Sallar Lauya ce, kenan ana yaki a watan harami ne? Kuma Jihadi a garin Musulmi? An ce sun isa garin Sarki yana Masallacin Juma’a.
Akwai dai bukatar bincike, duk da su din din yi kokarin shafe tarihin Hausawa ta hanyar boye rubuce rubuce dana Malaman Hausawa kafin Jihadin.