A ZAMANIN sa, Sarkin Kano murabus, Sir Muhammadu Sanusi, ya taɓa hana karuwai su wala a ƙasar sa, musamman ma a Kano, birni mafi girma a arewacin Nijeriya. Ya ce kowace mace ta je ta yi aure. Sir Sanusi babban malami ne.
Sai ‘yan doka na hukumar En’e su ka shiga kamen karuwai, ana yi masu tara. Su kuma su ka dinga gudu ko ɓoyewa ko fakewa da wasu sana’o’in, kamar tuwo-tuwo da saida shinkafa. Wasu, maneman su su ka riƙa ba su mafaka a ɓoye.
Ana kiran wannan al’amarin da “korar karuwai a Kano”.
Saboda yadda karuwai ke gudu su na ɓuya, sun ƙi barin garin ko sana’ar, sai Alhaji Mamman Shata ya yi waƙar nan ta “Na Ga Jahilci Wurin Karuwai” inda ya ke cewa ana korar mutum kamar kare shi ko ya liƙe kamar angulai.
To, sai Malam Ibrahim Ɗanmani Caji Bauchi, wanda ya na daga cikin manyan mawaƙan ƙasar Hausa, ya yi wa Shata martani da waƙar nan mai amshin “Haka Ne Malam Na Maude” inda ya ce shi bai ga laifin karuwai ba, a’a laifin masu neman su ya kamata a gani. Akwai inda ya ce:
“Yau mutum da abin sayarwa,
Ya kasa bai san wani mai saye ba,
Gobe ya kasa ya kwashe,
Bai san wani mai saye ba,
Jibi ya kasa ya kwashe,
Bai san wani mai saye ba,
Gata ya kasa ya kwashe,
Ya kwan bai sam saye ba,
Labudda barin garin ya ka yi!”
Manufar sa ita ce duk abin mutum zai sayar, ciki har da abin da karuwai ke sayarwa, idan babu mai saye to tilas ya sake wuri ko kuma ya bar sana’ar kwata-kwata.
A waƙar, ya ambaci Shata ɓaro-ɓaro, ya nuna cewa ɗora laifin karuwanci da Shata ya yi kan matan ba daidai ba ne; laifin mazan ne.
A zamanin, ba mawaƙin da ka iya ƙalubalantar Shata, don haka sai aka ga lallai Malam Ɗanmani ya yi bajinta. Kuma ba wannan ba ne karo na farko da Shata da Ɗanmani su ka gwabza. A shekarar farko ta mulkin Sir Sanusi ma sun kara a wani babban bikin aure na ‘ya’yan sarki su 12, taron da ake kira da Bikin ‘Yan Sarki. A bikin, Shata ya yi wa manyan makaɗa zarra, ciki har da Ɗanmani Caji, Ibrahim Daɓalo, Hamza Caji, Inu Caji, da sauran su. Daga bikin ne ma yawanci su ka fara sanin Shata a Kano.
Kowane mawaƙi so ya ke ya ga wallen Shata tun daga lokacin, amma ana shakkar taɓo shi, sai ka ce wani dodo!
Sai ga dama ta samu, Ɗanmani ya taɓo shi.
Shi kuma Shata, sai ya ga kamar an takale shi ne. Sai su ka shiga zaman doya da manja shi da Caji.
Ana wannan zaman sai aka haɗu a bikin auren fari na Alh. Babangida, ɗan wani babban attajiri a Jos mai suna Alh. Sa’adu (aminin Alh. Ibrahim Nashe ne, mahaifin yallaɓai Injiniya Abdullahi Ibrahim Nashe).
A labarin da marigayi Alhaji Ya’u Wazirin Shata ya ba ni, ya ce a wurin bikin auren, manyan makaɗa sun hallara, ciki har da Shata da Ɗanmani Caji. To sai ‘yan birni su ka ce su na so a yau dai a raba gardamar nan ta Shata da Ɗanmani kan wa ke da laifin karuwanci tsakanin matan bariki da mazan da ke neman su. Aka ce Shata ya rera waƙar nan tasa ta “Na Ga Jahilci Wurin Karuwai”, sannan Ɗanmani zai zo ya yi tasa ta martani. Sai Shata ya ce a’a, sai dai Ɗanmani ya fara, Allah basshi shi sai ya zo da tasa. Tilas aka yarda da hakan. Ba a san dabarar Shata ba!
Ɗanmani ya zo tsakar fage ya rera waƙar sa. Aka yi tafi aka yi masa liƙi, ya ja baya.
Da Shata ya shigo fage, duk an buɗe haƙora a ji waƙar nan da ya yi. Shi kuwa gogan naka da ya kalli ‘yan amshi da makaɗan sa, sai ya ba su sabon amshi, ya ce, “Don Sallah Da Salatil Fatih Don Allah Mata Ku Yi Aure”.
Sai wuri ya kaure da sowa da ife-ife da tafi.
Shata ya shiga waƙa fa, ya na cewa, “Tun daga Lawwali har ga Risala, Haƙ Ƙur’ani babban kundi, Ina ayar da ta kankare aure?”
A waƙar, ya nuna cewa auren dole na jawo shiga karuwanci ga ‘ya’ya mata.
Saboda zaƙin muryar Shata da fiƙirar sa da salon wasan sa (wato ‘showmanship’), nan take ya ci gari. ‘Yan birni su ka ce lallai hujjojin Shata sun fi na Ɗanmani ƙarfi. Haka kuma su ka ce, “Kai Malam Ɗanmani daga yau ka bar takalar Shata!”
Da aka watse daga wannan biki sai magana ta dinga yaɗuwa cewa Shata ya doke Ɗanmani a waƙa a Jos. Hakan bai yi wa Ɗanmani da yaran sa daɗi ba; su ka dinga jin haushi.
Bayan wani lokaci, Shata ya je Kaduna, Ɗanmani ma ya je. Sai yaran su su ka yi arba da juna a wani gidan mata mallakar Hajiya Hauwa Maikoko da ke Titin Ɓachama a Tudun Wada (gidan na nan kusa da maƙarbartar Chanchangi, dama da hanya in ka kalli gabas). A nan, sai yaran Ɗanmani su ka shiga takalar na Shata, wato su Lalo (wanda daga baya ya zama mawaƙi mai cin gashin kan sa, har na sha ganin shi ya na wasa a ƙauyen mu). Abin kamar za a dambace, amma aka raba su. An ce da Ɗanmani ya ga abin da ke faruwa, ya goyi bayan yaran sa.
Da labari ya kai kunnen Shata, sai bai ji daɗi ba.
Mafari kenan Shata ya yi wa Ɗanmani Caji zambo a dai wannan waƙa ta “Don Sallah Da Salatil Fatih…” A ta farkon, babu zambo, amma sai ya dinga maimaita ta a wurare daban-daban, ya na ragargazar Ɗanmani. A wata, ya na kiran sa da “kaɗon Bauchi”, wanda ƙabilanci ne da Fulani kan yi wa Hausawa. Sannan ya kira shi da “dugunzuma”, kuma ya ce, “Sai a littafin Malam Ɗanmani, ya ja baƙi ya kai wata aya, Sai na ji ya ce ‘Kak kui aure!'” duk da yake a zahiri Ɗanmani bai ce hakan ba, tsiya ce kawai ta zambo don a muzanta mutum.
A waƙar, Shata ya taɓo tarihin dalilin waƙar, ya ce:
“Mun saɓani a Jas,
Mun daidaita rannan a bukin Babangida,
Sai a Kaduna ta koma ɗanya,
Ya zagi su Lalo gidan Maikoko.”
Shi ko Malam Ɗanmani, bai riƙa maimaita waƙar sa ba tun daga lokacin da ya yi ta aka ɗauka a faifai.
A wata hira da Yusufu Ladan ya yi da Shata a Rediyon Nijeriya na Kaduna a cikin 1970, Shata ya bayyana cewa waƙar Malam Ɗanmani ita ce zambo na farko da ya yi inda ya ambaci sunan mutum muraran. Kuma ina jin a yawancin waƙoƙin zambo da ya yi daga bisani ba ya ambatar sunan mutum, sai dai ya yi kwatance ta yadda za a gane wanda ya ke yi wa zambon.
Allah ya jiƙan su baki ɗaya, amin.