• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Tsaron Arewa: Mamallaka gidajen rediyo da talbijin sun ƙaddamar da yekuwar yaƙi da rashin tsaro

by DAGA WAKILIN MU
February 4, 2022
in Nijeriya
0
Alhaji Abdullahi Yelwa ya na jawabi a taron

Alhaji Abdullahi Yelwa ya na jawabi a taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Mamallaka gidajen rediyo da talbijin da ke arewacin Nijeriya sun bayyana matuƙar damuwa dangane da ayyukan ‘yan ta’adda da mahara da sauran abubuwan assha da ke addabar yankin.

Don haka a ƙarƙashin Ƙungiyar Mamallaka Gidajen Rediyo da Talbijin ta Arewa (Northern Broadcast Media Owners Association, NBMOA) sun bayyana cewa za su fara wani aikin faɗakarwa ta hanyar kafafen su a kan wasu daga cikin munanan ayyukan da ke fuskantar Arewa da ma ƙasar baki ɗaya.

Ita dai NBMOA, ƙungiya ce ta mamallaka gidajen rediyo da talbijin da sauran masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai a Arewa wadda aka kafa domin samun cigaban yankin da ƙasa baki ɗaya tare da tabbatar da ƙwarewa da bunƙasa a harkar aikin rediyo da talbijin a Nijeriya.

A lokacin da ya ke jawabi ga wani taron manema labarai da aka yi a Abuja a ranar Laraba, muƙaddashin shugaban ƙungiyar, Alhaji Abdullahi Yelwa, ya ce ma’aikatan yaɗa labarai sun samu kan su a cikin mawuyacin hali dangane da rashin tsaro a Arewa.

Ya nuna cewa an cusa ƙasar nan cikin yaƙi da bala’in ta’addanci, ‘yan bindiga, kidinafin, rashin zuwan yara makaranta da kuma shaye-shayen muggan ƙwayoyi. 

Ya ƙara da cewa wannan jerin ƙalubalen ya samu ne sakamakon fatara da kuma rashin cigaban al’umma.

A cewar Alhaji Abdullahi Yelwa, gwamnati a dukkan matakai ta na yin iyakar ƙoƙarin ta domin ta daƙile waɗannan matsalolin saboda ta daidaita komai.

Ya ce an ɗauki matakai iri-iri, sannan an sawo sababbin kayan yaƙi na zamani waɗanda aka sanya cikin yaƙin.

Ya ce: “A kullum mu na fuskantar muggan abubuwan da waɗannan illoli su ke haifarwa a kan mutanen mu. A kullum ‘yan rahoton mu su na aiko da labaran hare-haren da ake kai wa ƙauyuka ana fatattaka su, sannan ana kama mutane ana garkuwa da su. 

“A kullum mu na bada labaran yadda mahara ‘yan bindiga ke aika wasiƙu zuwa ga ƙauyuka da al’ummomi su na cewa a kai masu kuɗin fansa ko kuɗin neman izinin zuwa gonakin su. Mu kan ji yadda ake harbe mutanen da aka sace idan an kasa biyan kuɗin da za a ‘yanto su. Mu kan ji yadda gwamnoni su ke bayyana baƙin cikin su ko yadda yanzu wasu sassa na jihohin su ba su ƙarƙashin ikon su. Mu kan bada rahoto kan mutanen da a da su ke iya ciyar da kan su amma yanzu sun koma zaman dirshan a sansanin ‘yan gudun hijira.

“Kafafen yaɗa labarai na Arewa su na kan gaba wajen kawo rahotanni game da  waɗannan matsaloli. Hasali ma dai wasu daga cikin membobin ƙungiyar mu sun sha wuyar wannan hali da ake ciki na ta’addanci, a yayin da a kullum mu ke faɗakarwa kan a kyautata wa mayaƙan mu da kuma waɗanda rashin tsaron ya shafa. Za mu ci gaba da sauke nauyin mu na tabbatar da nuna wa gwamnati abin da ya dace ta yi, tare da bada dama ga duk wani mai son ya faɗi ra’ayin sa kan yadda za a samo mafita kan tabbatar da tsaro a Arewa da Nijeriya baki ɗaya.”

Daga nan shugaban ƙungiyar ya bada sanarwar cewa daga yanzu  sun ɗaura yaƙin faɗakar da jama’a  kan wasu daga cikin manyan matsalolin da ke addabar Arewa. 

Alhaji Abdullahi Yelwa ya ce, “A ci gaba da ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da rashin tsaro tare da bada gudunmawa ga nemo hanyoyin da za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali da arziƙi a yankin mu da ƙasar mu, ƙungiyar mu ta NMBOA ta na sanar da jama’a cewa ta fara yekuwa ta kafofin ta a kan wasu daga cikin manyan matsalolin da ke addabar al’ummar mu. 

“Tsarin da za mu bi shi ne za mu yi amfani da inda mu ke shiga da fita da kuma hanyoyi daban-daban da ke faɗin Arewa da ma wajen ta, mu yi magana da hukumomin gwamnati a dukkan matakai, tare da ƙungiyoyi masu zaman kan su, da sarakuna da shugabannin addini da muhimman masu ruwa da tsaki domin a samo ingantattun shawarwari na jama’a da yadda al’ummomi za su kasance su ne kan gaba wajen yaƙi da rashin tsaro.

“Ta hanyar tsara wasu shirye-shirye na musamman a tsanake, da tallace-tallace na musamman, da sauran su, za a ilmantar da masu saurare kan rawar da ya kamata su taka da kuma yadda abin da su ka yi ko su ka kasa yi ya ke taimakawa wajen samar da wani sakamako a wannan yaƙi kan rashin tsaro.

Hakan ya kasance cigaba ne da haƙƙin jama’a da ya rataya a wuyan mu a matsayin mu na huɗu a jerin masu faɗa a ji a cikin al’umma.”

Loading

Tags: Alhaji Abdullahi Yelwagidajen rediyo da talbijininsecurityNBMOAnorthNorthern Broadcast Media Owners Associationrashin tsaroterrorism
Previous Post

Laifi ne idan an sayar da gidan Shata?

Next Post

Zaɓen Abuja: INEC ta bada tabbacin gudanar da zaɓe mai nagarta

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Sabuwar rajistar zaɓe: An samu mutum miliyan 5.35

Zaɓen Abuja: INEC ta bada tabbacin gudanar da zaɓe mai nagarta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!